Home Labarai Buhari ya ƙaddamar da aikin kwalbati a Jama’are

Buhari ya ƙaddamar da aikin kwalbati a Jama’are

0
Buhari ya ƙaddamar da aikin kwalbati a Jama’are

 

A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin kwata da kwalbati mai tsawon kilomita 7.6 a Ƙaramar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi.

Da ya ke samun wakilcin Ƙaramar Ministar Harkokin Masana’antu, Cinikaiya da Hannun-jari, Maryam Yalwaji-Katagum, Buhari ya ce an ƙaddamar da aikin ne domin magance zaizayar ƙasa a ƙaramar hukumar.

Ya ƙara da cewa an tsara aikin ne ta yadda zai magance wahalar da al’ummar yankin ke sha.

Aikin ya haɗa da gina kwatoci, kwalbati, gyaran hanyoyi da sauransu.

Buhari ya ƙara da cewa aikin zai magance matsalar muhalli a yankin.