Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴan sanda 3 a caji-ofis a Kogi

Ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴan sanda 3 a caji-ofis a Kogi

0
Ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴan sanda 3 a caji-ofis a Kogi

 

Wasu ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴan sanda uku a yau Asabar da sassafe a Jihar Kogi yayin da su ka kai hari a caji-ofis ɗin ƴan sanda na Adavi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edward Egbuka, ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ovye-Aya ya fitar a Lokoja.

Ya bayyana harin a matsayin rashin tausayi kuma abin takaici.

Egbuka ya bayyana cewa an kashe jami’an uku ne a wani artabu da maharan da su ka yi sumame wa jami’an da ke aiki a sashin Adavi da mamaki.

“Da sanyin safiyar ranar Asabar, rundunar ‘yan sandan ta samu rahoton wani mummunan lamari da ya faru a ofishin ‘yan sanda na Adavi, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishin.

“Sun yi harbin kan-mai-uwa-da-wabi, amma jami’an mu da jami’an sashin gaggawa da ke gudanar da ayyuka na musamman a karamar hukumar Adavi suka maida martani.

“Sai dai kash, rundunar ta rasa jami’anta guda uku sakamakon harbin bindiga, yayin da ‘yan bindigar suka gudu da raunukan harbin bindiga saboda sun kasa shiga ofishin.

“Saboda haka, an tura wata tawaga ta jami’an tsaro, kuma cikin sauri ta dawo da zaman lafiya a yankin.

Ovye-Aya ya nakalto Egbuka yana cewa “tuni a ka tura jami’ai domin bin sahun barayin da nufin kama su da kuma gurfanar da su gaban kotu.”