Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya kaddamar da Ikeja Bus Terminal,katafariyar tashar mota ta zamani, a cigaba da ziyarar da yake yi ta kwana biyu a jihar Legas.

Wannan katafiriyar tashar mota ta zamani irinta ta farko a Najeriya da aka kaddamar a Legas na daya daga cikin manyan ayyukan da Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya gabatar.

Gwamna Ambode, ya taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kaddamar da wannan tashar da aka gina a tsakaiyar birnin jihar Legas dake Ikeja.

Sabuwar  tashar zata kasance babbar santa ta harkokin sufuri a yankin Ikeja dake jihar Legas wanda akalla mutane 50,000 zasu dinga safara akullum. Inda daga nan mutane zasu tashi zuwa ko ina a fadin jihar Legas musamman gurare da suka kunshi Oshodi da Ojota da Iyana-Ipaha da Maryland da Agege da Ogba da CMS da Obalende da sauransu.