Home Lafiya Buni ya amince da maida asibitocin sha-ka-tafi 7 zuwa manyan asibitoci a Yobe

Buni ya amince da maida asibitocin sha-ka-tafi 7 zuwa manyan asibitoci a Yobe

0
Buni ya amince da maida asibitocin sha-ka-tafi 7 zuwa manyan asibitoci a Yobe

 

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, PHC, wanda a ka fi sani da sha-ka-tafi guda bakwai zuwa manyan asibitoci a jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG, Baba Wali ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu a yau Alhamis.

Ya ce asibitocin da za a daga likkafar su sun haɗa da Machina, Nguru, Jajimaji Yusufari, Babangida, Bara da Buni Gari.

Wali ya ƙara da cewa, wannan daga likkafar ya kasance cika alkawarin da Buni ya yi na samar da babban asibiti guda ɗaya a kowace Ƙaramar Hukuma 17 da ke jihar.

Sakataren ya ce za a damar da asibitocin ne ƙarƙashin kulawar Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa jihar za ta ci gaba da ɓullo da manufofi da tsare-tsare da za su inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.