
Babban layin wutar lantarki ta na ƙasa ya sake sauka, inji rahoton Daily Trust.
Babban layin wutar lantarkin ya sauka ne da misalin karfe 2:42 na safiyar yau Litinin, inda karfin wutar ya ragu zuwa megawatt 64.70 kacal.
Kamfanin samar da wutar lantarki guda daya ne kawai ke aiki kamar yadda bayanai daga cibiyar sarrafa aikin rarraba wutar lantarki (ISO), reshen kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa suka nuna.
Wannan shine karo na shida da babban layin ya sauka a 2024.
Daily Trust ta ruwaito cewa, da misalin karfe 8 na safiyar yau Litinin, sabbin bayanai da cibiyar ta ISO ta fitar sun nuna cewa a halin yanzu tashar tana samar da wutar lantarki mai karfin megawat 266.50 daga Okpai, Geregu da Ibom.
Da yake tabbatar da saukar layin a cikin wata sanarwa, kfanin rarraba wutar lantarki na Jos ya ce: “Katsewar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin jihohinmu ya samo asali ne daga saukar babban layin wutar lantarki na kasa. Hakan kuma ya afku ne da sanyin safiya da misalin karfe biyu na yau litinin, 15 ga watan Afrilu 2024, wanda hakan ya sa aka rasa wutar lantarki a kasar.”
Shugaban sashen hulda da jama’a na Kamfanin, Dakta Friday Adakole Elijah, ya bayyana fatan cewa za a shawo kan lamarin nan ba da dadewa ba.