Home Labarai Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — IGP

Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — IGP

0
Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — IGP

 

Sufeto-Janar na ƴan sanda, IGP, Usman Baba, ya tabbatar da cewa babu wata barazana ga gudanar da zaben 2023.

IGP ya bayar da wannan tabbaci ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

A cewar Baba, wannan tabbacin ya biyo bayan nazarin barazanar tsaro da ƴan sanda su ka yi, ta yin amfani da mafi kyawun tsari a duniya don tabbatar da yanayin da ake sa ran za a gudanar da zaɓen.

Baba ya yi magana ne a wata ganawa da Todd Robinson, mataimakin sakatare, ofishin kula da harkokin miyagun kwayoyi da tabbatar da doka da oda, ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

IGP din ya gana da jami’in me a yayin taron shugabannin ƴan sandan Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a Amurka.

Ya ce batutuwan da a ka tattaunawa a wurin taron sun ta’allaƙa ne kan inganta tallafin da ake baiwa shirin horas da ‘yan sandan Najeriya.

Baba ya ce an fi mayar da hankali ne musamman kan horar da rundunonin dabarun yaki da aka tura a yankin Arewa maso Gabas da sauran yankunan da ta’addanci yai ƙamari a ƙasar.