A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Gini Bissau Jose Mario Vaz yau a fadar Gwamnati dake Aso Rock Villa.

Shugaba Buhari tare da dafawar karamar ministar harkokin wajen Najeriya Khadija Bukar Abba tare da kai taimakawa Shugaban kasa ta musamman akan ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje Abike Debiri ne suka karbi bakuncin Shugaban na Gini Bissau.