Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, ya kawar da shakkun da ake yi akansa, cewar ko zai bi sahun takwaransa na jihar Kaduna malam nasiru el-Rufai wajen korar malaman makarantar da basu cancanta ba.

Tambuwal yace, zamu yi kokarin ganin mun inganta iliminsu ta hanyar turasu aro karatu, da samun horo da kwarewa wajen koyarwa. Babu wani Malami da zamu kora a Sakkwato, ko da kuwa mun samu Malaman da suka kasa yin kokari a horon da zamu tura su, zamu cigaba da rike su a matsayin ma’aikatan Gwamnati, amma zamu canza musu wajen aiki.

Wani bincike da kwamitin bibiyar harkar Ilimi a jihar Sakkwato ya gudanar, ya ce akwai sama da kashi 31 na malaman makaranta wanda basu cancanci aikin koyarwa ba a jihar ta Sakkwato. Sai dai tuni Gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti domin ya duba harkar ilimin da batun kwarewar Malaman makaranta a Sakkwaton.

Kwamitin ya bayar da shawarar daukar sabbin Malaman makaranta 548 a maimakon korar wadan da ba kwararru ba. Domin dacewa da tsarin nan na yara 40 ko wanne Malami 1. Wannan na daya daga cikin kudirin Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal na kawo gyara a harkar ilimi, a cewar shugaban kwamitin.

A yayin da yake gabatar da rahotonsa, a gidan gwamnatin Sakkwaton, Dr. Shadi Sabeh yace, kwamatin nasu ya ziyarci makarantu 360, yace akwai bukatar gaggawa ga Gwamnatin da ta yi hanzari waje samar da Malaman Makarantu cikin sauri a wasu makarantun jihar.

Haka kuma, Sabeh, yace akwai karancin kayayyakin sadarwa na harkar koyarwa a galibin makarantun Gwamnatin jihar, dan haka yace, akwai bukatar Gwamnatin ta samar da kayyakin zamani domin bukatar Malamai su samu sukunin koyarwa cikin kwanciyar hankali.

A lokacin da yake mayarda Jawabi, Gwamna Aminu Waziri tambuwal na jihar Sakkwaton, ya godewa kwamitin, sannan ya tabbatar da cewar gwamnati zata aiwatar da rahoton kwamitin ba tare da wani bata lokaci ba.

“Gwamnati zata samar da sabon tsarin da zai baiwa Malamai damar samun horo da kwarewa akan harkar koyarwa tare da samar da sabbin kwasa kwasai da zasu taimakawa malamai wajen samun kwarewa da gogewa.

“Bari na sake tabbatar muku da cewar,babu wani malami ko guda daya da zamu kora daga aikinsa, mun fada mun kara jaddawa, dan haka kowanne malami ya kwantar da hankalinsa, a sabida haka zamu tabbatar mun baiwa malamai damar samun horo nan ba da jimawa ba.”

“Ina kara amfani da wannan damar, wajen mika godiya ta musamman ga wannan kwamiti da kuma jinjinawa namijin kokarinsa, Gwamnati da al’ummar jihar Sakkwato zasu yi alfahari da wannan namijin kokari da kukayi”. A cewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.