Categories
Duniyan Labarai

Sifeton ‘Yan sanda na kasa ne ke da alhakin duk abinda ya same ni – Saraki

Shugaban Majalisar dattawa ya kasa Bukola Saraki ya kalubalanci ‘Yan sanda a lokacin da suke baiwa ‘yan daba da suka farmasa kariya a Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Haka kuma, Saraki ya kalubalanci Sifeton ‘Yan sanda na kasa akan yadda yake shiga harkar abinda ya Shafiu jihar Kwara musamman a Siyasance.

A saboda haka, Saraki ya bukaci ‘Yan Najeriya da su kalubalanci Sifeton ‘Yan sanda akan duk abinda ya shafe shi shi da iyalansa.

Saraki na yin wannan bayani ne a shalkwatar yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar PDP ta kasa dake Abuja yayin da yake ganawa da manema labarai.

Categories
Duniyan Labarai

Ilham Omar: Musulmar da ta lashe zaben majalisar dokokin Amurka

Musulma ta lashe kujerar majalisar wakilan Amurka daga jihar Minnesota, Ilhan Omar wadda ta yi takarar a jam’iyyar adawa ta Democrat, ‘yar asalin kasar Somaliya ce, kuma ta doke Jennifer Zielinski ta jam’iyyar Republican ne a zaben rabin wa’adi da aka yi ranar Talata.

BBCHAUSA.COM

Categories
Duniyan Labarai

Shugaba Buhari ya ziyarci birnin Fatakwal dan kaddamar da ayyuka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci birnin Fatakwal a jihar Ribas domin kaddamar da wasu ayyuka da suka kunshi sabon filin jirgin saman Fatakwal da aka sake inganta shi.

Categories
Duniyan Labarai

Yau za a binne gawar Kofi Anan a Ghana

A yau Alhamis be ake sa ran Shugaban kasar Ghana Nana-akupo Addo zai jagoranci binne gawar tsohon Sakataren majalisar dinkin Duniya Kofi Anan wanda ya mutu kwanakin baya a kasar Suwizalan.

Tuni dai aka kawo gawar ta Kofi Anan zuwa mahaifarsa domin bikin binne shi.

Categories
Duniyan Labarai Labarai

An kubutar da dukkan yaran da suka makale a kogo a kasar Thailand

Hukumomi a Thailand sun tabbatar da ceto sauran yara 5 da suka rage a kogon kasar yau din nan bayan tun farko an iya ceto 13 da Kociyansu. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka ilahirin yaran na karbar kulawar gaggawa a Asibiti la’akari da yadda suke a galabaice.

Cikin wasu bayanai da ta wallafa a shafinta na Twitter rundunar sojin ruwan kasar ta ce an kubutar da ilahirin yaran ko da dai wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali haka zalika jami’i guda ya rasa ransa.

A ranar 23 ga watan jiya ne, yaran da shekarunsu ke tsakanin 11 zuwa 16 da kuma kocinsu mai shekaru 25, suka shiga cikin kogon Tham Luang a dai dai lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin-kwarya bayan sun kammala atisayen kwallon kafa.

A ranar 24 ga watan na jiya ne, jami’an tsaro suka gano sahun kafa da na hannu na wadannan yara a hanyar kogon, lamarin da ya sa aka fara gudanar da aikin neman su.

A ranar 25 ga watan Yuni ne, wasu sojin ruwa kuma gwanayen ninkaya suka kutsa cikin kogon, yayin da aka kafa wata rumfar wucen-gadi don gudanar da addu’o’in ceto yaran.

A ranar 26 ne kuma, gwanayen ninkayar suka isa wata mahadar hanya mai tazarar kilomita mai yawa zuwa cikin tsakiyar kogon, amma sun gaza karasawa ciki saboda ambaliyar ruwa wadda ta toshe mashigin wurin da yaran suka fake.

A kashe-garin ranar ne, wata tawaga da ta kunshi kwararru daga Amurka da Birtaniya ta iso Thailand don ceto yaran.

Bayan shafe wasu ‘yan kwanaki , gwanayen ninkaya suka yi nasarar gano yaran 12 da kocin nasu a raye, yayin da a ranar 3 ga wannan wata aka isar da abinci da magunguna ga yaran duk da cewa, za su ci gaba da zama a cikin kogon kafin kammala dabarun futo da su.

Sai dai a ranar Lahadi ne aka fara ceto yaran daya bayan daya inda aka kammala aikin ceton a yau Talata.

RFI.HAUSA.FR

Categories
Duniyan Labarai

An Kasa Cimma Matsaya a Tattaunawar Sudan Ta Kudu

An kammala tattaunawa tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da jagoran ‘yan tawaye Riek Machar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ba tare da cimma wata yarjajjeniya ba, to amma watakila mutanen biyu za su sake ganawa, mai yiwuwa ma nan da sati biyu a birnin Khartoum na kasar Sudan.

Ministan Yada Labaran Sudan Ta Kudu Michael Makuei, wanda ya dawo Juba daga Addis Ababa jiya Jumma’a, ya gaya ma manema labarai cewa Majalisar Ministocin kungiyar kasashen kuryar Afirka, IGAD a takaice; sun ayyana kawo karshen ganawar ta Addis Ababa.

Ya ce Shugabannin kungiyar ta IGAD sun yi kira ga Kiir da Machar da su cigaba da tattaunawa kan batutuwan da har yanzu su ke da sabani; su kuma amince su gana a Khartoum babban birnin kasar Sudan a sati mai zuwa, sannan in ta yiwu, a yi taro na gaba kuma a birnin Nairobin Kenya.

Wakilan Kiir da Machar duk su ma sun tabbatar cewa ba a cimma jituwa a ganawar ta Addis Ababa ba.

VOAHAUSA.COM

Categories
Duniyan Labarai

Shugaban kasar Afirka ta kudu, Ramaphosa zai bayar da rabin albashinsa ga mabukata

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa ya yanke hukuncin raba albashinsa biyu, inda za a na sanya rabin a wani asusun tallafawa mabukata.

Asusun wanda za a sanyawa suna Nelson Mandela Thuma Mina Fund zai kasance ne a karkashin asusun Nelson Mandela, kamar yadda shugaban ya fadawa ‘yan majalisar kasar a yau.

Ya ce banda na shi albashin, za a janyo hankalin ‘yan kasar da za su iya bada wani kaso na albashin su domin a yi amfani da su waje yin kananan ayyukan da ke gina kasa.

Ramaphosa dai ya na daukan albashin rand miliyan 3.6 wanda ya yi daidai da dala 293,000 a kowacce shekara.

Categories
Duniyan Labarai

An jefe matar da ke auren maza 11 a Somalia

Daga Hassan Y.A. Malik

Mayakan kungiyar Al-shabab sun jefe wata mata mai shekaru 30 a duniya a bisa zargin ta da auren maza har sau 11, a cewar mazauna wani gari a kudancin kasar Somalia.

Wannan lamari dai ya faru ne a jiya Laraba.

Mazauna garin mai suna Sablale sun halarci wajen da aka jefe matar mai suna Shukri Abdullahi.

“An gurfanar da Shukri Abdullahi da anihin mijinta da sauran mazaje 9 a gaban kotun kungiyar al-Shabab, inda kowanne daga cikin mazajen ke ikirarin cewa shi ne ainihin mijinta,” Mohamed Usama, gwamnan al-Shabab na yankin Shabelle Lower, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kungiyar al-Shabab dai na daya daga cikin kungiyoyin ta’addanci duniya, inda ta ke ikirarin yunkurin kafa daular Musulunci a kasar Somalia.

Mambobinta sun sha yanke hukuncin yanke hannu ga mutanen da aka kama da laifin sata tare da jefe wanda aka kama da laifin zina.

Hukuncin na su ya na hawa kan maza da mata ne.

Categories
Duniyan Labarai

Malaysia zata daure duk wanda aka samu da yada labarin karya shekaru 10

Daga Hassan Y.A. Malik

Gwamnatin kasar Malaysia a yau Litinin ta fitar da wata doka da nufin kawo karshen yada labaran kanzon kurege a fadin kasar.

Dokar ta yankewa duk wanda ya yada labarin da bashi da majiya ko tushe da gangan zaman gidan kaso na shekaru 10.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ta rawaito cewa kasashe da dama za su kafa irin wannan dokar ta yaki da labaran karya bisa jagorancin Shugaba Donald Trump na Amurka duk kuwa da kalubale da dokar ke samu daga kungiyoyin jama’a na cewa shugabannin kasashen da ke son dabbaka dokar shugabanni ne da ke da sha’awar shimfida kama karya a kasashensu.

Ana zargin Firayi Ministan kasar Malaysia, Najib Razak da kafa wannan doka da nufin yi wa abokan hamayya bita da kulli sakamakon kalubalantarsa da suke yi da wawushe kudade daga baitul malin gwamnati tare

Shugaban ‘yan adawa, Charles Santiago ya bayyana kudirin dokar a matsayin wani makami mai linzami da gwamnati ta fitar don yakar ‘yan adawa a kasar.

Categories
Duniyan Labarai

‘Yan sandan Abuja sun cafke ‘yan fashi 30 da suka addabi al’ummar birni

Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan Sandan birnin tarayya Abuja ta bayyana kama wani gungun ‘yan fashi da makami da suka dade suna addabar rukunin gidaje na gwamnatin tarayya mai suna Sauka Federal Housing Area.

Majiyarmu ta bayyana cewa ‘yan fashin da adadinsu ya kai 30 na tsaka da yin fashi akan hanya ne a lokacin da ‘yan sanda suka samu kiran yawa cewa akwai ‘yan fashi akan hanya, inda nan take suka garzaya wajen.

Da isar ‘yan sandan ne fa sai suka shiga artabu da ‘yan fashin, inda a nan take ‘yan sanda suka harbe ‘yan fashi biyu suka mutu, uku kuma suka tsere da raunika, inda aka cafke wasu ukun.

An samu ‘yan fashin da bindigu kirar Hausa, talabijin na bango guda 9, takalma da kuma wuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Manzah Anjugri ya tabbatar da faruwar wannan labari, inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bawa ‘yan sanda hadin kai don kawar da masu laifi a fadin birnin tarayya Abuja.

Manzah ya ce, “A wani fita aikin da muka yi ma mu n kama wasu mutum shida a yankin Banex a lokacin da muke caje ababen hawa. Mun yi nasarar kwato bindigu da tabar wiwi daga hannunsu. Za mu ingiza keyarsu zuwa sashen bincike na hukumarmu don gudanar da bincike akansu.”