Aliyu Mohammed Tukur Gantsa, Jagoran kungiyar Siyasa Akida ta Najeriya

Shugaban kungiyar nan mai fafutikar dawo da siyasar Akida a zukatan matasan Najeriya, Aliyu Mohammed Tukur ya tattauna da DAILY NIGERIAN kan batun siyasar Akida da ta yi karancia zukatan matasan Najeriya. Aliyu Mohammed Tukur, shi ne shugaban kungiyar Advocacy Network Nigeria, wato Kungiyar Siyasa Akida ta Najeriya kenan da Hausa. Ya tattauna da DNH kamar haka:

DNH:Barkanmu dai Alhaji Aliyu Tukur,muna fatan zaka bamu tarihinka a takaice?

Aliyu Tukur: Ni sunana Aliyu Mohammed Tukur, kuma an haifeni a garin Gantsa dake ƙaramar hukumar Buji a jihar Jigawa. Kuma nayi makaranta har zuwa matakin jami’ah, nayi aikin koyarwa a jami’a a kasar Ethiopia, sannan na zagaya kasashen duniya daban daban, tundaga kasashen Turai da yankin gabas ta tsakiya da yankin gabas me nisa na Asia.

Idan kuma muka dawo bangaren siyasa inda nan nafi kwarewa, na faro siyasa tun daga matakin farko, abinda ake cewar ‘grass root’ a turance, kuma na faro ta ne tun kafin zamanin PRP da kuma bayan lokacin, har zuwa yanzu.

Na rike mukamin sakataren jam’iyyar PDP na jihar Jigawa, sannan na rike mukamin mai baiwa Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido shawara, nayi takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji.

Ina daya daga cikin memba a kwamitin da Jam’iyyar PDP ta kasa ta kafa domin sake dawo da martabar PDP, wanda Shugaban jam’iyya Sanata Ahmad Mohammed Makarfi ya ƙaddamar da mu a Shehu Musa YarAdua centre dake Abuja. Na shiga kwamitoci daban daban a Jigawa da ma najeriya baki daya.

Yanzu haka nine, “National Coordinator” na kungiyarmu mai suna Advocacy Network Nigeria ANN ko kuma Siyasa Akida, wadda muka dauki gabarar yada Siyasa cikin mutunci da girmamawa da kuma nuna martabar na gaba, da yin biyayya ga manya da kokarin jajircewa da sauransu.

DNH: Zamu so ka bayyana mana dalilan kafa wannan ƙungiya ta Siyasa Aƙida?

Aliyu Tukur: Mun kafa ANN ko kuma Siyasa Akida ne domin dawo da martabar siyasa irin ta da, irin wadda su Marigayi Malam Aminu Kano suka ginamu akai. Siyasar Akida ba komai bane, face jajircewa, da sanya kishin kasa da kuma al’umma a gaba, da fifita bukatun jama’a sama da bukatun kashin kai. Wannan shi ne abinda muka sanya a gaba, kuma muke kokarin ganin mun shiga lungu da sako na kasar nan wajen yin kira ga ‘yan uwanmu matasa wajen ganin sun jajirce wajen yin siyasar ra’ayi da akida.

DNH: Me ya saka ka kuduri wannan aniya ta dawo da siyasar Akida, ganin cewar yanzu da yawan mutane suna bin wanda zai basu kudi ne kawai?

Aliyu Tukur: To, irin wannan siyasar da ka fada ita muke son mu kawar mu kawo tsarkakkiyar siyasa ta kishin kasa. Domin a duk lokacin da mutane suka zama cima zaune, kawai su burinsu waye zai basu kudi su bishi,daga lokacin da muka yi haka, to mun gama yawo. Tilas mu yaki wannan tsari kuma mu jajirce akan wannana yaki da muke yi.

DNH: Kana ganin matasan yanzu zasu yadda da wannan tsari da kira da ka fito da shi na su kawar da batun kudi su yi siyasar Akida?

Aliyu Tukur: Alhamdulillah, kwalliya tana biyan kudin sabulu, domin duk jihohin da muke shiga da wannan batu muna samun goyon baya da cigaba sosai, domin jama’a da dama suna fahimtar abinda muke yi, kuma suna yabawa.

Akwai matasa masu mutunci da kullum suke fatan samun cigaba a wannan kasa, su kansu basa jin dadin yadda wasu ‘yan uwansu matasa suke syar da mutuncinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Kuma yanzu, misali ni da na shafe shekaru sama da 30 ina yin siyasa,sabida Allah sai mutum ya bani miliyan daya ko biyu ko uku na bishi dan ba ni da kishi, ashe duk shekarun da nayi ina gwagwarmayar siyasa farashinsu bai wuce miliyan daya ko biyu ba!

DNH: Ya zuwa yanzu ina da ina kuka shigar da wannan kungiyar ta Siyasa Akida?

Aliyu Tukur: Yanzu haka maganar nan da nake da ku, ina yankin kudu maso kudancin Najeriya ne a jihar Osun, inda muka kaddamar da reshen wannan kungiya. Kuma a Arewa inda wannan kngiya nance cibiyarta, kusan kowacce jiha mun je mun kafata, kuma tana da wakilai. Hakan nan ma, mun shiga yankin inyamurai na kudu maso gasa da yankin kudu maso kudu duk mun isar da wannan kungiya.

DNH: Ko wannan kungiya taku tana da alaka da wata jam’iyya?

Aliyu Tukur: Eh, ba zan ce a’a ba, domin dai ni duk wanda ya sanni ya san cewar ni dan jam’iyyar PDP ne, ita nake yi kuma zan cigaba da yinta. Amma hakan baai hana mu janyo wasu wadan da ba ‘yan PDP ba a cikin tafiyar Siyasa Akida, domin mu burinmu a kowacce jam’iyya mutum yake  ya rungumi Akida, ba siyasar me zan samu ba.

DNH: Wanne irin kira zaka yi ga matasa, musamman a wannan lokaci da zabe yake kara kusantowa?

Aliyu Tukur: Kirana ga ‘yan uwana matasa, shi ne mu tsaya mu jajirce akan siyasar ra’ayi da Akida, kuma mu tabbatar bamu cefanar da ‘yancinmu da ra’ayinmu ba, mu kaucewa yin siyasar kudi da abin duniya. Mu tsaya kai da fata wajen ganin mun kawo canji mai ma’ana a kasarmu, da kuma al’ummarmu.

Mu yi fatan jawowa yankunanmu abubuwa na cigaba, ta hanyar zabar mutane masu mutunci da suka dace, ba bin inna rududu ba, muyi siasar cancanta, mu zabi mutumin da ya dace, ba wai kawai muna jiran masu mulki su kwaso kudi su bamu muna binsu sai yadda suka yi da mu ba.

Mu tsaya, mu jajirce wajen ganin mun samar da wani sauyi da zai taimake mu ya taimaki ‘ya ‘yanmu da zasu zo nan gaba. Wannan shi ne zai tarihi ba zai mance da irin gudunmawar da muka bayar ba, kuma za’a jima ana tunamu, sannan kuma Allah ya gani irin ayyukan da muka yi na samarwa al’ummarmu cigaba, domin wannan aikin da muke yi shima jihadi ne irin na siyasa.

DNH: Muna godiya gareka, da aka samu dama aka tattauna da mu.

Aliyu Tukur: Nima na gode, da damar da kuka bani a wannan jarida taku mai farin jini.