
Babbar Kotun Tarayyar Najeriya reshen Jihar Legas ta yanke wa wani ɗan ƙasar China hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu bisa samunsa da laifin wulaƙanta kuɗin Najeriya wato Naira.
BBC Hausa ta rawaito Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ce ta kai ƙararsa inda alƙali I. Nicholas Oweibo ne ya yanke hukuncin.
Bayanai sun ce jami’an hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ce ta kama shi a ranar 17 ga watan Mayun 2022 lokacin da yake kokarin hawa jirgi zuwa kasar Kenya.
Sun kama shi ne yayin da jami’an suke binciken miyagun ƙwayoyi a jakar matafiyin inda shi kuma ya fusata ya yaga wasu kuɗaɗen Najeriya, kimanin Naira dubu uku da dari biyu.