Home Labarai Babbar Sallah: KAROTA za ta baza jami’anta 1500 a titunan Kano

Babbar Sallah: KAROTA za ta baza jami’anta 1500 a titunan Kano

0
Babbar Sallah: KAROTA za ta baza jami’anta 1500 a titunan Kano

 

 

 

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA Zata baza jami’anta 1500 sassa daban daban na jihar danufin gudanar da bukukuwan sallah babba ta bana.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar-Na’isa ya sanya wa hannu a biya Laraba, KAROTA ta ce Jami’an nata zasu taimaka wajen sauƙaƙa ayyukan sufuri yayin shagulgulan Sallar.

Sannan hukumar ta gargaɗi masu ababen hawa su kiyaye dokokin hanya tana mai cewa duk wanda ta kama da laifi to kuwa za’a hukuntashi.

KAROTA ta kuma bukaci iyaye su guji bada mota ga ‘ya’yansu da basu kai munzalin tuƙi ba, inda ta ce zata kama duk yaron da ta gani da abin hawa yana tuƙi.