Categories
Nishaɗi

Munir Dan Iya ya lashe zaben fidda gwani na PDP a Sokoto

Tsohon kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Sakkwato Alhaji Munir Dan Iya shi ne ya lashe zaben fidda gwani na Gwamnan jihar Sakkwato karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Baturen zaben jihar Bashir Yuguda shi ne ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a yau, inda ya samu kuri’u 2,175.

An gudanar da wannan zaben ne karkashin kulawar tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da kuma Gwamna mai ci Aminu Waziri Tambuwal.

Categories
Nishaɗi

Labarin Bakano da Bazaazage da kuma Bazamfare a Muzdalifa

Labarin Bakano da Bazazzage da Bakatsine da kuma Bazamfare.
Jiya na samu kaina a MUZDALIFA bayan na baro Arafa ‘yan uwa na suka bace min, bani da abin shimfida, sai na ga wasu Kanawa sun shimfida kwali su uku sai na dan raba na kwanta sai naga suna hararata, nayi musu sallama shiru, sai dayan su yace Malam akwai mai wajen sai na dan matsa, ina gani suka sayo abinci da naman kaza da lemo amma babu Wanda yayi min Bismillahi, suka cinye kayan su tass, ina nan zaune wajen 12 dare can sai ga wani Bazazzagi ya hango ni a gefe yazo ya gaishe ni kafin kace kwabo yaje ya sayo min shinkafa kaza, ya kawo, na fara ci ke nan sai ga wani Bazamfare yaje ya kawo ruwa, can sai ga wani Bakatsine ya kawo lemo da shayi, sai na fara tunani ko ina karamcin mutanen Kano, ko Kuma Wadannan ba Asalin tsatson Kanawa bane. ko Kuma Zazzagawa da Zamfarawa da Katsinawa sun kwace musu karamcin ne.
Barkammu da Sallah
Allah ya karba mana.

Categories
Nishaɗi

Boyayyen labarin Jaruma Sadiya Idris da ya kamata ku sani

Daga Hassan Y.A. Malik

Sadiya Adam Idris na daya daga cikin jaruman Kannywood mata da suka sha fama da daraktoci da furodusoshi kan sai ta yi soyoayya da su sakamakon kyan diri da kyawawan idanu da Ubangiji ya yi wa jarumar.

Wannan dalili ne ma ya sanya furodusoshi suka yi ta rige-rigen sanya ta a manyan finafinai kuma suka yi ta biyanta manya kudade sama da tsararrakinta don su samu kanta, dalilin da ya sanya cikin dan kankanin lokaci ta yi shuhura.

Sai dai wani abinda mutane basu sani ba game da Sadiya Adam shi ne, Sadiya yarinya ce mai rikon addini, domin ma kuwa bincike ya nuna cewa tana daya daga cikin kalilan na mata jarumai da za su iya kawo Baqara zuwa Nasi.

A lokacin da  Sadiya ta zo Kano shekaru 4 da suka gabata, ta hadu da wani matasshin dan kasuwa mai suna Sanusi Ahmad, wanda da ne a wajen Ciroman Kantin Kwari kuma mai unguwar Rijiya Biyu a cikin kwaryyar birnin Kano.

Sanusin ne ma ya kamawa Sadiya gida kuma ya kawata mata shi yadda ta ke bukata, kana kuma ya saya mata tsadaddiyar mota.

Wannan ya sanya abokan aikinta suka fara kyashinta sakamakon karbuwa da kuma babbar yarinya da ta zama cikin dan karamin loto.

Sai dai daukaka da kuma dukiyar da Sadiya ta samu sam bai dadata da kasa ba, hasali ma dai, sai ya kasance jarumar ta ci gaba da bayyana burin da ya kawo ta Kano na ta zama fitacciyar jaruma bayan nan kuma ta samu miji ta yi aure ta zauna a gidanta har abada.

Allah kuwa ya amshi addu’ar Sadiya domin kuwa ya bata duk abinda ta roka a zuwanta Kano. Ita da Sanusi suka shirya angwacewa a ranar 17 ga watan Nuwamban, 2017, amma kash! Sai shirin nasu ya gamu da tasgaru sakamakon son jarumi Ramadan Booth da ya kamata da har ya sanya ta nemi ta fasa auren Sanusi.

Ko da matsin lamba ya yi wa Sadiya yawa na cewa Ramadan fa ba aurenta zai yi ba sai ta saduda ta sake sanya ranar aurenta a matsayin ranar 1 ga watan Afrilu, 2018.

Nan ma dai sai aka sake samun matsala sakamakon kin amincewa da iyayen Sanusi suka yi na ya auri ‘Yar Fim’, kamar dai yadda majiyarmu ta bayyana mana.

Daga bangaren iyayen Sadiya ma dai an samu irin waccan matsalar sakamakon wai su sun fi amincewa da Sadiya ta koma gida Maiduguri ta auri dan uwanta.
Hakan ya sanya dole Sadiya ta tattara ya-nata-ya nata ta koma Maiduguri kuma ta daina ko yin waya da abokan aikinta na Kannywood.

Can daga baya kuma sai jita-jita ta ci gaba da yaduwa a industiri na cewa fa batun auren Sadiya a ranar 1 ga watan Afrilu, 2018 na nan ba a fasa ba sakamakon ganin kawayenta na kusa suna ‘yan shirye-shirye.

An dai daura auren a garin Kano a ma masallacin Umar Bin Khattab da ke shataletalen Dangi, inda kashegari amarya ta gayyaci kawayenta zuwa wani kasaitaccen walima a Magajin Rumfa da ke unguwar Nassarawa Kano, walimar da ta samu halartar tsofaffi da jarumai mata na wannan zamani.

wasegari dai har lau, Sadiya ta sake shirya wani bikin al’adarsu ta barebari da suke kira da ‘Wushe-wushe’, kuma shi ma ya samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki da dama daga ciki da wajen Kannywood., kuma an ci an sha daga abincin gargajiyar barebari.

Bayan an kai Sadiya dakinta ne sai ta rubuta a shafinta na Instagram cewa tana bukatar ‘yan uwa da abokan arzuka da su taya ta da addu’ar samun zaman lafiya a gidan mijinta.

Sai dai wata majiya ta ce wasu daraktoci da furodusoshin Kannywood basa yi wa Sadiya fatan ta zauna a gidan mijin nata, saboda basu koshi da samun riba daga irin rawar da jarumar ke takawa a finafinai ba, a cewar majiyar.

Categories
Labarai Nishaɗi

Sojoji sun cafke wani dan leken asirin masu aikata kashe-kashe a jihar Taraba

Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar sojojin bataliya ta 93, a jiya Lahadi ta cafke wani wanda a ke zargi da cewa dan leken asirin masu kashe-kashe ne, a yayin da ya ke kokarin binciko bayanai akan wani wanda za su kashe.

Dan leken asirin na fakon wanda suke harin ne a yayin da ya ke tafiya a mota a kan hanyar Takum zuwa Chanchangi a jihar Taraba a lokacin da sojojin suka kama shi.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na sojin Nijeriya, Birgediya Texas Chukwu, ya fitar ya bayyana cewa, wani mutum mai tafiyar kafa ne ne ya ji lokacin da shi  dan leken asirin ke magana da wani Malam Musa Ibrahim cewa ya shaida mutumin da za su kaddamarwa.

A lokacin da sojoji ke tuhumar wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa shi dan leken asiri ne da ke yi wa masu aikata muggan laifuka aikin leken asiri.

A yanzu haka dai wanda a ke zargin na hannun sojoji kuma suna ci gaba da tuhumarsa don samun wasu bayanan.

Categories
Nishaɗi

Shehu Jaha da masu fada akan Gurmi

Daga Danladi Haruna
Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfana gabansa ya daka musu tsawa ya ce, “me yake tafe da ku? Kun san nan kotu ce, ba a mana wargi anan!”
Daya daga ciki ya mike ya ce, “Allah ya gafarta Malam wannan gurmina ne aka dauke min yau kwana uku ina nemansa na ganshi a hannun wannan mutumin yana kadawa ana ba shi kudi. Na zo gabanka ne domin a karbar min kayana.” Alkali Shehu Jaha ya dubi wanda ake kara ya ce, “ka ji abin da ake kararka da shi. Haka ne? Dauke masa ka yi?” Mutumin ya ce, “gafarta Malam na tabbata dai ba nawa ba ne, amma shi ma ba nasa ba ne, tunda tsinta na yi a wuri kaza.”
Alkali ya ce da mai kara, “kana da shaidu? Kuma da wata alama a jikin gurmin naka?” Mai kara ya ce, “eh daga wuyan gurmin akwai inda aka yi ‘yar k’ofa inda ake dura mai saboda ya yi laushi, sannan daga kasansa akwai wata alamar maciji da na zana. Har ila yau akwai shaidu mutum biyu da suka san wannan gurmin nawa ne tun da jimawa.”
Alkali ya sa aka duba gurmi aka ga alamun da ya fada haka suke, sannan aka shigo da shaidu suka shaida tabbas gurmi mallakinsa ne. Ba tare da bata lokaci ba alkali Shehu Jaha ya sa aka kwace gurmi daga hannun daya aka mikawa mai shi. Sai kuwa wanda aka kwace gurmin daga hannunsa ya yi farat ya ce, “Allah ya gafarta Malam ban yarda da shaidun wadannan mutanen ba. Domin na farko yaron mai dafa giya ne, na biyu kuma dan wankin gidan karuwai ne.”
Shehu Jaha ya ce, “Shaidu sun cika yadda ake bukata, domin kayan banza mutanen banza ne ke shaida akansu. Da alk’urani ne ko wani abin kirki ba za mu karbi shaidunsu ba.”
Categories
Nishaɗi Siyasa

Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi fatali da karin lokacin da aka yiwa Oyegun

Reshen jihar Lagas na jma’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun sanya kafa sun yi fatali da batun karawa Shugaban jam’iyyar na kasa John Oyegun lokacin, domin cigaba da kasancewarsa Shugaban jam’iyyar, sun bayyana cewar wannan karin lokaci ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan sun tattauna da dukkan bangarorin jam’iyyar na masu ruwa da tsaki wanda suka halarta a ofishin jam’iyyardake Marina a Legas din, a cewar uwar jam’iyyar reshen jihar Legas.

A lokacin karkare zaman tattaunawar, Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewar, karawa Shugaban jam’iyyar na kasa lokaci, wannan abu ne da ya sabawa tanade tanade na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Mista Oyegun dai na zaman doya da manja ne a yanzu haka tsakanin da jagoran jam’iyyar na kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne ke juya jam’iyyar reshen jihar Legas.

“Sashi na 223 a cikin kundin tsarin mulkin 1999, yayi bayanin hanyoyin da ya kamata abi idan wa’adin Shugaba ya kare a matakin shugabancin jam’iyya”

A cewar uwar jam’iyyar wannan sashi na 223 a kundin tsarin mulkin Najeriya yayi bayanin hanyoyin da ya kamata abi idan lokacin mai rike da mukamin Shugaban jam’iyya ya kare, ba irin yadda aka yi ba.

Haka kuma, sashi na 17 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya nuna cewar Shugaban jam’iyyar zai yi wa’adin mulki na shekaru hudu ne kawai, wanda kuma ana iya sake sahale masa wasu shekaru hudun masu zuwa. sabanin abinda aka yi.

A lokacin da yae zantawa da manema labarai, abayan kammala zaman taron, Shugaban jam’iyyar reshen jihar Legas ta tsakiya, Tajudeen Olusi, yace yanke hukuncin da majalisar zartarwar jam’iyyar ta kasa ta yi na karawa Mista Oyegun shekara daya ya saba da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.

 

Categories
Nishaɗi

Saraki ya kyauta kan batun ‘yar wasan barkwancin nan Emmanuella

Daga Anas Saminu Ja’en

Duk da ba a taru an zama daya ba a Social Media din akwai mutane gurbatattu amman kuma akwai masu kirki masu ilimi wadanda suka san ya kamata, A yankin Arewa an dauki duk wani wanda zai dauki waya ya yi rubutu a matsayin dan zaman banza wanda bai san ciwon kansa ba. Abun da mutane suka manta shi ne kowane dan adam yana da baiwar da Allah ya yi masa ta kowane fanni na rayuwa.

Misali: Akwai da yawa matasa a arewa masu amfani da wayoyin hannu na zamani suke rubuce-rubuce na nuna kauna da kare martabar wani ko wata musamman a bangaran siyasa, kaga matashi ya yi bakin jinin duniya a zageshi a ciwa iyayen sa mutunci amman saboda takaici wanda yake karewa babu ruwansa da shi idan dan siyasa ne lokacin da ya samu nasara lokacin zai raba hanya da shi, babu ruwansa da tallafawa rayuwar sa.

Matasa suna amfani ne da basira da kudin su ya kamata a ce ana agazawa basirar ta su domin cimma ga ci ta fuskar karo karatu amman babu ruwan su, kuma abun takaicin shi ne zaka nuna rashin ko’inkula da wanda yake kaunarka babu dare babu rana, Ta ya wanda yake nuna maka waccar kaunar zai ji idan har ya fuskanci kai da yake yi domin kai kuma baka kaunar ci gaban rayuwar sa idan har ya waiwayeka ya dawo mai sukar ka.

Wannan abubuwan sune suke sakawa matasan arewa masu yin Social Media jin ciwo suna yin wahala dan mutun amman kuma shi ba ruwan sa da su ga dama ta samu a siyasan ce sai a haye su bayan kowa ba ya san ita fa siyasar nan ba dan Allah ake yin ta ba harka ce kurum ta biyan bukatar kai. ita kuwa zuciya tana bukatar mai kyautata mata a koda yaushe kuma ko ya ya ne, amman babu takaici kana nunawa mutun kauna amman shi da ‘yan uwan sa suna kallon ka dan iska suna ganin ai wayon su ne yake kai su matsayin da har kai kake son su kake kare musu mutuncin su.

Yanzu ku dubi shugaban majalissar dattawa Bukola Saraki inda yake neman kyautawa wadda yake kauna. kuma ya ajiye misali mai kyau ga ‘yan siyasa da sauran mutane, Ya gayyaci Yarinya Emmanuella mai yin wasan barkwanci zuwa gaban su a majalissa domin su tallafa mata da kudade wanda zata inganta harkokin ta na barkwanci, ka ji masu son ci gaban al’umma ga dukkan alamu Bukola yana jin dadin kallon wasan barkwanci kuma yake ganin tana bukatar taimako. Tabbas Emmanuella da iyayen ta, ‘yan uwa ta da kwayenta ba za su manta da Bukola Saraki ba domin ya kyauta sosai.

A arewa muna da matasa maza da mata masu basira ta huce tunani amman saboda da rashin matallafi sai mutun ya kare a cikin wahala, kuma babu mai kwatanta haka kullum shi yasa yara suke ciwa ‘yan siyasa zarafi a Social Media saboda ba su taimake su ba, amman kuma lokacin da suke neman kujerin da suke kai sun nemi taimakon matasan.

 

 

Categories
Nishaɗi

Kanawa! Abin Naku Ba Dama – Inji Dr. Aliyu Tilde

Yanzu na gama shan abarba a Zungeru Road inda ake min gyarar mota. Zanne kan benchi, bayan na sha abarba ta kai min karo, sai na tambayi mai-tallar abarbar ta nawa na sha.
Ya ce, “Ta Naira dari biyu.
Sai na sake habata, na ce: “Malam, yar wannan din?”
Ya ce, “Kwarai kuwa.”
Sai na yi ajiyar zuciya, na tambaye shi: “Hala kai Bakano ne dan na ganka da uku-uku a kuncinka.”
Ya ce, “E. Bakano, cikakkensa.”
Na ce, “Haba. Ai ba mamaki. Don tsakanin Bakano da Inyamuri ban san wanda ya fi son kudi ba. Kanawa dai mun san su da sane.”
Sai ya yi wuf, ya ce, “A da ne, ranka ya dade.”
Na ce, “To ai ka ji. Da kuka daina sane shi ne kuka koma satar mota ba?”
Ya ce, “To ai an gudu ba a tsira ba ke nan.”
Na ce, “Ni tun 1978, shekara arba’in ke nan, in na je Kasuwar Kurmi, hannu na dafe yake da aljihuna.”
Kafin in gama bayani, sai mai-abarba ya ce, “Wallahi ni ma a nan suka koya min hankali.”
Na ce, “Ya aka yi?”
Ya ce, “Ai da na je da gwaiba shekarun baya sai suka kira ni kamar za su saya. Suka mamaye ni wai bari su taya ni saukewa. Ashe yayin da wasu suke kama min tire, wani ya sa hannu a aljihun kirjina ya zare dan cinikin da na yi.”
Na tuntsire da dariya, na tambaye shi: “To ya ka yi?”
Ya ce, “Na bar su da Allah.”
Na ce, “Tab. “Ka ce dara ta ci gida.”
Nan na ba shi labarin yadda Kanawa suka sace wa yarona, Omer, mota a Farm Centre shekaru uku da suka wuce. Ya je masallacin juma’a latti, sai garin sauri don ya riski raka’ar karshe bai kulle kuloch ba. Ana idar da sallah ya yi sauri ya dawo wajen mota, sai ya ga wayam. Har yau! Kan ka ce kwabo an kai ta Sabongari an sassare ta wajen su Kachikwu.
Nan dai hirarmu ta kare da mai-abarba. Na ciro N200 zan mika mar sai na ce, “Ko za ka yi sadaka da dari daya ne, in baka dari kawai?”
Ya dara, ya ce, “A yi haka, yallabai?”
Na ce, “Ato. Ai kanawa ba sa sadaka. Mabaratansu ma fata suke baki Zagezagi su shigo birni don su sami na kashewa. Ka san sadaka sai masu ilimi, ba yan sane ba.”
Ya ciccibi tiren abarbarsa ya dora a ka. Ban tallafe shi ba, kalen ya yi tsammani zan zare mar aljihu yadda aka taba mar a Kasuwar Kurmi.
Abin na Kanawa da ban mamaki.
Categories
Nishaɗi Wasanni

Yadda ta kasance a gasar tseren dogon zango na ‘Lagos Marathon’ da bankin Access ya dauki nauyi

 

Gasar tsere mai nisan zango karo na uku da ake kira a turance da Lagos City Marathon na bana ya fara da misalin karfe 6:30 na safiyar yau Asabar.

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Austin Jay-Jay Okocha da takwaransa na tawagar kwallon kwandon Nijeriya, Olumide Oyedeji sun halarci wajen mika kyaututtukan ga wadanda suka yi nasarar lashe gasar ta bana, kuma sun yabawa wadanda suka shirya gasar tseren da ma duk wadanda suka bayar da gudunmawarsu wajen ganin gasar ta bana ta yi nasara.

Tseren da zangonsa kilomita 42 ne ya fara ne daga filin wasanni na kasa da ke Surelere inda ya kare a Eko Atlantic.

Taron na bana ya samu akalla mutane 100,000 da suka shiga gasar, wanda Okocha ya bayyana cewa wannan ba karamin ci gaba bane ga ci gaban harkar wasanni a kasar Nijeriya.

 Bafuranshe, Abraham Kiprotich, ne ya lashe gasar ta bana wacce bankin Access ya dauki nauyi. Kiprotich, wanda haifafen kasar Kenya ne kuma mai shekaru 32, ya kammala kilomita 42nsa a cikin awanni 2 da mintina 15 da sakan 4. Wannan ya bashi damar lashe kyautar dalar Amurka dubu 50 da aka sanya za a bawa duk wanda ya lashe gasar.
Iliya Pam, shi ne dan Nijeriyan da ya zo na daya a kafatanin ‘yan Nijeriyan da suka shiga gasar. Iliya, ya shanye kilomita 42 a cikin awanni 2 da mintuna 27

A yayin mika kyautukan, Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya bayyana cewa, “Har yanzu matsayin shirya gasar bai kai yadda jihar ta ke so ba, tunda bai kai yadda manyan kasashen duniya suke shirya nasu ba, amma nan da shekaru biyu masu zuwa, za mu kai inda muke burin kaiwa.”

“Mun gaji da mika kyautar gasar ga ‘yan Afirka ta gabas a duk shekara. Saboda haka za mu horar da masu tserenmu na gida Nijeriya ta yadda suma za su dinga yin nasara a gasa irin wannan,” inji Ambode.

Categories
Nishaɗi

Kurtun Barau tare da Danladi Haruna

 

Barau Gangariya wani hatsabibin mutum ne da ke iya sarrafa miyagun ƙwari ba tare da sun yi masa komai ba. Yakan ɗauki maciji ya rataya a wuya, ko ya riƙa sa kunama a baki ba ta cije shi ba.
Kowa na shakkarsa saboda hatsabibancinsa amma Malam Idi, wanda ake wa laƙabi  da Ta Faɗa. Shi Idi Ta Faɗa wani irin makwadaicin mutum ne ga yawan roƙo kamar ganyen rogo. A taƙaice dai, ya mayar da rok’o sana’arsa domin kuwa ko yaro k’arami ya gani yana tauna wani abu, ko yana tsotson alewa sai ya fisgi rabonsa daga gare shi. Bayan wannan  dabi’ar tasa ta rok’o sannan Allah ya hore masa tsananin rowa kamar na goye. Idan yana cin abu ya hango wani na tahowa cikin sauri sai ya jefa aljihu ya goge bakinsa kamar dad’ai duniya baya tauna komai.
Duk safiya idan zai fita daga gida ya kan yi karatun  Izawaqa ya shafa ya fita, idan ya samu wani babban mutum ya yi masa maula aka ba shi na goro sai ya kama murna yana cewa, “ta faɗa, ta faɗa” watau Izawaqa ta yi aikin nata.
Rannan ya fito sana’ar maula kamar yadda ya saba, ya zaga ciki da waje, sama da k’asa ya rasa ko sisin kwabo. Dauke batun kudi ma hatta ruwan da zai jika a mak’oshi a ranar nan rasawa ya yi. Ga shi ya yawata har ya gaji. K’ura duk ta bule shi budu – budu kamar wanda aka tono daga kabari.
Da ya gaji da bilumbituwa, sai ya haƙura ya kama hanyar gida domin ya huta. Daga nesa sai ya hangi Barau a kusa da tubani an zuba masa zai soma ci. Mutumin naka sai ya k’ara azama ya zauna gabansa, tun kafin Barau ya kai lomar farko shi ya kai ta uku.
Cikin fushi Barau ya tashi bar masa abincin yana ta zabga loma yana cewa, “ta faɗa, ta faɗa! dai yau bata faɗa da wuri ba.” Bayan ya k’are cinye abinci ya sha ruwa ya yi gyatsa ya kade rigarsa ya yi gaba.
Sai da Barau ya bari Malam Idi Ta Faɗa ya manta da wannan banzar da ya kwasa. Rannan ya dawo daga maula Barau ya hange shi yana tahowa. Ya yi sauri ya ɗauko wani kurtu  yana lakatar wani abu daga ciki yana tandar baki kamar yana shan kayan dad’i. Malam Idi na ganin haka yawun bakinsa ya tsinke, ya ce da shi “Barau me kake sha haka?” Barau ya ce yana tanɗar baki, “Zumumuwa ce kakar zuma.”
“Sammin kad’an mana.” In ji Idi Ta fad’a.
“To bismillah, lakaci kad’an amma fa kar ka shanye min duka na san halinka.”
Idi wanda tuni yawu har zuba yake ya mika hannu zai lakaci zumumuwa. Sa hannunsa ke da wuya cikin kurtu sai kuwa kunama ta gallara masa cizo. Ya cire hannun da sauri yana mai kwalla k’ara. Barau kuwa ya daka tsalle saboda murna yana cewa, “ta fada, ta fada!”
Ashe fisgar hannun da Idi ya yi wata kunama ta makale a hannunsa bai sani ba. Ta sauka akan hancinsa ta sake kwabɗa masa wani cizon. Ya gigice saboda da  azabar zafi. Barau kuwa ya sake daka tsalle yana cewa ta kuma fadawa! Ta kuma fadawa!”
Idi mai kwad’ayi ya tafi gida da kumaburarren hannu da hanci. Bayan ya jima yana jinya ya samu ya warke da kyar. Daga wannan ranar duk sa’adda zai fita bayan karanta izawaqa sai ya yi addu’a ya ce,, “ya Allah ka sa ta faɗa amma kar ta faɗa a irin kurtun Barau.”