
Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta ce babu wani jami’in ta da ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje, bayan harin ta’addancin da aka kai a cibiyar tsare masu laifin.
Jami’in hulda da jama’a na SSS, Dakta Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa: “An jawo hankalin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan rahoton jaridar Vanguard ta yanar gizo na ranar 6 ga Yuli, 2022 mai taken: Harin gidan yari na Kuje: An kama mutum ɗaya bayan jajirtattun jami’an tsaro sun ƙure masa gudu.
“Rahoton ya yi zargin cewa ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere, wanda ya yi ikirarin cewa shi ma’aikacin DSS ne, ya shiga hannun jami’an NCS bayan sun cafke shi a kusa da Kwali.
“Rahoton ya kuma bayyana cewa wanda jami’in da a ke cewa DSS ne ɗin ya kuma yi iƙirarin cewa yana gudanar da wani aiki ne na musamman a dajin.
“Hukumar tana son bayyana cewa babu wani ma’aikacinta da ya tsere yayin da a ke guje-gujen.
“Hakika, a lokacin da aka kai hari gidan yarin, babu wani jami’in DSS da ya kasance a cikin fursunonin domin ya aiwatar da wani aiki na musamman.
“Rahoton Vanguard ba gaskiya bane don haka yaudara ce. Mu na shawartar jama’a da su yi watsi da shi.”