‘Yan sintiri a Maiduguri sun ce, a ranar Juma’a wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne dauke da makamai akan babura sun bude wuta akan wasu mutane da suka yi kungiya domin zuwa saran itace a kauyen Kaje dake kusa da birnin Maiduguri.

“Tabbas ‘yan Boko Haram ne kuma sun kashe mutum 20”

Mutane 15 kuma sun dimauce yayin da aka neme su aka rasa a cikin daji.

Shuaibu Sidi, wani mazaunin garin na Kaje ya tabbar da abinda ya faru na kisan mutanen da Boko Haram suka yi.

Liman yace, mun samu yakinin cewar Boko Haram ne suka kai wannan harin, haka kuma, su wadannan masu dauke da makamai sune dai suka kashe wasu mutum 25 da kauyen Maiwa dake da nisan mil biyu daga kauyen na Kaje a ranar 30 ga watan Disambar da ya gabata.

Haka kuma, akwai yuwuwar wadannan ‘yan ta’adda sun fito ne daga dajin Sambisa suka kai wannan harin.

Ana yawan samun kai hare hare kan masu shiga daji saran itace daga ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sabida suna zarginsu da kaiwa soja bayanansu, hakan kuma na taimakawa wajen samun nasara kan ‘yan ta’addar.

A kalla masu saran itace 31 ne aka neme su ko sama ko kasa aka rasa tun daga 2 ga watan Janairu, wanda ake kyautata zaton an yi garkuwa da su a Gamboru iyakar Najeriya da Kamaru.