Home Labarai An ɗauke mutane da dama bayan da ƴan ta’adda su ka buɗewa matafiya wuta a titin Kaduna-Abuja

An ɗauke mutane da dama bayan da ƴan ta’adda su ka buɗewa matafiya wuta a titin Kaduna-Abuja

0
An ɗauke mutane da dama bayan da ƴan ta’adda su ka buɗewa matafiya wuta a titin Kaduna-Abuja

 

Waɗansu da a ke zargin ƴan ta’adda ne sun kwashe matafiya a kan titin Kaduna-Abuja a yau Lahadi.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa ƴan ta’addan sun buɗe wuta kan me-uwa-da-wabi a kan matafiya da misalin ƙarfe 4 na yamma, inda hakan ya sanya wasu su ka ɗimauce.

Majiyoyi sun baiyanawa jaridar cewa matafiyan da su ka yi yunƙurin guduwa sun sha harbi, inda waɗanda su ka tsaya kuma a ka kaɗa su daji.

Wani matafiyi da ya tsira da ga harin ya shaidawa ɗan rahoton mu cewa lamarin ya faru ne a yankin Rijana.

“Masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da lalacewar titi a daidai wajen, tunda duk motar da ta zo sai ta rage wuta sannan ta ƙetare a hankali” in ji shi.

Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Kaduna, Mohammed Jalige bai amsa kiran wayar da ɗan rahoto ya yi masa domin jin ƙarin bayani ba.