Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara hubbaren shugaban kasar Turkiyya na farko wato Mustafa Kemal Ataturk.

Bayan ya ziyarci kabarin Marigayi Shugaba Ataturk kuma ya ajiye damin fulawa don nuna jimami da ladabi, sai kuma ya zarce fadar Shugaba Recep Tayyif Erdogan.

A jawabin da Garba Shehu kakakin shugaban ya bayar, Buhari ya girke damin fulawa mai launin tutar kasar Turkiyya na ja da fari.

Shugaban ya samu rakiyar Jakadan Najeriya a kasar Turkiyya Ambasada Iliyasu Paragalda da wasu manyan jami’an gwamnati.