
Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi watsi da zargin cewa za a mayar da jam’iyyar ta ƴan Arewa bayan da a ka kai muƙamin shugaban jam’iya da na kwamitin amintattu zuwa yankin.
DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar PDP, Iyorcha Ayu, ya fito ne daga jihar Benue, yayin da shugaban kungiyar BoT, Walid Jibril, ya fito daga jihar Nasarawa, dukkansu jihohin Arewa ne
Amma Atiku Abubakar, wanda ya yi magana da manema labarai a jiya Alhamis, yayin da ya dawo kasar don halartar babban taron jam’iyyar a Osun bayan ya sha dogon hutu, ya bayyana ikirarin a matsayin ba na gaskiya ba.
Ya ce: “Ba wani yunƙuri na maida PDP ta ƴan Arewa , ban yarda da hakan ba.”
Ɗan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya kuma ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ta adawa ba sabon abu ba ne a siyasance, inda ya ce a shirye yake ya gana da gwamna Nyesom Wike wanda ake rikicin da shi.