
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi 36 Naira Biliyan 570 inda ya ce babu gaskiya a bayanin.
A wata sanarwa da Gwamnan ya sanywa hannu kuma aka wallafa ta a shafin gwamnatin jihar a jiya Alhamis, Makinde ya ce kudin da aka bayar ba daga gwamnatin tarayya suke kai tsaye ba.
Gwamnan ya ce kudin da jihohi suka karba, kudin COVID-19 ne daga bankin duniya, inda gwamnatin tarayya ta zama a tsakiya kawai.
Sannan ya ce kudin, an bada su ne domin mayarwa jihohi abinda suka kashe kan cutar COVID-19.
Nairametric