Categories
Bayani

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 300 a shekarar 2017

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 299.5 a shekarar 2017 da ta gabata. Babban Kwamishinan sadarwa na hukumar Abdullahi Goje shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar talata a Legas.

Kwamishinan yace, alkalun sun zarta abinda aka samu a shekarar 2016 da kaso 84.65.

Mista Goje ya cigaba da cewar, wannan shi ne karon farko cikin shekaru biyar da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara wannan zunzurutun makudan kudade a shekarar 2017.

“A shekarar 2013, hukumar a tara Naira biliyan 154.50, daga nan aka samu karin naira biliyan 159.30 da kuma biliyan 180.50 a shekarar 2014 da kuma 2015”

NAN

Categories
Bayani Siyasa

Burinmu dawo da siyasar Aƙida a zukatan matasan Najeriya – Aliyu Tukur Gantsa

Shugaban kungiyar nan mai fafutikar dawo da siyasar Akida a zukatan matasan Najeriya, Aliyu Mohammed Tukur ya tattauna da DAILY NIGERIAN kan batun siyasar Akida da ta yi karancia zukatan matasan Najeriya. Aliyu Mohammed Tukur, shi ne shugaban kungiyar Advocacy Network Nigeria, wato Kungiyar Siyasa Akida ta Najeriya kenan da Hausa. Ya tattauna da DNH kamar haka:

DNH:Barkanmu dai Alhaji Aliyu Tukur,muna fatan zaka bamu tarihinka a takaice?

Aliyu Tukur: Ni sunana Aliyu Mohammed Tukur, kuma an haifeni a garin Gantsa dake ƙaramar hukumar Buji a jihar Jigawa. Kuma nayi makaranta har zuwa matakin jami’ah, nayi aikin koyarwa a jami’a a kasar Ethiopia, sannan na zagaya kasashen duniya daban daban, tundaga kasashen Turai da yankin gabas ta tsakiya da yankin gabas me nisa na Asia.

Idan kuma muka dawo bangaren siyasa inda nan nafi kwarewa, na faro siyasa tun daga matakin farko, abinda ake cewar ‘grass root’ a turance, kuma na faro ta ne tun kafin zamanin PRP da kuma bayan lokacin, har zuwa yanzu.

Na rike mukamin sakataren jam’iyyar PDP na jihar Jigawa, sannan na rike mukamin mai baiwa Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido shawara, nayi takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji.

Ina daya daga cikin memba a kwamitin da Jam’iyyar PDP ta kasa ta kafa domin sake dawo da martabar PDP, wanda Shugaban jam’iyya Sanata Ahmad Mohammed Makarfi ya ƙaddamar da mu a Shehu Musa YarAdua centre dake Abuja. Na shiga kwamitoci daban daban a Jigawa da ma najeriya baki daya.

Yanzu haka nine, “National Coordinator” na kungiyarmu mai suna Advocacy Network Nigeria ANN ko kuma Siyasa Akida, wadda muka dauki gabarar yada Siyasa cikin mutunci da girmamawa da kuma nuna martabar na gaba, da yin biyayya ga manya da kokarin jajircewa da sauransu.

DNH: Zamu so ka bayyana mana dalilan kafa wannan ƙungiya ta Siyasa Aƙida?

Aliyu Tukur: Mun kafa ANN ko kuma Siyasa Akida ne domin dawo da martabar siyasa irin ta da, irin wadda su Marigayi Malam Aminu Kano suka ginamu akai. Siyasar Akida ba komai bane, face jajircewa, da sanya kishin kasa da kuma al’umma a gaba, da fifita bukatun jama’a sama da bukatun kashin kai. Wannan shi ne abinda muka sanya a gaba, kuma muke kokarin ganin mun shiga lungu da sako na kasar nan wajen yin kira ga ‘yan uwanmu matasa wajen ganin sun jajirce wajen yin siyasar ra’ayi da akida.

DNH: Me ya saka ka kuduri wannan aniya ta dawo da siyasar Akida, ganin cewar yanzu da yawan mutane suna bin wanda zai basu kudi ne kawai?

Aliyu Tukur: To, irin wannan siyasar da ka fada ita muke son mu kawar mu kawo tsarkakkiyar siyasa ta kishin kasa. Domin a duk lokacin da mutane suka zama cima zaune, kawai su burinsu waye zai basu kudi su bishi,daga lokacin da muka yi haka, to mun gama yawo. Tilas mu yaki wannan tsari kuma mu jajirce akan wannana yaki da muke yi.

DNH: Kana ganin matasan yanzu zasu yadda da wannan tsari da kira da ka fito da shi na su kawar da batun kudi su yi siyasar Akida?

Aliyu Tukur: Alhamdulillah, kwalliya tana biyan kudin sabulu, domin duk jihohin da muke shiga da wannan batu muna samun goyon baya da cigaba sosai, domin jama’a da dama suna fahimtar abinda muke yi, kuma suna yabawa.

Akwai matasa masu mutunci da kullum suke fatan samun cigaba a wannan kasa, su kansu basa jin dadin yadda wasu ‘yan uwansu matasa suke syar da mutuncinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Kuma yanzu, misali ni da na shafe shekaru sama da 30 ina yin siyasa,sabida Allah sai mutum ya bani miliyan daya ko biyu ko uku na bishi dan ba ni da kishi, ashe duk shekarun da nayi ina gwagwarmayar siyasa farashinsu bai wuce miliyan daya ko biyu ba!

DNH: Ya zuwa yanzu ina da ina kuka shigar da wannan kungiyar ta Siyasa Akida?

Aliyu Tukur: Yanzu haka maganar nan da nake da ku, ina yankin kudu maso kudancin Najeriya ne a jihar Osun, inda muka kaddamar da reshen wannan kungiya. Kuma a Arewa inda wannan kngiya nance cibiyarta, kusan kowacce jiha mun je mun kafata, kuma tana da wakilai. Hakan nan ma, mun shiga yankin inyamurai na kudu maso gasa da yankin kudu maso kudu duk mun isar da wannan kungiya.

DNH: Ko wannan kungiya taku tana da alaka da wata jam’iyya?

Aliyu Tukur: Eh, ba zan ce a’a ba, domin dai ni duk wanda ya sanni ya san cewar ni dan jam’iyyar PDP ne, ita nake yi kuma zan cigaba da yinta. Amma hakan baai hana mu janyo wasu wadan da ba ‘yan PDP ba a cikin tafiyar Siyasa Akida, domin mu burinmu a kowacce jam’iyya mutum yake  ya rungumi Akida, ba siyasar me zan samu ba.

DNH: Wanne irin kira zaka yi ga matasa, musamman a wannan lokaci da zabe yake kara kusantowa?

Aliyu Tukur: Kirana ga ‘yan uwana matasa, shi ne mu tsaya mu jajirce akan siyasar ra’ayi da Akida, kuma mu tabbatar bamu cefanar da ‘yancinmu da ra’ayinmu ba, mu kaucewa yin siyasar kudi da abin duniya. Mu tsaya kai da fata wajen ganin mun kawo canji mai ma’ana a kasarmu, da kuma al’ummarmu.

Mu yi fatan jawowa yankunanmu abubuwa na cigaba, ta hanyar zabar mutane masu mutunci da suka dace, ba bin inna rududu ba, muyi siasar cancanta, mu zabi mutumin da ya dace, ba wai kawai muna jiran masu mulki su kwaso kudi su bamu muna binsu sai yadda suka yi da mu ba.

Mu tsaya, mu jajirce wajen ganin mun samar da wani sauyi da zai taimake mu ya taimaki ‘ya ‘yanmu da zasu zo nan gaba. Wannan shi ne zai tarihi ba zai mance da irin gudunmawar da muka bayar ba, kuma za’a jima ana tunamu, sannan kuma Allah ya gani irin ayyukan da muka yi na samarwa al’ummarmu cigaba, domin wannan aikin da muke yi shima jihadi ne irin na siyasa.

DNH: Muna godiya gareka, da aka samu dama aka tattauna da mu.

Aliyu Tukur: Nima na gode, da damar da kuka bani a wannan jarida taku mai farin jini.

Categories
Bayani

FADAKARWA: Zuciya na samun nutsuwa da tawakkali idan . . . Sheikh Aliyu Said Gamawa

Rayuwa na da ban tsoro… in kana cikin daula da natsuwa to ka bi a hankali kayi komi don neman yardar ALLAH, ka mutumta dama ka zauna lafiya da kowa.
Tabbas nishadi da yalwa duk suna iya canza maka a cikin wuni daya, abinda ka saba dashi zai iya sauyawa zuwa wanda baka taba tunani ba.​ ​wato daga Bakin ciki ka koma farin ciki, ko daga mai babu ka ko ma mawadaci. Haka nan daga mai mulki kana iya dawowa talaka…
Allah na jarabtar bawa ta ko wanne fanni, don haka a kullum karka ta6a dauka kai kadai ne a yayin da duniya taimaka kunci ko in tayi maka dadi.
​Jarabawa ce Allah ya dora maka wani abu da zai zama abin damuwa a gareka dan a ga karfin imaninka a gare Shi. Ka zama mai tawakkali da addu’a, zaka ga sakamakon alheri, amma in kaki natsuwa ka dogaro ga Allah to zaka rayu cikin nadama da masifar rashin godiya ga Allah
​Ba lallai bane ace komi ka nema a take zaka samu, ko abinda kake so ya faru a lokaci daya ba, saboda haka kar ka gaza, Ka rike addu’a da sadaka, ka kyautata imaninka, ka yawaita istigfari kuma ka mika lamurranka ga Allah.
Allah ya sa mu dace, Amin
Categories
Bayani

Dan Najeriya yaci nasara a musabakar karatun Qurani ta duniya da aka yi a Makkah

Ranar laraba ne aka kammala musabakar karatun Qurani mai girma ta duniya da aka yi a birnin Makkah mai tsarki. Inda mutane daban daban daga sassan kasashen duniya suka halarci gasar.

Faisal Muhammad Auwal daga jihar Zamfara shi ne ya wakilci Najeiya a gasar karatun Quranin a matakin izufi 60 da Tafseer. Faisal ya samu nasarar zamowa na biyu a matakin duniya baki daya.

Sannan kuma, shima wani dan Najeriya mai suna Albashir Goni Usman daga jihar Borno yaci nasarar zuwa mataki na biyu a izufi 60 babu Tafseer. Wadannan sune mutum biyu da suka wakilci Najeriya a wannan gasa da ake yi duk shekara a birnin Makkah.

Najeriya dai na samun halartar shiga wannan gasa da ake gudanarwa a duk shekara a birnin na Makkah mai tsarki. Tuni dai aka raba kyaututtuka ga wadan da suka yi nasara a wannan gasa, wanda babban limamin masallacin Ka’aba Sheikh Abdul-Rahman Sudais ya jagoranci rabawa.

Categories
Bayani

NAZARI: Rayuwar kare a karofi

Zaman kare a karofi

Daga Yasir Ramadan Gwale

Rashin tsari da bin ka’ida na daya daga cikin dumbin matsalolin da suka dame mu. Idan za’a yi bayani na gaskiya kan irin dumbin matsalolin da suke dabaibaye da wannan al’umma tamu ta Nigeria, bai wuce irin zaman rashin tsari da rashin son kowace irin ka’aida ba, a harkokin rayuwa na yau da kullum, a koda yaushe, da yawan mutane sun fi son gudanar da al’amuran rayuwarsu, cikin rashin bin tsari da kiyaye ka’ida. Ana rayuwa tamkar zaman kare a karofi.

Yana daga cikin ayyukan hukuma na wajibi, tilasta mutane bin ka’aida, da shiryawa mutane bin tsarin da ya dace da hankali da addini da kuma al’ada. Wannan shi ne ke bayuwa zuwa ga samarwa da al’umma tarbiyya. Domin ita tarbiyya, ana dora mutune akanta ne, domin saita musu rayuwa ta dace da yadda ya kamata a gudanar da ita, kuma ta dace da hankali da yanayin rayuwar mutane.

Wajibin hukuma ne ta sanyawa mutane bin tsari. Amma sau da yawa abinda yake faruwa shi ne akasi, mutane daman bisa dabi’arsu basa son bin tsari da ka’ida. Misali idan muka dauki harkar sufuri a Nigeria, abin yana bambanta tsakanin wani gari zuwa wani. Gwamnatoci har yanzu basu kai ga samar da tashoshin mota na zamani da suka dace da rayuwar karni na 21 ba, zaka yi mamaki idan ka zagaya jihohinmu kaga inda ake kira tashoshin mota saikayi mamaki, kayi zaton har yanzu muna rayuwa a karni na goma sha uku ne.

An bar mutane suna rayuuwa sasakai, ba tare da kiyaye ka’ida da doka ba. An samar da tashoshin mota ne domin amfanin jama’a na yau da kullum, amma hukumomi da ya kamata su maida hankali wajen ganin lallai masu motocin sufuri suna amfani da wadannan tashoshin mota ko dan ingantar samun kudin shigar kananan hukumomi da jihohi, amma abin ba haka yake ba. Ga tasha an samar, amma masu diban fasinja, basu cika son shiga tasha ba sai dole, haka suma, fasinjoji masu hawa mota basa son shiga tasha su hau mota. An bar mutane kara zube.

Maimakon hukumomi su tilastawa masu motocin sufuri amfani da tashoshin mota, da tilasta masu hawa mota zuwa tasha su hau mota, sai aka bar abin taci barkatai, kowa yana yin yadda yaga dama. Da yawan fasinjoji na yin korafin yadda da dama daga cikin masu motocin sufuri kan ci zarafinsu, ko kin mutuntasu a matsayinsu na abokan mu’amala. Mai mota ya zagi fasinja, akan abinda bai taka kara ya karya ba, ko kaga dan kankanin yaro sabo da shi kwandasta ne, ya samu babban mutum yana ruga masa ashariya, kuma ba abinda zai faru. Wanda wannan ba daidai bane.

Tilas ne sai an dawo da bin doka da kuma tsari da da’a a rayuwar yau da kullum ta jama’a. Gwamnatoci musamman na jihohi su samar da tashoshin mota na zamani da suka dace da rayuwar yau da kullum, domin ingantawa mutane sha’anin sufuri da sauransu. Sannan tilas gwamnatoci su tursasawa masu motocin sufuri na yau da kullum su dinga amfani da tashar mota domin dauka da sauke fasinja. Ba daidai bane abar mutane suna samarwa da kansu tashoshin mota na babbu gaira bare dalili. Mutane su tsaya inda suka ga dama su hau mota, sannan su sauka inda suka ga dama. Inda duk aka cigaba ba irin wannan tsarin ake bi ba. Dole ne ya zama akwai ka’aida, kuma an sanyawa mutane kiyaye wannan ka’idar wajen hawa ko sauka daga motocin haya.

Hakazalika, masu baburan nan mai kafa uku, da ake kira Adaidaita Sahu a kano, ko Keke nafef a Kaduna. Suma suna bukatar samar musu da tashoshi domin samar da tsari a harkar sufinsu, ba daidai bane suma ace an barsu suna abinda suka ga dama, babu wani tsari akansu, in ma kaga wani tsari a tare da su daga hukuma, to bai wuce na karbar haraji ba. Amma karewa mutane walwala ko mutunci sam babu wani abu mai kama da haka. Zaka sha mamaki, idan kaga yadda masu tuka irin wannan Babura ke yin tukin ganin dama akan tituna, su zagi wanda duk suka ga dama, ko wanda yayi musu kuskure, su yi tuki son ransu, ba tare da tunanin akwai wata doka da zata yi aiki akansu ba.

Idan mutum ya kasance mai zafin rai ne, to kusan kullum sai ya hadu da takaicin masu Adaidaita sahu. Domin galibinsu matasa ne, kuma sun koyi tuka babur dinne a titi, basu san, ka’idar amfani da hanya ba, basu san ka’idar yin kiliya ko shan kwana ba, suma kuma wasu masu motocin da yawa basu san wadancan ka’idojin ba, dan haka sai ake rayuwar kare a karofi. Babu wani wanda yake mutunta kowa, kowa na takama da hanya, ba tare da saurarawa dan uwansa ba, ko daga kafa, kowa bai isa ba. Wannan duk laifi ne da hukumomi suka dauki kaso mafi tsoka a cikinsa, domin su ne a hakku, na su samar da tsarin da zai dadadawa kowa, tsakanin mai babur da maimota da kuma masu hawa mota ko babur dama masu ababen hawa nasu.

Yana daga cikin abubuwa na sakacin hukumomi shi ne rashin samar da kyakkyawan tsarin amfani da hanyoyin ababen hawa. Ga hukumomin kula da hanyoyi da masu lura da masu ababen hawa, amma kadan ne ke aikinsu yadda ya dace. Domin hukumomin gwamnati sunfi maida hankali akan abinda ya shafi cin tara ko karbar haraji, a maimakon aikin kula da ingancin hanyoyi da kuma tabbatar da cewar mutane suna amfani da hanyoyi ba tare da sun cutar da wasu ba. Amma galibi akasi ne ke faruwa.

Mutane na yiwa kansu tsari ne yadda suka ga dama. Basa mutunta dokokin amfani da hanyoyi, su kuma hukumomin basa sanya mutane su fahimci abinda ke kansu na kiyaye doka da ka’ida ba. A dinga tare motoci babu gaira babu dalili akan hanya, a cutar da mutane masu amfani da hanyar, sannan a cutar da wanda aka tsare. Sau da dama, idan anga matsala ta auku, ya kamata a dubi me ya samar da ita, kuma tayaya ta auku, ayi kokarin magancewa daga tushe, amma sam ba’a lura da wannan sai dai kawai ayi batun cin mutum tara.

Zaka ga yadda dogarawan hanya kan tare motocin da suka yi lodi fiye da kima, ana cin tararsu. Da ya kamata ne, a duba musabbabin faruwar abin. Tayaya direba ya yi lodin day a wuce ka’ida kuma ya hau titi? Asali ina tashoshin mota, wanda hakkin su ne su tabbatar da cewar masu motoci basu dauki kaya fiye da kima ba a motocinsu. Wannan zai tabbatar maka irin masu wannan daukar kaya fiye da kima, basa yin amfani da tashoshin mota na hukuma, suna amfani ne da tashoshin da suka tsarawa kansu, su dauki kaya a inda suke so, su sauke kaya a inda suka ga dama. Maganin irin wannan matsalar yana da alaka da samar da tashoshin mota na zamani, wanda suka kunshi duk wasu injina da zasu auna adadin kayan da mutum yake dauke da su, da kuma adadin kayan da mota zata iya dauka.

Abin mamaki, kaga an laftawa karamar mota kaya fiye da kima, kuma ka samu mutane sun hau saman kayan ana zuba mugun gudu da su, a irin wannan ne, daga zarar hadarin mota ya auku sai kaji anyi hasarar rayuka masu yawa. Duk wannan yana faruwa ne sakamakon sakacin hukumomi. Asalima akwai motocin da aka yisu domin daukan kaya wato “Goods Only” ma’ana kaya kawai. To amma irin wannan motocin ne zaka ga an lafta musu kaya da ya shige kimar abinda zasu dauka, sannan kuma an dora mutane a saman kayan.

Akwai kuma, motocin da zaka ga, na sufuri ne, amma a haka zaka ga ana jibga musu kaya, sannan a zuba mutane. Ko kuma motar da aka yi a ka’ida zata dauki mutum hudu banda direba, amma sai a zuba mata mutum shida, kuma hukumomi suna kallo anki tsawatarwa ko daukar matakin da ya dace, ai ba daidai bane, abar masu mota na daukar fasinja yadda suka ga dama, su loda mutane kamar kayan wanki wani kan wani.

Haka nan suma masu tuka irin manyan motocin nan masu sufiri daga wani garin zuwa wani, suna daukar kaya fiye da kima, kuma a inda suka ga dama, wani zubin su kashe titi suna lodi ba tare da kiyaye hakkin mutane masu amfani da hanyar ba. Ko su kashe hanya sabida an batawa wani daga  cikinsu rai, ko anyi masa ba daidai ba. Lallai suma, ya kamata, hukumomi su kawo tsarin da ya dace akansu. A hana musu shigowa cikin gari a lokacin da mutane suke tsaka da hada-hadar yau da kullum, a sanya su su dinga daukar kayan da bai wuce kima ba.

Amma abin takaici, da tsakar rana, sai kaga mai babbar mota ya dauko siminti buhu dari shida ya biyo kan titin da ake hada-hada da tsakar rana, duk ya batawa mutane rai, kuma ana kallonsa sai dai wani zubin kaga ana binsu ana cin tarar da bata shiga aljihun gwamnati. Wadannan kadan ne daga cikin irin abubuwa na rashin tsari da rashin son bin ka’ida da mutane suke yi musamman ta fuskar sufuri da kuma ababen hawa. Muna fatan hukumomi zasu yi abinda ya dace a harkar sufuri a fadin jihohin kasar nan.

 

Categories
Bayani

BINCIKE: An bankado almundahana a sashen ilimi na kananan hukumin jihar Kano

Daga Yasir Ramadan Gwale

Hukumar karbar koke-koken danne hakki da yaki da almundahana da zambar kudade ta jihar Kano ta bankado wata almundahana da zambar kudade da ta shafi wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Kano tare da hadin bakin wasu daga cikin shugabannin makarantun primary dake jihar Kano.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka, a lokacin da yake karbar rahoton binciken daga daraktan hukumar da ya jagkranci wannan bincike SA Gusau. Magaji ya bayyana cewa, laifukan da suka bankado sun sabawa dokokin da suka kafa hukumar a shekarar 2008.

Muhuyi magaji ya kara da cewar, hukumarsa ta kwato sama da Naira Miliyan 21 daga hannun wadan da ake zargi da yin almundahanar. A cewarsa wasu daga cikin mutanan da ake zargi sun baiwa hukumar hadinkai wajen gudanar da binciken don gurfanar da wadan da ake zargi da laifukan zambar kudaden.

A wani bayani kuma, da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Maimuna Saidu Bello ta sanyawa hannu, ya bayyana cewar tun kusan a shekarar bara ne, hukumar ta kaddamar da gudanar da binciken akan irin bayanan sirrin da suke samu kan badakalar da ake tafkawa a sashen ilimi na kananan hukumomin jihar Kano. Ta kara da cewar, hukumar ta yi bincike akan mutane sama da 50 wadan da ake zargi suna da hannu dumu dumu cikin almundahanar.