Home Labarai Bushasha Zainab Ado Bayero ta yi da tallafin da gwamnan Kano ya bata – Majiyoyi

Bushasha Zainab Ado Bayero ta yi da tallafin da gwamnan Kano ya bata – Majiyoyi

0
Bushasha Zainab Ado Bayero ta yi da tallafin da gwamnan Kano ya bata – Majiyoyi

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, Zainab Ado Bayero ba ta yi amfani da tallafin kudade ga Gwamnan Kano , Abba Kabir Yusuf ya bata ba ta hanyar da ya dace, a cewar wasu majiyoyi.

A watan Yuni, Gwamna Yusuf ya kai mata ɗauki bayan ta roki a agaza mata lokacin da ake kokarin tashin su daga gidan haya a jihar Legas da ita da dan’uwan ta da mahaifiyar ta.

A wata sanarwa, mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya labarta yadda ya ziyarci jihar Legas ya gana da ma mallakin gidan da Zainab Ado Bayero ta ke a watan Yuni, inda aka biya kudin hayar gidan, kuma aka bata wasu kudaden da za su rike gidan.

Sai gashi watanni biyu bayan hakan, Zainab ta kara fitowa ta nemi tallafin kudi inda ta ce kudin da Gwamnan ya basu sun yi kadan.

Acewar ta, ta samu labarin cewa Gwamnan na shirin sama musu gida a Kano, amma su sun fi son gidan Naira Miliyan 150 a Legas.

Sai dai kuma Daily Trust ta rawaito cewa wasu majiyoyi sun bayyana mata cewa, Gwamnan ya bata wadataccen kudi da zai isa ta kula da kanta da sauran ƴan uwanta amma ta barnatar da su.

Majiyar ta ce gwamnan ya bata wajen Naira miliyan 10 amma duk ta ki amfani da su yadda ya dace.

Sai dai kuma ta shaidawa Daily Trust cewa batun cewa ta barnatar da kuɗaɗen ba gaskiya bane.