Na farko daga hagu, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo, sai Abba Kyari sai kuma ta farko daga dama Shugabar ma'aikatan Gwamnatin tarayya Winifred Ayo-Ita

Jaridar Punch ta ruwaito Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa Alhaji Abba Kyari yana cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya umarce shi da ya ware kudi har Naira biliyan 50 a wani asusu na musamman, a yayin da Manajan Daraktan Kamfanin mai na kasa NNPC, Maikati Baru ya tambayi bahasi game da kudin.

An bankado wannan kullaliya ne, bayan da Majalisar wakilai ta kasa ta nemi karrin bayani kan wadancan zunzurutun kudaden da ake ajiye da su a wani kebantaccen Asusun da ya saba da tsarin nan na Asusun bai daya da ake ajiye kudaden Gwamnatin tarayya wato TSA.

Majalisar ta nemi karin bayani ne kan yadda akai wadan can kudade basu shiga asusun bai daya ba, inda Kamfanin NNPC karkashin Maikanti Baru ya shaidawa majalisar umarnin da Abba Kyari yace Shugaban kasa ya bashi kan wadancan kudade.

Wani kwamitin majalisar wakilai ne karkashin dan majalisa Danburam Abubakar Nuhu (APC- Kano) ya gano wannan badakala, inda yace, kwamitinsu ya gano wadancan kudade makare a wani asusun da ba shi ake ya kamata a ajiye kudaden ba.

Haka kuma, Babban bankin kasa CBN ya tabbatarwa da kwamitin Danburan cewar yana sane da wadancan kudade, bankin yake sanar musu cewar, sun samu bayanai daga kamfanin mai na NNPC cewar da umarnin Shugaban kasa aka ajiye wadancan kudade a wani asusu na musamman.

Wancan umarni na ajiye wadancan kudade yana rubuce ne a wata wasika da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Abba Kyari ya aiko, yana bayar da umarni ga kamfanin mai na kasa NNPC da kada ya shigar da kudin Naira biliyan 50 zuwa asusun nan na bai daya wato TSA, dan haka ne aka ajiye kudin a wani asusu na musamman.

A lokacin da yake nuna matukar mamakinsa kan wannana batu, dan majalisa Abubakar Danburam Nuhu,  yace “Ashe daman bankuna suna cigaba da ajiye kudaden da suka kai biliyan 50 a wani asusu ba tsarin nan na bai daya ba wato TSA”.

“Shi kansa bankin da ke ajiye da wadannan makudan kudade, yace ya samu umarni ne daga fadar Shugaban kasa kan cewar, ya ajiye wadannan kudade a wani asusu na musamman”

“Wadannan kudaden fa a asusun NNPC muka gano su, dan haka dole ne su nuna bayanan da suke tabbatar da umarni ne daga Shugabankasa yace a ajiye a wani asusu na musamman a cewar Dan majalisa Abubakar Danburan Nuhu”.

Sai dai wani babban jami’ai a babban bankin kasa na CBN Dipo Fatokun, ya tabbatarwa da kwamitin Danburam cewar NNPC ta aikowa bankin kasa a rubuce cewar akwai umarni daga Shugaban kasa kan ajiye wadancan kudade a wani asusu na musamman.

Wani mamba a kwamaitin ya nuna rashin gamsuwarsa da wadannan bayanai da suka fito daga wajen Abba Kyari, domin yace takardar ta fara bayani ne da “An bani umarni”, domin bai yi bayanin waye ya bashi umarnin ba, a cewarsa, dole ne a gayyato Abba Kyari ya zo yayi bayanin wanda ya bashi wancan umarni.

“Dole ne Abba Kyari ya zo ya bayyana a gaabanmu ya nuna mana shaidun da suka tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ajiye wadancan makudan kudade a wani asusun musamman sabanin wanda ake aiki da shi”

Wani dan majalisar mai suna Simon Arabo, yace akwai abinda yake nuna cewar wadannan kudade an ajiye su ne bisa wani umarni daga sama, to amma waye ya bayar da umarnin, tilas sai an gudanar da bincike mai zaman kansa.

A dan haka, kwamitin ya aamince da cewar, nan da s’o’i 48 dole Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Maikanti Baru ya bayyana a gabansa yayi masa bayanin yadda aka yi ya samu wannan umarni, da kuma inda umarnin ya samo asali.

Sannan kuma, dole babban bankin kasa CBN yazo da wani cikakken rahoto da zai yi bayanin yadda aka yi wasu bankuna suke cigaba da ajiye kudaden Gwamnati sabanin asusun baidaya da aka san ana ajiye dukkan kudaden Gwamnati a cikinsa, kafin karshen watan nan.