Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba lallai ne yaje jihar Kano yakin neman zabe ba, saboda abinda Gwamnan Kano Ganduje ya aikata na karbar cin hanci a wani faifan bidiyo na Gwamnan da Daily Nigerian ta Wallafa.

Shugaba Buhari yana magana ne jiya a fadar Gwamnati yayin da yake tattaunawa da manyan jami’an yakin neman zabensa.

Daya daga cikin ‘Yan kwamitin Sanata Bashir Garba Lado ne ya tambayi Shugaban kasa akan a jinkirta zuwa jihar Kano da Legas sabida yawansu.

Sai Shugaba Buhari ya bashi amsa da cewar “Jihar Kano da aka nuno Gwamna yana karbar cin hanci yana murna” a cewar Shugaba Buhari ba lallai ne yaje Kano yakin neman zabe ba sai in “ya zama dole “.