Categories
Siyasa

Isa Ashiru ya kada Ramalan Yero a zaben fidda gwani na PDP a jihar Kaduna

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya sha Kaye a hannun tsohon dan majalisar wakilai na tarayya Isa Ashiru Kudan a zaben fidda gwani na Gwamnan jihar Kaduna karkashin tutar jam’iyyar PDP da ya gudana a ranar Lahadi a jihar Kaduna.

 

Categories
Siyasa

Ranar 6 ga Oktoba zamu fitar da dan takarar Shugaban Kasa – PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewar ya sanya ranar 6 ga watan Oktoba a matsayin ranar da zata fitar da dan takarar Shugaban Kasa da zai Kara da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

’Yan takarar neman jam’iyya ta amince musu yi mata takara a 2019 sun hada da tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo.

Sauran su ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Attahiru Bafarawa da Ahmad Makarfi da Kabiru Tanimu Turaki da tsohon Gwamnan jihar Plateau Jonah Janga.

Ragowar sune David Alachenu Mark da Datti Baba-Ahmed da sauransu.

Categories
Siyasa

Sokoto: Jam’iyyar PDP ta zabi Munir Dan Iya a matsayin dantakarar Gwamna

Daga Bilya Yariman Barebari

Jam’iyyar PDP a Jahar Sokoto, ta dunkule guri daya, ta fitar da Dan Takarar Gwamna a Jam’iyar a shekara ta 2019, inda duk wasu masu ruwa da tsaki na Jam’iyar PDP suka yarda da suka amince da Hon. Manir Dan Iya a matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto a karkashin wannan Jam’iya mai farin jini waton PDP Power.

Wani abin jim dadi tare da farin ciki, duk masu neman wannan kujerar ta Gwamna, tuni suka sallama masa tare da yi masa fatar alkhairi.

Sen. Ibrahim Abdullahi (Danbaba Dambua) da kanshi yace ya janye takarar shi, kuma zaya bayarda cikakken goyon baya don ganin an samu nasarar wannan tafiya.

Tun lokacin da aka aka ayyana Hon. Manir Muhammad Dan’iya, a wannan matsayin, nan take lungu da sakuna, cike da wajen Jahar Sokoto, sai kowa murna yake da wannan zabin da Allah ya yiwa Sakkwatawa.

Ko a Kafar Sadarwar yanar Gizo ta Social Media, kowa sai murna yake, babu masu kushe, kowa sai fatar alkhairi kawai suke yi.

Ta sakamakon tsayar da Dan’iya a kan wannan matsayi, tuni wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC, suka ce suna nan suna shirye shiryen sauya sheka zuwa Jam’iyar PDP mai taken Nasara.

Allah ya kara bamu nasara ga wannan tafiya mai alamar nasara.

Categories
Siyasa

Dalilin raba garina da Shekarau a Siyasa – Takai

 

Tsohon kwamishina a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a Kano, Malam Salihu Sagir Takai ya ce sun yi hannun riga da tsohon mai gidan nasa a fagen si.

Malam Salihu Takai ya jima yana mu’amala da Malam Ibrahim Shekarau tun gabanin shiga siyasa a 2003, kuma yana daga cikin kwamishinonin da suka fi fada-a-ji a lokacin gwamnatin Shekarau.

Takai ne dai Shekarau ya tsayar takarar gwamnan Kano a shekara ta 2011, sannan ya sake mara masa baya a 2015.

Malam Salihu Takai ya ce ya yanke shawarar zama a PDP ne saboda dalilan da Shekarau ya bayar na fita daga jam’iyyar ba su gamsar da shi ba.

Ya ce mafi yawan mutanen da ya tuntuba gabanin yanke hukunci sun ba da shawarar ya ci gaba da zama a PDP, kada ya koma jam’iyyar APC.

A yanzu dai Malam Salihu Takai ya ce ya koma bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tun da suna jam’iyya daya.

Sai dai ya ce duk da haka babu wani sabani tsakaninsa da Malam Shekarau a mu’amala, kawai dai a siyasance ne suka raba hanya.

Tuni dai Malam Salihu Takai ya yi mubaya’a ga shugabancin riko na jam’iyyar PDP a Kano karkashin Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwakwaso ne.

A ranar Asabar da ta gabata ne tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC bayan ficewa daga PDP saboda zargin rashin adalci wajen rusa shugabancin jam’iyyar a jihar.

To sai dai PDP ta musanta zargin na Shekarau.

An fara samun sabani ne bayan komawar Sanata Rabi’u Kwankwaso PDP a watan Yuli.

A baya dai Shekarau ya shaida wa BBC cewa yana maraba da shigar Kwankwaso PDP, kuma za su yi aiki tare domin kai jam’iyyar ga nasara a jihar Kano.

To sai dai tun tafiya ba ta yi nisa ba tsofaffin gwamnonin biyu suka raba gari.

Da ma wasu masharhanta al’amuran siyasa na ganin zai yi wuya Shekarau da Kwankwaso su iya zama a jam’iyya daya, saboda mummunar hamayyar da ke tsakaninsu, da kuma banbancin.

BBCHAUSA.COM

Categories
Siyasa

Atiku Abubakar ya nemi Sule Lamido ya janye masa takara

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP ya nemi Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da ya taimaka ya janye masa takara a wannan zaben na 2019.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a Sakatariyar jam’iyyar PDP dake birnin Dutse lokacin da ya kai ziyarar neman goyon bayan wakilan jam’iyyar da zasu yi zaben fidda gwani.

”Na girmi Sule Lamido dan haka ya dace ya janye takararsa ya kyale ni domin na gwada sa’ata a wannan karon” A cewar Atiku Abubakar

Categories
Siyasa

Kano 2019: Takai ya yanki takardun tsayawa takarar Gwamna

Malam Salihu Sagir Takai da ya yiwa jam’yun ANPP da PDP takarar Gwamna a zabukan 2011 da 2015 ya yanki takardar sake neman kujerar Gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Wannan shi ne karo na uku da Malam Salihu Sagir Takai yake neman takarar Gwamnan jihar Kano. A baya yayi takara a 2011 inda Sanata Kwankwaso ya samu galaba a zaben da tazara ‘yar kadan.

Sai dai a zaben 2015 Malam Salihu Sagir Takai ya kuma shan Kaye a hannun Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, masu sharhin Siyasa a jihar Kano na ganin cewar a wannan karon Malam Salihu Sagir Takai na Iya samun galaba akan Gwamna mai ci Ganduje, idan har PDP ta amince ya bashi takara.

A zaben bana dai za a samu gagarumin canji a jihar ta Kano, kasancewar tsaffin Gwamnonin jihar guda biyu Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da dumbin magoya baya, kuma na tare da jam’iyyar ta PDP.

Haduwar Shekarau da Kwankwaso a cikin inuwar jam’iyyar PDP babbar barazana ce ga sake komawar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, kasancewar su duka tsaffin Gwamnonin na da dumbin magoya bayan da zasu iya kayar da Gwamna Ganduje.

Daman dai ba abin mamaki bane a jihar Kano a kayar da Gwamna kai ci a yukurinsa na sake komawa, domin ko a 2003 Malam Shekarau ya kayar da Gwamna mai ci Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da shima Malam Shekarau yana Gwamna Kwankwaso ya kayar da dantakararsa Malam Salihu Sagir Takai.

A wannan zaben na 2019, jihar Kano na databank cikin inda za a fafata sosai, inda tsaffin Gwamonin jihar biyu zasu kalubalanci Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje. Shin ko PDP zata samu Nasara a jihar Kano? Lokaci je zai tabbatar da hakan.

Categories
Siyasa

APC ta Amince da yin ‘yar tinke a zabukan fidda gwani na jam’iyyar

Uwar jam’iyya mai mulki ta kasa APC ta amince da yin kato bayan katon a yayin zabubbukan fidda gwani na jam’iyyar a dukkan fadin Najeriya.

Sai dai kuma Gwamnonin jam’iyyar tun kafin wannan lokaci suka nuna kin amincewa da zaben fidda gwani ta hanyar ‘yar tinke ko kato bayan kato.

Uwar jam’iyya ta APC tace za a yi kato bayan kato tun daga kan zaben Shugaban Kasa har zuwa kasa.

Categories
Siyasa

An samu muguwar baraka a APC kan zaben fidda gwani

Wani rikici ya kunno kai a cikin uwar jam’iyyar APC ta Kasa kan batun hanyoyin da za a bi wajen yin zaben fidda gwani na wadan da zasu tsayawa jam’iyyar takara a mukamai daban daban.

Jagoran jam’iyyar na Kasa Bole Ahmed Tinubu da Shugaban jam’iyyar na Kasa Adams Eric Oshiomhole suka nemi abi wannan tsarin wajen fitar da wadan da zasu wakilci jam’iyyar a matakai daban daban a duk fadin Najeriya.

Sai dai kuma, Geamnonin jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamnan jihar Imo Rochas Owelle Okorocha sun ce Sam ba zata sabu ba kan wannan hanya da aka ce za a bi wajen fidda ‘Yan takarkarun Jam’iyyar.

A ranar Alhamis ne dai ake sa ran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zasu suke zama a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, domin tabbatar da hanyar da za a bi wajen yin zaben fidda gwani na karshe a cikin jam’iyyar.

Categories
Labarai Siyasa

Kwankwaso zai kaddamar da takararsa ta Shugaban kasa

A ranar Laraba je ake sa ran Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai kaddamar da takarar neman Shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’Iyyar PDP.

Sanata Kwankwaso na daya daga cikin mutanan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a baya bayan nan, kuma yana daga cikin na gaba gaba da suke neman jam’iyyar ta PDP ta basu tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa.

Ko a baya dai, Sanata Kwankwaso yayi takarar Neman tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta bashi tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa, inda ya zo na biyu a zaben fidda gwani, yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Nasara.

Categories
Siyasa

Wani kusa a jamiyyar APC a jihar Gombe ya koma PDP

Tsohon dan takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2011 karkashin rusasshiyar jam’iyyar CPC Abubakar Aliyu ya bayyana ficewar daga cikin jam’Iyyar ta APC zuwa jam’iyyar PDP mai mulkin jihar.