
Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi da ke Jihar Nasarawa, Muhammad Shehu Baba tare da hadiminsa, Tanimu Mohammed, sun shaƙi iskar ƴanci daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya tabbatar da hakan ga NAN a yau Lahadi a garin Lafiya.
Wasu ƴan bindiga ne ɗauke da makamai su ka yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi ɗin da hadiminsa a hanyar Keffi zuwa Akwanga a ranar Juma’a, inda su ka kashe dogarinsa kuma jami’in ɗan sanda, Sajan Alhassan Habib.
Nansel ya ce ƴan bindigan sun sake shi da misalin karfe 9:00 na dare a jiya Asabar, inda tuni su ka dasu da iyalansu.
Kakakin ‘yan sandan, ya ce an kama wasu mutane uku a kusa da unguwar Gittata da ke karamar hukumar Keffi da su ke da alaƙa da aikata laifin.
“Wadanda ake zargin sun fito ne daga jihar Kaduna, an kama su ne a lokacin da suke tattaunawa kan neman kudin fansa,” inji shi.
Nansel, ya ce ‘yan sandan ba su da masaniyar wani kudin fansa da aka biya kafin a sake su.
Ya bayyana cewa waɗanda suka yi garkuwa da su ɗin sun sako su ne saboda ci gaba da matsin lamba daga jami’an tsaro.
A halin da ake ciki kuma, tuni aka yi jana’izar dan sandan da ya mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Keffi.