Home Labarai DG ga Ƴan bautar ƙasa: Kar ku shiga harkokin siyasar garuruwan da a ka tura ku

DG ga Ƴan bautar ƙasa: Kar ku shiga harkokin siyasar garuruwan da a ka tura ku

0
DG ga Ƴan bautar ƙasa: Kar ku shiga harkokin siyasar garuruwan da a ka tura ku

 

 

 

Darakta-Janar, DG, na Hukumar kula da Masu yi wa ƙasa Hidima ta ƙasa NYSC Brigediya Janar Muhammad Fadah ya hori matasa yan yiwa kasa hidima da su guji shiga harkokin Siyasa a wuraren da aka turasu domin yiwa kasa hidima.

Fadah ya bayyana hakan ne yayi taron yaye ƴan yiwa kasa hidima rukuni na 2, kashi na 2, wanda ya gudana a sansanin masu yiwa kasa hidima na din-din-din dake kusalla a karamar hukumar karaye, Kano.

DG ɗin, wanda babbar jami’ar NYSC a Kano, Hajiya Aisha Tata Muhammad ta wakilta, ya ce ya gargadi matasan da su guji shiga siyasa, inda yace maimakon hakan, su maida hankali wajen gudanar da aiyukan da suka shafi cigaban al’ummar da aka turasu cikin su.

” ku zama jakadun hukumar NYSC na gari, ku kiyaye mutuncin makarantun da kuka gama da kuma na iyayen ta hanyar yin abubuwan da suka dace da gujewa yin duk wani abun da ya sabawa doka”.

Fadah yace su iya bakin kokarisu su bada ta su gudanarwar su wajen gudanar da aiyukan cigaba, tare da kiyaye duk wasu dokoki da ka’idoji na al’ummar da aka turasu cikin su, ya kuma bukace su da su kiyaye al’adun a mutane da suke cikin su.

“Ina gargadin ku guji aikata da duk wasu abubuwan da basu dace ba, kamar Shan miyagun kwayoyi da yawon dare da tafiye-tafiyen dare da Kuma shiga motar wanda Basu Sani ba da zummar rage hanya da dai sauransu”. inji Fadah

Darakta Janar din ya kuma bukace Yan yiwa kasa hidimar da su Maida hankali wajen aiwatar da sana’o’in dogaro da kai da suka kowa yayin zamansu a sansanin, saboda su dogaro da kawunansu sannan kuma al’umma ma su amfani da abubuwan da suka koya.

Yace hukumar ta NYSC tana iya bakin kokarita wajen haɗa hannu da duk Masu ruwa da tsaki domin nemar musu rancan yadda zasu sami jari don fara sana’o’in da aka koya musu don su dogara da kawunansu ko da bayan sun kammala yiwa haka hidima.

Daga ƙarshe ya yaba wa gwamnatin tarayya saboda irin gudunmawar da take bayarwa wajen tabbatuwar aikin yiwa kasa hidimar da Kuma Samar da ababen more rayuwa a dukkanin sansanin Yan yiwa kasa hidima dake fadin kasar nan.