Home Labarai Bandits sun koma karɓar giya a matsayin harajin noma a Taraba

Bandits sun koma karɓar giya a matsayin harajin noma a Taraba

0
Bandits sun koma karɓar giya a matsayin harajin noma a Taraba

Yan fashin jeji, da aka fi sani da bandits, sun koma karbar barasa a matsayin haraji daga manoma kafin su ba su damar girbe amfanin gona a karamar hukumar Ardo-Kola da ke jihar Taraba.

Wani babban ma’aikacin gwamnati a Jalingo, wanda ya so a sakaya sunansa, ya shaida wa Daily Trust cewa, bandits din sun tilasta masa sayen giyar da kudinta ya haura Naira dubu 200,000 kafin a bar shi ya girbe amfanin gonarsa.

Ya ce harajin da ‘yan fashin jejin suka dora ya fara daga Naira dubu 20,000 zuwa Naira dubu 100,000 ya danganta da girman gonar.

“Na biya da giya ta kimanin N200,000 kafin in shiga gonata,” in ji shi.

Ƙauyukan da ‘yan fashin jejin suka dora wa harajin sun hada da Baka, Kasakuru, Majowere, Digun, Nyapori, Buzi, Dare, da Sakala.

Wani mazaunin karamar hukumar, Malam Dantala Bello ya shaida wa Daily Trust cewa manoma sun saba biyan harajin ga yan fashin jeji kafin girbi.

Wata majiya a yankin ta ce ƴan bindigar na aiki da masu basu bayanan sirri domin samun bayanai kan mutanen da ke zuwa girbin gonakinsu a yankin, inda ta kara da cewa ana ganin bandits din suna yawon su dare da rana dauke da makamai.