Home Labarai Ɗaya da ga cikin waɗanda su ka naɗa Sarkin Kano Ado Bayero, Sarkin Bai Adnan ya rasu

Ɗaya da ga cikin waɗanda su ka naɗa Sarkin Kano Ado Bayero, Sarkin Bai Adnan ya rasu

0
Ɗaya da ga cikin waɗanda su ka naɗa Sarkin Kano Ado Bayero, Sarkin Bai Adnan ya rasu

 

 

 

 

Sarkin Ban Kano, Tsohon Hakimin Ɗambatta, Dakta Mukhtar Adnan ya rasu.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa marigayi Adnan ya rasu ne a asibiti da asubar yau Juma’a a Kano.

Kafin rasuwarsa, marigayin shine Kwamishinan Ilimi na farko a tarihin Kano.

Dakta Adnan ya kasance ɗan majalisar Sarki tun a shekarar 1954.

Marigayin ya kuma kasance ɗaya da ga cikin masu naɗin Sarki, inda da shi a ka naɗa Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero a 1963.

Tun a 1953 marigayi Adnan ya zama Hakimin Ɗambatta har zuwa shekarar 2019, inda a ka cire daga hakimcin sakamakon sabuwar dokar masarauta da Gwamna Abdullahi Ganduje ya ƙirkiro.

Wannan jarida ta jiyo cewa da safen nan ne dai za a yi jana’izar Sarkin Bai kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.