
Wasu ƴan bindiga sun kashe dagatai 2 da wasu mutane 2 biyu a kauyen Kulias da ke yankin Butura, a Ƙaramar Hukumar Bokkos a Jihar Plateau.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai dagaci mai suna Mataru Mahwash, mai shekaru 67, Mallan Amalam, mai shekaru 50, wanda shima dagaci ne, sai Ishaya Fompun mai shekaru 50, da Daniel Ishaya mai shekaru 22.
Da yake ba da labarin faruwar lamarin, wani dan unguwar mai suna Josiah, wanda ya rasa babban yayansa, ya ce maharan sun zo ne da yawa, kuma al’ummar yankin sun shiga cikin firgici yayin da jama’a su ka tsere domin tsira da ransu.
“Mutane da dama dauke da makamai sun afkawa unguwarmu da misalin karfe 9:00 na daren jiya. Sakamakon haka, an kashe mutane hudu ciki har da yayana, Mataru Mahwash.
“Da jin karar harbe-harbe da maharan ke yi, kowa da kowa ciki har da ni mu ka yi ta kanmu cikin dazuzzukan da ke kusa da mu har sai da aka gama harbe-harben. Da dawowarmu, na tarar da yayana da wasu mutane uku a cikin jini. Mu na cikin tsananin bakin ciki da firgici. Ba mu da tabbas kan abin da zai same mu nan gaba,” inji shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce an aika runduna ta ƴan sanda zuwa garin.
Ya ce za su tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.