Categories
Cinikayya

Amurka zata zuba jari na makudan kudade a Najeriya

Tawagar da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranta, itace ta bayyana haka bayan ta gana da ‘yan kasuwa da masana fasaha a Silicon Valley, dake jahar California.

Tawagar jami’an Najeriya karkashin jagorancin mataimakin shugaban Najeriya Farfessa Yemi Osinbanjo, ta kammala wata ziyarar kwadaitawa ‘yan kasuwar Amurka musamman masu masana’antun fasaha su tafi Najeriya su zuba jari.

Shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya Dr.Isa Ali Pantami, yace akwai kudi dala milyan dubu daya da Amurkan ta ware domin zuba jari ta fannin fasaha. Saboda haka ne suka kawo ziyara suka gana da ‘yan kasuwa da masu manyan kamfanonin fasaha, suka gwada musu fa’aidar zuba jarin a Najeriya fiyeda wasu wurare.

Dr. Pantami, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya cewa, akalla ‘yan kasuwa da masu kamfanonin fasaha da ba zasu kasa 30 bane suka halarci ganawar.

Pantami, yace, sunyi amfani da damar suka kuma ziyarci manya manyan kamfanonin fasaha kamar su Google, da takwarorinsa a fannin fasaha wadanda walau za su je Najeriya su zuba jari, ko kuma za su je kasar domin horasda matasa da akalla za su kai dubu ashirin.

VOAHAUSA.COM

Categories
Cinikayya

Yadda Kasuwar Bello ta bunkasa cikin kankanin lokaci – Bello Galadanci

DAILY NIGERIAN ta zanta da Shugaban kasuwar Bello, kasuwa irinta ta farko a shafukan yanar gizo da Hausa, wadda Bello Galadanchi PhD ya kirkira, inda kuma yake gudanar da hada hadar kasuwancin nasa duk a kafar sadarwa ta intanet.

Bello ya bayyana mana yadda suka samu tagomashi cikin kankanin lokaci a yanayin kasuwancin da suke yi a kasuwar Bello. Ya kuma bayyana mana yadda suka yi cinikin miliyoyin kudade a cikin kankanin lokaci:

“Kasuwar Bello ta fara hada-hadar sayar da kaya a tsarin kasuwanci gabannin watan azumi saboda neman albarkar wannan lokaci, da kuma fahimtar bukatar jama’a gabannin Sallah. To jama’a daga duka jihohin arewacin Najeriya masu yawa sun yi cinikin kaya ta shafukan Kasuwar Bello dake yanar gizo da WhatsApp, da Facebook da Instagram, da ma ta wayar tarho.”

“Tsarin Kasuwar shine saya wa jama’a irin kayan da suke so a China, a tura musu har jihohin su kyauta a farashi mai ban mamaki. Misali, jakar dubu biyar a Kasuwa ana samun ta a dubu biya a Kasuwar Bello, haka zalika rigunan yara na dubu biyar akan same su a dubu daya da dari biyar. Bello Galadanchi Ph.D wanda ya kirkiri kasuwar ya fahimci bukatun masu karamin karfi, shiyasa ya shirya tsare tsaren da zai samar da kayan Sallah ga masu bukatar sari akan farashi mai rahusar gaske, da har ta kai wasu kwastomominsa suna rera mishi wakoki saboda murna.”

“A cikin watanni da bude hada-hadar kasuwanci, Kasuwar Bello ta sayar da rigunan yara mata dubu huda da dari takwas da sittin da shida (4865) da takalman yara kafa dubu uku da dari takwas da ashirin da biyar (3825) da leggings dubu biyu da dari bakwai da saba’in da biyar (2775), da takalman mata dubu biyu da tamanin da shida (2086). Banda su akwai kaya masu yawa kamar jakunkunan mata da kayan wutar lantarki da kayan wasa da suma aka yi cinikinsu. A takaice Kasuwar tayi cinikin sama da Nera miliyan 30 a cikin watanni biyu.”

“Idan kayan suka isa Lagos daga China, agents din Kasuwar Mudassir Mande da Alhaji Arzeka zasu tarbe su sannan su tura su Kano wajen Super Agent Yaya Abubakar da Haruna Shu’aibu Danzomo da Muhammad Sulaiman Labbo. Daga nan za’a kaisu warehouse din Kasuwa a sharada inda za’a tantance su, sannan a ware su domin turawa agents din jihohi daban daban da kwastomomi a duk arewacin Najeriya.” A cewar Shugaban Kasuwar Bello, Mallam Bello Galadanchi PhD.

Categories
Cinikayya

Kasuwar Bello na kara bunkasa harkar cinikayya a intanet ga Hausawa

Kasuwar Bello ita ce kasuwar hada hadar kayayyaki irinta ta farko da aka yi domin Hausawa ko masu jin harshen Hausa. An kafa kasuwar Bello ne domin bunkasa harkar cinikayyar zamani a intanet ga Hausawa.

A halin yanzu a dalilin gabatowar bukukuwan Sallah kasuwar Bello na kara samun bunkasa sosai ta yadda mutane kan shiga shagunan cikin kasuwar dake kan intent su yi sayayya kuma a kawwoo musu abinda suka saya har gida.

Shugaban Kasuwa Bello Galadanchi, ya bayyana a shafin kungiyar na Facebook yadda mutane ke kara nuna gamsuwa da mu’amala da Kasuwar Bello.

Ita dai kasuwar Bello na baiwa ‘yan kasuwa damar tallata hajarsu a shagunan dake cikin kasuwar kyauta ba tare da sun biya ko sisi ba, haka nan kuma tuni ‘yan kasuwa da dama suka mallaki shaguna inda suke tallar hajarsu ga masu saye.

Yanzu haka kasuwar Bello ta cika da ‘yan kasuwa masu saye da sayarwa, inda jama’a da dama kan sayi musamman takaalma da riguna da kayan amfanin gidaje da sauran kayan kwalliya domin gwangwajewa a Sallar bana.

Bello Galadanchi ya bayyana cewar dukkan kayan da ake sayarwa a kasuwar Bello masu inganci ne da kuma rahusa sosai, bugu dakari akwai ragi mai yawa ga wanda zasu sayi kaya da yawa.

Ana iya shiga dandalin kasuwar Bello dake kan yanar gizo a www.kasuwarbello.com domin ganewa ido, ko kuma a duba su akan shafinsu na Facebook wanda za’a iya samu idan aka rubuta Kasuwar Bello a shafin facebook.

Categories
Cinikayya

Babban Bankin Najeriya yayi ruwan dalar Amurka a kasuwar musayen kudade

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana cewar ya antayo zunzurutun kudi kimanin dala miliyan 293 domin rabawa bankunan da suke hulda da ‘yan kasuwa.

Bankin ya bayyana cewar ya rabawa Bankunan dalar ne domin magance karancin dala da ‘yan kasuwar musayar kudade suke fuskanta a lokuta da dama.

Ya kara da cewar, ana bukatar dalar Amurka domin shigo da kayan ayyukan gona daga kasashen waje, da kuma kamfanonin zega zirgar jiragen sama dama kamfanonin mai duk suna da bukatar dalar Amurka mai yawa.

 

Categories
Cinikayya

Kamfanin Max Air zai fara zirga-zirga a cikin Najeriya da sabon jirgi 737

Kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Max Air, ya bayyana fara yin zirga zirgar cikin gida da sabon jirgi samfurin 737.

Kakakin kamfanin Ibrahim Dahiru ya bayyana cewar tuni suka karbi jirgi guda daya a cikin guda uku da suka sayo domin yin wannan zirga zirga a cikin gida.

Yace nan ba da jimawa ba ne kamfanin zai fara yin jigilar fasinja a jihohin Najeriya da sabbin jiragen da kamfanin ya samar.

 

Categories
Cinikayya

Gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi sun raba Tiriliyan 1.9 a wata uku

Kwamatin dake kula da rabon arzikin kasa tsakanin Gwamnatin tarayya da Gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi (FAAC) ya tabbatar da cewar a cikin wata ukun farko na wannan shekarar Gwamnatocin sun kasafta Naira Tiriliyan 1.9 a tsakaninsu.

Bayanai sun nuna cewar an samu karin kashi 37.3 akan abinda aka raba a baya cikin wata ukun karshe na shekarar 2017, inda Gwamnatocn suka raba Naira Tiriliyan 1.411.

A wannan karon Gwamnatin tarayya ta samu zunzurutun kudi Naira biliyan 812.8 yayin da jihohi 36 suka kasafta Naira biliyan 683.4, haka suma Gwamnatocin kananan hukumomi sun rabauta da samun Naira biliyan 393.3 domin kasaftawa tsakaninsu.

Ko meye ra’ayinku game da yadda ake rabon wadannan kudade tsakanin Gwamnatoci, shin kwalliya tana biyan kudin sabulu?

Categories
Cinikayya

Buhari ya kashe sama da Tiriliyan guda dan inganta rayuwar ‘yan Najeriya – Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta kashe sama da Naira Tiriliyan guda domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, inda yace Gwamnatin ta mayarda hankali sosai wajen ayyukan raya kasa da suka hada da gina hanyoyi da aikin layin dogo da kuma taimakawa rayuwar matasa, musamman ta bangaren aikin N-Power.

Mataimakin Shugaban kasar ya kara da cewar ya zuwa yanzu bliyoyon kudade aka kashe wajen ciyarda daliban Firamare abinci kyauta a makarantunsu, wanda Gwamnatin Buhari ce ta bullo da wannan shiri na ciyar da dalibai abinci kyauta.

Ko me zaku ce kan wannan batu?

Categories
Cinikayya Raayi

TATTAUNAWA: Yadda muka kafa kasuwar yanar gizo da babu irin ta – Bello Galadanchi

Jaridar Daily Naigerian Hausa ta yi wata tattaunawa ta musamman da hazikin matashi mai himma da kokarin bunkasa harkar kasuwanci da saye da sayarwa ta hanyar amfani da yanar gizo. Wannan matashi Bello Galadanchi, wanda yake zaune a kasar Chana ya kafa wannan kasuwa irin ta ta farko a yanar gizo musammana domin al’ummar Hausawa da kuma masu magana da harshen Hausa. Ga yadda tattaunawarsu da wakilin DNH da shi ta kaya:

DNH: Ko zaka yi mana bayanin wannan kasuwa a takaice?

Bello Galadanchi: To, Bismillahirrahmanir Rahim, Masha Allah, da farko mun yi nazari mungan cewar an dade ana cutar Mallam Bahaushe a wasu bangarori na tattalin arzikinsa da kasuwancinsa, ta yadda ake kwashe masa kafa, tamkar kura da shan bugu; gardi da kwashe dukiya,  wasu baki na mamaye su. To abunda babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba. A matsayi na na yaro, sai na nemi karin sani akan dalilan da yasa Hausawa suke komawa baya a fannoni da dama, a nan ne bincike na ya bayyana abubuwa da yawa kamar rashin iya tafiyar da kasuwanci, da rashin iya tafiyar da shugabanci komai kankantarsa. Ba shakka, wannan babban kalubale ga kowace irin al’umma, domin shi ne abincin da zai ciyar da ita ga, shiyasa muka fara shawarwari akan yadda zamu taimakawa manoman Hausawa sayar da amfanin gonarsu a kasashen waje.

A wannan yunkuri ne, muka gane cewa, akwai rashin mattatara ko ma’adana ta bayanan manoma, da abinda ya shafi kasuwaci da sana’o’in Hausawa. Daga nan ne muka tsara tambayoyin bincike (Questionnaire) muka aikawa jama’a, domin fahimtar bukatunsu, da kuma yadda suke tafiyar da wasu muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarsu na yau da gobe. Anan ne muka fahimci abubuwan dake daukar lokacin su, da kuma irin bukatun su. To, zamu iya kawo tsarin da zai hada wadannan batutuwa a waje daya domin samun nasararsu.

Haka kuma, binciken kuma ya nuna mana cewa jama’a musamman matasa da matan aure tsakanin shekaru 18 zuwa 35 suna sha’awar sana’a ko kasuwanci, amma basu da dandali nasu na kansu da zasu koya, ko su koyar da baiwar da Allah ya basu ga al’umma domin bada tasu gudunmuwa. Shafuka kamar Facebook na bayar da dandali na yin talla da koyo, amma abun babu tsari, saboda manhajar zumunta ce. Haka zalika WhatsApp, amma shima bashi da tsari, kuma yana da wahalar samun bayanai da ake nema. To amma kuma jama’a suna sha’awar duka biyun, shi ne muka ce to me zai hana a samar da tsari da jama’a zasu iya tallata hajar su, su kuma ringa sada zumunci suna gaisawa da kokarin sanin juna. Mun yi imanin cewar idan muka gina al’umma mai karfi da jin dadin alherin dake cikin wannan Kasuwa, wannan zai harzuka manufar mu na mayar da Kasar Hausa cibiyar kasuwancin yanar gizo a yammacin Afirka.

A takaice, manufar mu shi ne, amfani da fasaha wajen saukaka rayuwar Hausawa ta hanyar saukaka saye da sayarwa da sufur da samun ilimi da bunkasa fasaha da kiwon lafiya da nufin mayar da ‘yan kasuwa Hausawa mafiya arziki a nahiyar Afirka ta hanyar mamaye wannan fanni kafin ragowa su farga. Masha Allah, alamu na nuna cewa muna kan alkibla mai kyawu. Wannan shi ne a takaice manufar kafa wannan kasuwa tamu a yanar gizo.

DNH: Ka yi mana Karin bayani akan taken da kuke cewa Kasuwar Ku Ce? Ba kune kuka mallake ta ba?

Bello Galadanchi: Da aka ce Kasuwar Bello Kasuwar Ku Ce, wannan ba take bane kawai. Tun kirkirar wannan Kasuwa kasancewar an ga mutane da yawa suna da ra’ayi daya, da kuma sha’awar tsari irin wannan. Tun wannan lokaci, duk wani mataki da aka dauka, sai an tambayi ‘yan Kasuwa sun bada shawarwari, har aka kai ga nan.

Duk wanda yake sha’awar mu’amala da Kasuwar Bello, kofa a bude take, shiyasa muke da ‘yan jarida da marubuta da malamai daban daban saboda suna zuwa domin bada tasu gudunmuwa ga al’umma da kuma nuna irin baiwar da Allah Ya basu. Bugu da kari shago kyauta ne, saboda haka ai babu shakka Kasuwar Bello kasuwar jama’a ce.

DNH: Ko akwai kalubale a wannan aikin?

Bello Galadanchi: Babu shakka muna fuskantar Kalubale. A lokutan baya mun fuskanci lokuta da adadin mutanen dake bukatar mu’amala da Kasuwar Bello da samun kulawa ta musamman ya zarta kiyasin da muka yi a lokacin rubuta tsarin Kasuwar a takarda, dama kuwa babu wanda ya san gaibu sai Allah. Yadda jama’a suka yi rububin shigowa da samun alheri a dan karamin lokaci, wannan ya harzuka mu. Sai dai duk yawan mu da karfin mu, da sababbin hannaye da muke horaswa kafin zuwansu, lokutan basa isa kwata-kwata. Wani lokacin idan ba’ayi sa’a ba, sai suyi zuciya suyi fushi da tafiyar su.

Haka zalika fasahar mu na jawo kalubale, saboda adadin jama’a dake hawa, amma akwai sababbin tsare-tsare masu matukar ban sha’awa da sai an gama gina su baki daya kafin a dora akan yanar gizo. In sha Allah a wannan lokaci, wata sabuwar duniya zata bude a rayuwar yau da gobe ta Hausawa. Muna addu’ar isowar wannan lokaci a halin yanzu da muke aiki babu dare babu rana domin kammalawa akan lokaci. Muna rarrashin ‘yan Kasuwar da suka yi fushi, akan su dawo, zamu kara kaimi da aiki tukuru domin biya muku duka bukatunku.

DNH: Su waye masu taka rawar gani wajen tafiyar da harkokin yau da gobe na Kasuwar Bello?

Bello Galadanchi: Ina, ai wannan tambaya tana bukatar amsa ta musamman. Nima ko da wasa ba zan fara ba, ganin irin girma da bangarori daban-daban na Kasuwar Bello a halin yanzu. A kowane bangare a Kasuwar, akwai wanda yake taka rawa ta musamman kuma shiyasa kullum kasuwar ke kara farin jini da karbuwa a kasar Hausa da sauran kasashen duniya inda akwai Hausawa. Shiyasa zan baiwa duk wanda yake sha’awa shawara akan yayi kokarin shiga groups na WhatsApp na Kasuwar Bello domin kulla alaqa da su.

DNH: Me kuke hasashe Kasuwar Bello zata kasance a shekaru nan gaba?

Bello Galadanchi: Muna kiyasin sama da shaguna dubu dari bakwai da saba’in bisa alkaluma, lamarin da zai janyo hankulan turawa da jama’ar kasashen ketare domin dubawa su nemi irin kayan da babu a wajen su. Anan kaga mun ci nasarar kusantar da mai haja wato kaya da kuma masu saye cikin sauki.

DNH: Wanne fanni kuka fi mayar da hankali akai?

Bello Galadanchi: Eh to, fannin da muka fi mayar da hankali akansa shi ne, na NOMA. Burin kasuwar Bello shi ne samarwa manomanmu na kasar Hausa kasuwar kayan da suka noma inda zasu sayar su ci riba mai yawa, muna son kawar  da batun nan na cid a gumin manomanmu da ake, su sha wahala su noma amfanin gona amma a saya bad a daraja ba a wajensu, amma idan an fitar da kayan aci kazamar riba, su kuma wanda suka yi noma sun kare ba tare da samun wata riba ta ku zo mu gani ba. To muna son yadda manomin da yayi nomansa ya sayar da kayansa da kansa a kasuwar Bello ta hanyar hada shi da masu saye daga kasashen duniya.

Harkar noma na daya daga cikin tushen kafa Kasuwar Bello, kuma dolen-dole mu rike noma hannu bi-biyu saboda a nan karfin mu yake a Kasar Hausa. Kasuwar Bello ta kwan biyu tana shirye-shirye akan tanadin da zai samar da tsarin auna inganci amfanin gona akan wani sikelin da kasashen waje zasu gani su amince da shi. Wannan zai bude hanyoyi masu yawa na sayar da amfanin gona na Hausawa zuwa kasashen waje. To a halin yanzu manoma a Kasuwar Bello basu da yawa sosai, kuma ana bukata su bude shago su tallata kayan su. Wannan zai bamu damar tsara shiri da zai budewa manoma da masu bukata ido ta yadda zasu san inda kaya keda daraja, da kuma inda ake bukata cikin sauki.

 

Categories
Cinikayya Labarai

CBN ta saki dalar Amurka miliyan 210 a kasuwar canji

 

Hassan Y.A. Malik

A wannan makon ma dai, babban bankin Nijeriya (CBN), ya sake sanya dalar Amurka miliyan 210 a kasuwar hada-hadar canji domin wadatar da ‘yan kasuwa da ma duk mabukata dalar Amurka don dakile karancinta a kasuwar canji, wanda hakan ka iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci na yau da kullum.

A wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin, Isaac Okorafor ya fitar a jiya Litinin a Abuja, ya ce, an saki dala miliyan 100 ga manyan ‘yan canji masu lasisi don sayar da shi ga mabukata.

Inda su kuma kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da ake kira da SMEs suka samu dala miliyan 55. Su kuma masu bukatar dalar don biyan kudaden makaranta, biyan kudaden magugunguna ko biyan kudaden asibiti a kasashen ketare da kuma wadanda ke da bukatar dalar a matsalayin alawus dinsu na tafiye-tafiye da ma’aikatu kan tura jami’ansu wato Basic Travel Allowance (BTA), suma suka samu dala miliyan 55.

Okorafor ya dada jaddada manufar babban bankin na tabbatar da samun wadatar dala a kasuwar canji ta yadda za a ci gaba da samun saukin mu’amala da kuma tabbatar da karbabben farashi.

Ya ci gaba da cewa, CBN zai ci gaba da gudanar da kasuwar canji ta hanyar rage adadin kayan masarufin da ake shigo da su daga waje tare kuma da kara karfin taskar kasar na kudaden waje.

Ko a ranar 12 ga wannan watan ma dai sai da CBN ta saki dala Amurka miliyan 210 don biyan bukatun dalar da ‘yan kasar ke da su a bangarori daban-daban na mu’amalar yau da kullum da kuma cinikayya.

Har yanzu dai Naira ta tsaya a darajarta na N30 a kowace dalar Amurka a kasuwannin canji na bayan fage.

Categories
Cinikayya Labarai

Bankin duniya zai baiwa Najeriya bashin dala miliyan 486 don inganta wutar lantarki

 Hassan Y.A. Malik

Bankin bayar da lamuni na duniya IMF, a yau Juma’a, ya bayyana cewa ya amince da bawa Najeriya bashin dalar Amurka miliyan 486 don inganta harkakokin wutar lantantarkin kasar.

A ta bakin bankin, “Hukumar rarraba wutar lantarki ta Najeriya ta nemi wannan bashi ne, a matsayin wani jari da za ta zuba wajen inganta samar da wutar lantarki tare da rarraba shi a fadin kasar ta hanyar yin amfani da kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasar.”

Bankin duniya ya ci gaba da cewa, an dade ana kalubalantar Nijeriya bisa rashin iya samar da wutar lantarki a fadin kasar, lamarin da ake bayyanawa a matsayin dalilin da ya haddasa tsaiko a ci gaban tattalin arzikin kasar. A Nijeriya, masana’antu da gidanjen zama na al’ummar kasar na fama da karancin wutar lantarki.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya bankin ya yanke hukuncin tabbatarwa da Nijeriya bashin don kasar ta inganta al’ummarta da wutar lantarki.