Harabar Masallacin 'yan Shuwa kenan, bayan kai mummunan harin kunar bakin wake

Akalla mutum 22 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani harin kunar bakin wake da aka kai cikin wani Masallaci da ake kira Masallacin ‘yan Shuwa dake yankin karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa.

A ‘yan kwanakin nan, ana ta samun hare haren ta’addanci a garuruwan Madagali, Maiha, Michika, Mubi ta Atrea da kuma Mubi ta kudu, wadannan garuruwan duk suna da iyaka da dajin Sambisa.

Shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa, Musa Bello ya tabbatar da cewar, jami’an asibitin yankin karamar hukumar, sun tabbatar da rasuwar mutum 22 a yayin da suke wannan Masallaci da Asubahi.

Ya kara da cewar, mutum 40 yanzu haka suna samun kulawar gaggawa a babban asibitin karamar hukumar Mubi ta Arewa.

Wani ganau ba jiyau ba, ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar, Maharin ya bi sahun Masallata ne da asubahin talatar nan, ya jira aka fara Sallah tare da shi, kafin ya tayar da Bom din da ya layyace jikinsa da shi.

Tare da shi aka ce, ALLAHU AKBAR a cikin Masallacin domin fara yin Sallar, a masallacin ‘yan Shuwa da ke yankin unguwar Madina, sannan daga bisani muka ji wata mummunar karar fashewa” A cewar wani ganau a wajen mai suna Musa Bukhari.

Mutane kadan ne suka bar asibitin da aka kai wadan da suka jikkata ba tare da sun samu wasu munanan raunuka ba.