Wasu daga cikin mutanan da aka kashe a kauyen Bawan Daji, a karamar hukumar ANka a jihar Zamfara

Bawan Daji, wani kauye ne dake yankin karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara, garin ya kasance cikin firgici da tashin hankali sakamakon kashe akalla mutane 60 da wasu ‘yan ta’adda suka yi a wasu hare hare guda biyu da suka kai kauyen.

Maharan dai sun kai wannan harin ne, a sakamakon wata tattaunawa da mutanan garin suka yi kan yadda zasu yi maganin ‘yan ta’adda masu kai musu farmaki a farkon kakar bana.

Tuni dai maharan suka yiwa al’ummar kashedin cewar babu yin aikin gona a bana, a wannan yanki baki dayansa.

Liman Umar, daya ne daga cikin Shugabannin al’umma a yankin, kuma shi ne mataimakin babban limamin garin, ya shaidawa manema labarai cewar maharan, sun jima suna matsawa mutane a yankin, suna bayyana muggan makamai a tsakanin mutane ba tare da tsoro ko fargaba ba.

“Bayan da ‘yan sintiri na garin nan suka yi wani taro domin tattauna hanyoyin magance hare haren wadannan ‘yan ta’adda a ranar Talata, wadannan mahara suka kawo mana wani mummunan hari, sun kashe har da wasu wadan da suke kokarin guduwa domin tsira da ransu”

Yace an samu da yawan gawarwaki sun fara lalacewa a cikin daji, wasu gawarwakinma ba za’a iya dauko su daga cikin daji a yi musu sutura ba sabida yadda suka rube suka lalace, bugu da kari, mutane a firgice suke da shiga cikin daji domin gudun abinda zai je ya dawo, domin ana da yakinin wadannan ‘yan ta’adda suna nan zaune cikin dajin.

Yace daya daga cikin mutanan kauyen, Danlai Shabalai, an kashe shi a lokacin da jami’an tsaro suka jiyo shi yana magana da maharan ta wayar tarho.

Shugaban karamar hukumar Anka, Mustapha gado, ya tabbatar da cewar an yi jana’izar mutane 32 a cikinsu akwai yara da mata wadan da suka rasu a wani asibiti a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

Mustapha Gado yace har ya zuwa yanzu an cigaba da laluben gawarwakin wasu wadan da ba’a gansu ba, duk kuwa da cewar an baza jami’an tsaro a yankin da abin ya auku, amma kuma kusan dukkan mutanan kauyen sun gudu sun bar gidajensu, saoda suna zaton maharan zasu iya dawowa.

Mai martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad wanda shi ne Shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara, yace wadannan kashe kashe da ake yi a yankin suna cigaba da aukuwa ne sabida karancin jami’an tsaro dama gawazawarsu ta wani fanni.

NAN