A lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari yake rattaba hannu akan dokar rage adadin shekarun tsayawa zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya sanya hannu kan daftarin dokar da ta baiwa batasa damar tsayawa zabe.

Dokar dai ta tanadi rage adadin shekarun da dan takara ya kamata ya kai kafin ya tsaya zabubbuka a Najeriya.

Ko a lokacin da ya yi jawabin ranar Demokaradiyya ta Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya alkawarta sanya hannu a dokar nan ba da jimawa, alkawarin da ya cika shi yau Alhamis.

Dokar dai ta tanadi cewar an sauya shekarun tsayawa Shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayin da aka rage shekarun tsayawa takarar majalisar dattawa daga 35 zuwa 30.

Haka kuma, an rage shekarun tsayawa takarar Gwamna daga shekaru 35 zuwa 30, yayin da aka rage shekarun tsayawa takarar majalisun dokoki na jihohi da na tarayya daga shekaru 30 zuwa 25.