Home Labarai Badaƙalar kwangilar magani: Hukumar yaƙi da cin-hanci ta kama ɗan’uwan Kwankwaso da kuma wasu

Badaƙalar kwangilar magani: Hukumar yaƙi da cin-hanci ta kama ɗan’uwan Kwankwaso da kuma wasu

0
Badaƙalar kwangilar magani: Hukumar yaƙi da cin-hanci ta kama ɗan’uwan Kwankwaso da kuma wasu

Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da suka hada da Mohammed Kabawa, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, bisa zargin badakala a kwangilar kawo magunguna na biliyoyin naira.

Haka kuma hukumar ta kama shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta ƙasa, ALGON, reshen jihar, Abdullahi Bashir, wanda kuma shine shugaban karamar hukumar Tarauni.

Hakazalika, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta damke Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed, Musa Kwankwaso, wanda ɗan yayan shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso ne, duk dai akan zargin badakalar da aka yi.

Ana zargin su ne da hada baki wajen ba kamfanin Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomin jihar 38, inda aka aikata abinda ya saba wa dokokin sayan kayayyakin gwamnati.

Binciken farko ya nuna cewa kowacce daga cikin kananan hukumomin 38 ta biya Novomed Naira miliyan 9.150 domin siyan magunguna amma har yanzu ba a kawo musu magungunan ba.

“Muna da kananan hukumomi 44 a jihar kuma sun yi nasarar karbar Naira 9.150 daga kananan hukumomi 38 don samar da magungunan da ba a samar da su ba.

“Binciken ya kuma nuna cewa dukkan wadanda ake zargin suna bayar da hadin kai ga tawagar binciken hukumar”, kamar yadda wata majiya da ke kusa da lamarin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Kabiru Kabiru ya tabbatar da kamen, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike