Farfesa Wole Soyinka

Hassan Y. A. Malik

Fitaccen marubucin nan na Nijeriya, Farfesa Wole Soyinka, a jiya Talata ya kwatanta Shugaba Muhammadu Buhari da mutumin da ke cikin magagi mai karfi da ya sanya ba ya iya fahimtar halin da kasar ke ciki.

Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai game da hare-haren da fulani makiyaya ke kaiwa akan al’ummamomin manoma a fadin kasar da ke nema ya haddasa yaki a kasar nan.

Soyinka ya ci gaba da bayyana takaicinsa kan abubuwan da ya kira manyan kurakuran gwamnatin Buhari.

Da aka tambaye shi, kan me zai ce da Shugaba Buhari in ka hadu da shi? Sai Soyinka ya kada baki ya ce: “Zan ce masa, mai girma shugaba kasa, bana jin kana cikin hayyacinka. Kuma bukatar ka farka cikin gaggauwa don maganci matsalolin kasar nan, domin kurakurai suna ta faruwa a gwamnatinka babu ji babu gani”

Soyinka ya bayyana dawo da shugaban hukumar inshorar lafiya, NHIS, Farfesa Usman Yusuf a matsayinsa bayan ministansa ya dakatar da shi, a matsayin daya daga cikin manyan kurakuran da gwamnatin Buhari ta tafka a baya-bayan nan.