
Hukumar yi wa kasa hidima NYSC, ta ce wani dan bautar kasa mai suna Mamudo Obaje, mai lamba KT/23B/1153 da aka kai jihar Katsina, ya kuma mutu a ranar 4 ga watan Janairu, ba ‘yan bindiga ne suka kashe shi ba.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Abuja.
Ya na mai da martani ne kan rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun kashe Obaje a kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Katsina.
A cewar Megwa, Obaje wanda ke koyarwa a Kwalejin ƴan Mata ta Gwamnati da ke Katsina, yana kan hanyar Kaduna zuwa Katsina a wannan rana, ya mutu ne sakamakon hatsarin mota a garin Gayaza da ke Karamar Hukumar Kankia ta Jihar Katsina, tare da wasu fasinjoji.
“biyu daga cikin fasinjojin, ciki har da Obaje sun rasa rayukansu a haɗarin.
“Mu a NYSC na kasa baki daya muna cikin makoki daga wannan mummunan lamari. Hukumar ta kuma jajanta wa iyalan marigayin bisa rashin babban dan kishin kasa wanda ya rasu a lokacin da yake yi wa kasarsa hidima.
“ NYSC na jaddada kira ga masu wallafa labarai da su kasance masu gaskiya a cikin rahotoninsu domin kada su haifar da fargaba a cikin al’umma, saboda wallafe-wallafen karya na rashin ƙwarewa sun saɓa wa ka’idojin aikin jarida,” inji shi.