27.7 C
Abuja
Friday, September 30, 2022

Buhari ya gana da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka sako

Must read

 

 

Buhari ya gana da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka sako
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.

Shugaban kasar ya gana da mutanen ne a yau Alhamis a fadar Aso Villa da ke Abuja kwana daya bayan sako karin mutum biyar da aka sace a jirgin kasan.

Ko da yake kawo yanzu ba a bayyana batun da suka tattauna ba, amma hakan na faruwa ne makonni kadan bayan ‘yan bindigar sun sha alwashin sace shi kansa shugaban kasar da kuma gwamnan Jihar Kaduna Nasir Elrufai.

Sun yi barazanar sace shugaban kasar ne a wani bidiyo da suka fitar wanda ya nuna su suna lakada wa fasinjojin duka.

Har yanzu dai akwai sauran fasinjojin da ke hannun ‘yan bindigar, wadanda suka yi barazanar kashe su idan gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba.

Shugaba Buhari ya sha kakkausar suka daga wurin ‘yan kasar bisa abin da suka kira rashin kubutar da fasonjojin duk kuwa da umarnin da ya bai wa jami’an tsaro na yin hakan.

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article