Home Labarai Babu ranar dena karɓar tsoffin kuɗi a Nijeriya — CBN

Babu ranar dena karɓar tsoffin kuɗi a Nijeriya — CBN

0
Babu ranar dena karɓar tsoffin kuɗi a Nijeriya — CBN

Babban Bankin Ƙasa, CBN, ya ce daga yanzu za a ci gaba da karɓar tsofaffin takardun Naira har abadan abada.

Daraktan Sashen Sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Abuja.

A cewar Abdulmumin, CBN, ba tare da wani haufi ba, na sanar da jama’a bukatar ta na tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira na N200, N500 da N1,000 har abada.

“Wannan ya yi daidai da yadda tsarin ya ke a fadin duniya da kuma hana maimaita wahalar da aka sha a baya.

A tuna cewa CBN ya kirkiri shirin sake fasalin takardun N200, N500 da N1,000 a watan Oktoban 2022.

Babban bankin ya kuma kayyade wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin.

Sai dai a watan Maris, Kotun Koli ta kara wa’adin ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200, N500, da N1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Shugaban kasa, Bola Tinubu, a yayin bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, ya yi alkawarin sake duba shirin sake fasalin Naira.