
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Asabar a Daura, mahaifarsa, ya bayyana cewar bai shigo siyasa ba domin ya tarawa kansa da iyalansa abin duniya ba, Shugaban ya bayyana hakan ne, a wajen zaben sabbin Shugabannin jam’iyyar APC a dukkan mazabu da ake gudanarwa yau a Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da Malam Garba Shehu kakakin fadarShugaban kasa ya sanar, inda yace Shugaba Buhari bai bayyana aniyarsa ta sake neman zabe ba domin kawai tamore ba, sai don ya bautawa ‘yan Najeriya.
Da yake jawabi a wajen zaben sabbin Shugabannin, Shugaba Buhari yayi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar ta APC da su kasance masu tsoron Allah da kiyaye dokoki da kuma mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
A nasa jawabin, Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana cewar gudanar da zaben yana tafiya daidai kamar yadda aka tsara ba tare da samun wasu matsaloli ba, saboda yadda aka yi shiri kuma aka tanadi komai domin gudanarda wannan zaben.