Home Labarai Babban Sifeton Ƴansanda ya baiwa jami’an sa umarnin kare ƴan Nijeriya masu zanga-zanga

Babban Sifeton Ƴansanda ya baiwa jami’an sa umarnin kare ƴan Nijeriya masu zanga-zanga

0
Babban Sifeton Ƴansanda ya baiwa jami’an sa umarnin kare ƴan Nijeriya masu zanga-zanga

Babban sufeton Ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci manyan jami’an ƴan sanda da su kare waɗanda suka shirya zanga-zanga kan adawa da tsadar rayuwa daga ranar 1 ga watan Agusta.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasika da Sufeto Janar ɗin ya aika kan buƙatar wani lauyan kare hakƙin ɗan’adam Ebun-Olu Adegboruwa.

A ranar 26 ga Yulin 2024, Adegboruwa ya rubuta wa Sifeton ƴan sandan wasika domin ya buƙaci ƴan sanda su bayar da kariya ga masu zanga-zangar.

Babban lauyan ya dai rubuta wasiƙar ne a madadin ƙungiyar ‘Take It Back’, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar.

A cikin wasikar martani mai ɗauke da sa hannun CP Johnson Adenola, Egbetokun ya umurci manyan jami’an ƴansanda da su saurari buƙatun babban lauyan.

Ya kuma buƙaci gana wa da Adegboruwa a Abuja a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2024, domin a ci gaba da tattaunawa kan buƙatarsa.

BBC Hausa