
Birtaniya ta yafewa Somalia bashin da take bin ta baki ɗaya ƙarƙashin shirin yafewa matalautan ƙasashe bashin da ake binsu.
Wannan mataki na nufin taimakawa Somalia ta samu damar shiga tsare-tsare da shirye-shiryen cibiyoyin kuɗi na duniya, don ta samu masu zuba jari da kuma habbakar tattalin arziki, tare gina tsaro mai ɗorewa a ƙasar.
Mataimakin jakadan Birtaniya Sam Thomas ne ya bayyana hakan bayan wata tattaunawa da suka yi a Mogadishu babban birnin ƙasar da ministan kuɗi na Somalia Dihi Iman Cige.
“A yau ina tabbatar wa da ministan kuɗi Bihiin cewa Burtaniya ta ta yafewa Somalia bashin da take binta da kashi 100,” kamar yadda ya sanar a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X daga ofishin jakadancin Burtaniya.
Ministan kuɗi na somaliya Bihii Iman Cige ya yi maraba da wannan mutuntawa.
BBC Hausa