
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta yi nisa wajen magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar rage adadinsu a jihar daga sama da miliyan biyu zuwa dubu 800.
Gwamna Babagana Zulum ne ya bayyana haka a yau Talata a Maiduguri a wajen bikin kaddamar da sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 27 da raba motocin aiki na makarantu 57.
“Tun lokacin da na hau mulki a 2019, ilimi shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai.
“Da farko kokarinmu ya karkata ne wajen sake gina makarantunmu da suka lalace domin samar wa yara sama da miliyan biyu da ba sa zuwa makaranta a Borno damar samun ilimi.
“Ina godiya da cewa, cikin ikon Allah, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a yanzu ya ragu zuwa kasa da 800,000,” in ji Zulum.
Gwamnan ya ce an ƙaddamar da motocin ga Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomin domin inganta zirga-zirga da kuma sa ido sosai, ya kara da cewa dole ne a yi amfani da motocin sosai a hukumance ta hanyar baiwa kwararrun direbobi.
Ya umurci kwamishinan ilimi da ya rika bayar da rahoto akai-akai kan ayyukan kowace sakatariyar ilimi, inda ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi kasa da yadda ake tsammani za a maye gurbinsa.