Hassan Y. A. Malik
 

Wasu matasa biyu, Abubakar Bello da Sikiru Bello, sun gurfana a gaban kotun majistare da ke Igbosere ta jihar Legas, jiya Litinin, bisa zargin zare belit tare da zane jami’an ‘yan sanda biyu masu mukamin Sufuritenda da kuma Cif Sufuritenda.

Matasan biyu,masu shekaru 16 da 19 da haihuwa, wadanda yaya da kanine, sun gurfana ne tare da mutum na uku da ta taimaka musu wajen aikata laifin, wata mai suna Risikat Arowolo, mai shekaru 33 da haihuwa, bisa laifuka biyu da suka hada da: hadin gwiwa wajen aikata laifi da kuma cin zarafi.

Furosikyutan ‘yan sanda, Sajan Peace Chukwudi ta fadawa kotu cewa, wadanda ake zargi sun aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2018, a cikin barakin ‘yan sanda na Macarthy da ke Legas.

Ta ci gaba da cewa, matasan biyu, wadanda ‘ya’yan dan sanda ne, tare da taimakon Risikat sun hada kai wajen cin zarafin jami’an ‘yansanda biyu wadanda ke zaune a cikin barikin ‘yan sanda daya da wadanda ake zargi.

“Wadanda ake zargi sun hada kai wajen zane jami’an ‘yan sanda biyu (Cif Sufuritenda Onojaife Kent da Sufuritenda Nwaimo Christopher) da belit tare kuma da hankada su cikin kwata.

“Wannan laifi nasu ya ci karo da dokar laifuka sashe na 172 da na 411 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015,” inji Furosikyuta Peace Chukwudi.

Fassarar sashen doka ta 172 na nufin wadanda ake zargi za su shafe 3 a gidan kaso bisa laifin cin zarafin dan sanda, doka ta 411 kuma na nufin wadanda ake zargi in har an same su da laifi za su shafe shekaru 2 a gidan kaso bisa laifin hada baki wajen aikata laifi.

Wadanda ake zargi dai basu amsa laifinsu ba, inda hakan ya sanya Mai shari’a Patrick Adekomaiya ta bayar da belinsu akan N50,000 kowannensu tare kuma da kawo mutanen da za su tsaya musu wadanda kowannensu sai ya bayar da takardar jawabin asusunsa na banki da kuma shaidar biyan haraji na ga gwamnatin Legas.

An daga sauraren karar zuwa ranar 14 ga watan Maris.