
Cibiyar mai rajin tabbatar da gaskiya da rikon amana, CAJA, ta ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan matasa kan tuntubar ƴan siyasa da su rika cika alkawuran da suka dauka yayin yaƙin neman zabe.
Da ya ke magana wajen ƙaddamar da shirin, shugaban CAJA, Kabiru Dakata ya ce an kirkiro da shirin ne da nufin ƙarfafa dimokraɗiyya don ci gaban kasa baki ɗaya.
A cewar sa, ƴan Nijeriya, musamman matasa, sun zafi zaɓe kaɗai shi ne dimokraɗiyya, inda ya kara da cewa mulki da ake gudanarwa da kuma tuntubar masu mulki kan cika alkawuran da suka dauka, shine ginshikin ci gaban dimokraɗiyya.
Ya ce a bangaren shirin, an samar da wasu gungun matasa da aka yi wa laƙabi da Democracy Ambassadors Network, DAN, domin a basu horo na musamman su kuma su shiga lungu da sako su na wayar wa da matasa kaina kan dimokraɗiyya.
A nasa jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar Kano, Hamza Safiyanu Kachako, ya yabawa CAJA bisa wannan kokari na ci gaban dimokraɗiyya.
Ya ce gwamnatin su ta baiwa matasa muhimmanci inda ya ce ta kuma yi musu tanadi mai girma domin inganta rayuwar su a jihar Kano.
A nasa bangaren, kodinetan DAN, Aminu Mukhtar Isah, ya yi alkawarin gudanar da aikin da aka basu cikin kwarewa da jajircewa.
Ya luma ci alwashin jagorantar DAN su shiga lungu da sako don wayar da kan jama’a a game da dimokraɗiyya.