Ahmed Musa, dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles

Daga Abba ibrahim wada Gwale

Dan wasan gaba na tawagar super eagles ta najeriya dan kungiyar kwallon kafa ta Leceister city, Ahmad Musa ya bayyana cewa burinsa shine yasake samun damar zura kwallaye a ragar tawagar Argentina idan yasamu dama a wasan da za’a buga a nan gaba.

Tawagar yan wasan najeriya dai zata kece raini da yan wasan kasar Argentina ne a ranar 14 ga wannan watan a wani wasan sada zumunta da kasashen biyu zasu fafata a kasar Russia.

Ahmad musa dai ya zura kwallaye biyu a ragar kasar Argentina a shekaru uku da suka gabata a wasan cin kofin duniya wanda akayi a qasar Brazil a shekara ta 2014 sai dai wasan Argentina ce tasamu nasara daci 3-2 duk da kwallaye biyun da Ahmad din yazura.

Yace yanason yasake samun damar zura kwallaye a raga Argentina domin yanason yaga yana buga wasa tare da Messi a fili da wasu yan wasan kasar ta Argentina.

Yaci gaba da cewa kasar Argentina tanada manyan yan wasa wadanda suke buga manyan kungiyoyi a duniya kuma sunada tarihin cin kofin duniya saboda haka zaiji dadi idan yasake zura kwallo a ragar su.

Sannan yace idan najeriya tasamu nasara akan kasar ta Argentina zai sake bawa yan wasan kasar da magoya baya kwarin guiwar cewa zasu iya buga abin azo agani a kasar rasha.

Sai dai yace dole sai sun samu kwarin guiwa sannan sun dage idan suna bugawa da manyan kasashe sannan kuma samun nasara a wasan zai kara sawa martabar najeriya ta karu a idon duniya a fagen kwallon kafa.

Sannan yace yana godewa mai koyar da yan wasan kasar da shugabannin hukumar kwallon kafar kasar bisa wannan wasa da aka hada domin wasa ne mai muhimmanci.

Kasar Argentina dai taje wasan karshe a gasar cin kofin duniya wanda tasha kashi a hannun Germany daci 1-0 a gasar da akayi a kasar Brazil.