Mansur Ahmed

Ban sani ba ko malamin da ya koya min lissafi ne bai k’ware ba, jama’a ku taya ni nazari, Aminu Ibrahim Ringim ya samu kuri’a 450,000 a zab’en 2015 a matsayin yawan kuri’arsa ta takarar Gwamna, a shekarar 2016 a wani taro da Badaru ya karb’i su Bashir Adamu Jumbo ance mutane 360,000 sun fita daga jam’iyyar PDP sun koma APC, a farkon shekarar 2018 Danladi Sankara ya fita daga PDP yace ya tafi da mutane 70,000, a yau kuma Tijjani Ibrahim Kiyawa sun ce sun fita da mutane 151,000, idan ka had’a lissafin zai baka 581,000. A cikin 450,000 idan aka debe 581,000 nawa ne saura? Ina suka samo sauran mutanen suka k’ara akan yawan kuri’armu ta 2015?

Abinda ya kamata tunanin duk mai cikakken hankali ya bashi shine, ko dai wadda suke komawa APC basu da cikakken wayo da hankalin gane abinda suke fad’a suna magana ne kawai zuciyarsu da idonsu a rufe saboda za’a basu wani k’aramin kud’i su chanza jam’iyya ko kuma makusantan Badaru burinsu kullum duniya tana masa kallon mak’aryaci domin ana fad’ar abubuwan da babu tunani da cikakken nazari a cikinsu, ko kuma sun mayar da dukkan al’umma marasa tunani da zasu iya ganewa gaskiya har su auna abubuwan da ake fad’a musu.

Ina yiwa wadda suka shiga jam’iyyar APC a ranar yau jaje tare da taya su jimami da tak’aicin da suka jefa rayuwar siyasarsu a ciki, ba shakka duk mutumin da ya kalli alk’aluman siyasa a Jigawa yasan jam’iyyar PDP ake yi kuma zata lashe zab’en ta da iznin Allah, domin asalin mutane masu kad’a kuri’a suna tare da ita, masu saka babbar riga su nemi muk’ami wadda baza su iya rayuwa babu gwamnati ba sune suke ficewa domin neman na kayan miya, shi yasa kullum a Jigawa talakawa suke ta dawowa jam’iyyar PDP.

Idan kana so ka gane abinda nake fad’a ka juya ka kalli tsohon mataimakin gwamna Ahmed Mahmud Kulkuli, Ka kalli Ambasada Ahmed Malam Madori, Ka kalli Sanata Mustapha Makama Kiyawa, ka kalli Sanata Bello Maitama, ka kalli Sanata Ibrahim Mohd Kiri-kasamma, ka kalli Hon. Yusuf Shitu Galambi, ka kalli Hon. Lawan Danzomo zasu baka tabbacin Badaru ba zai baka muk’ami ko ya sama maka makoma ta siyasa ba domin dukkan wad’ancan sun bar PDP sun tafi wajen Badaru idan muk’ami ake samu a chan ko mutunci sune zasu zame maka hujja, idan koma baya da wulak’anci ake samu sune zasu zame maka madubi.

Ko da yake Hausawa sunce ” idan ka kasa kayanka a kasuwa aka yi ciniki aka baka kud’inka to kuma sai yadda wadda ya sayi kayan yayi da abinsa domin shine mallakinsa juma kud’insa ya biya.

MASU KWADAYI SUN TAFI GIDAN MAYE KWADAYI. ALLAH KA KIYASHE MU DA SHAHADAR BUNSURU.