Categories
Kanun Labarai

Buhari ya kaddamar da tashar jirgin ruwa ta farko a Arewa

Categories
Kanun Labarai

Badakalar Ganduje: Buhari na tantamar zuwa Kano yakin neman zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba lallai ne yaje jihar Kano yakin neman zabe ba, saboda abinda Gwamnan Kano Ganduje ya aikata na karbar cin hanci a wani faifan bidiyo na Gwamnan da Daily Nigerian ta Wallafa.

Shugaba Buhari yana magana ne jiya a fadar Gwamnati yayin da yake tattaunawa da manyan jami’an yakin neman zabensa.

Daya daga cikin ‘Yan kwamitin Sanata Bashir Garba Lado ne ya tambayi Shugaban kasa akan a jinkirta zuwa jihar Kano da Legas sabida yawansu.

Sai Shugaba Buhari ya bashi amsa da cewar “Jihar Kano da aka nuno Gwamna yana karbar cin hanci yana murna” a cewar Shugaba Buhari ba lallai ne yaje Kano yakin neman zabe ba sai in “ya zama dole “.

 

Categories
Kanun Labarai

Mataimakin Shugaban PDP da aka dakatar ya koma APC

Mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP na kasa shiyyar Arewa da aka dakatar Sanata Babayo Garba Gamawa ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ne ya jagoranci Sanata Gamawa zuwa fadar Shugaban kasa dake Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja domin ya mika mubayi’arsa ya Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Categories
Kanun Labarai

Gwamnan Borno ya fashe da kuka a gaban Buhari

A yayin da dattawa da shugabanni na jihar Borno suka kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar Gwamnatin tarayya dake Aso Villa, Gwamnan jihar Borno Kasheem Shettima ya fashe da kuka yayin da yake yiwa Shugaban kasa bayani kan ta’adin ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Categories
Kanun Labarai

Aisha Buhari ta kaddamar da yakin neman zaben Buhari a Kano

Uwar gidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman sake zaben Shugaba Buhari a karo na biyu a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Hajiya Aisha Buhari ya kaddamar da gangamin taron a shiyyar Arewa maso yamma wanda aka yi a birnin Kano. Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da uwar gidansa Hajiya Hafsah Ganduje.

Categories
Kanun Labarai

Zamu samar da cibiyar tunawa da Shehu Shagari – Buhari

Yayin da ya isa jihar Sakkwato domin yiwa Gwamnati da iyalan Tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari ta’aziyar rasuwarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhinin sa na rasuwar Shagari. Ya Kara da cewar dole ne Gwamnati ta samar da cibiyar tunawa da tsohon Shugaban kasar akan irin gudunmawar dabya bayar don ciyar da Najeriya gaba.

Shugaban kuma yayi bayanin cewar babu wata tsattsamar dangantaka tsakaninsa da marigayi Shehu Shagari kamar yadda wasu ke tunani.

Categories
Kanun Labarai

Ku zabi nagartattun ‘yan takara a duk inda suke – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jira ga ‘Yan Najeriya da su zabi nagartattun mutane masu amana a yayin da zaben 2019 ke kara kusantowa.

Shugaban yayi wannan kiran ne a yayin da Shugaban Tetfund Baffa Bichi ya wakilce shi a wajen taron Maukibi na darikar kadiriyya da ya gudana a karshen makon da ya wuce.

Haka kuma, Shugaban ya bayyana cewar Gwamnatinsa tayi abin a zo a gani a lokacin da ta yi a mulki, kuma zata sake dorewa idan ‘Yan Najeriya suka zabe ta.

 

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban hadakar zauren majalisun dokoki da na dattawa.

‘Yan majalisun dokoki na tarayya sun dinga ihu tare da fadin Sai Buhari a lokacin da Shugaban ya iso zauren majalisar wakilai ta kasa domin gabatar da kasafin kudin.

Categories
Kanun Labarai

‘Yan bindiga sun kashe Alex Badeh

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe tsohon Shugaban hafsan sojojin sama na Najeriya Alex Badeh.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya yi bikin cika shekaru 76 a ranar Litinin

Cikin raha, a yayin da ake murnar bikin cikarsa shekaru 76 a fadar Gwamnati dake Aso Villa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci makisantansa da su daina rage masa shekaru.

Shugaban dai bai yi karin bayani ba akan ko shekarunsa 76 ne ko kuma 77 kamar yadda wasu ke zargi.

Shin wane sako zaku baiwa Shugaba Buhari a yayin da yake bikin zagayowar ranar haihuwarsa.