Categories
Labarai Siyasa

Gwamnan Binuwai Ortomya fice daga jam’iyyar APC

Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya bayyana cewar ya fice daga jam’iyyar APC bayan abinda ya kira “Jan kati” da jam;iyyar ta bashi.

Ortom ya bayyana hakan ne a ranarLitinin a babban birnin jihar Makurdi jim kadan bayan da ya rantsar da sabbin masu bashi shawara na musamman akan kananan hukumomi Jerome Shimba wanda ya maye gurbin Titus Zam.

A cewarsa, jan katin da jam’iyyar ta bashi, ya bashi damar shiga duk jam’iyyar da yaga dama, wadda ta dace da muradun al’ummar jihar.

Gwamna ya kara da cewar dangantaka tsakaninsa da jam’iyyar da ta bashi damarzama Gwamnan jihar a shekarar 2015 ta yi tsami matuka, ta yadda aka watsarda shi har ya kasance ba shi da jam’iyya.

 

Categories
Siyasa

Sule Lamido ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a Zamfara

Daga Mansur Ahmed
Da ranar yau Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido CON, tare da mambobin kwamatin yak’in neman zab’ensa sun ziyarci jihar Zamfara a cigaba da ziyarar jihohin Nigeria 36 domin ganawa da dattawa, shugabannin jam’iyyar PDP da masu ruwa da tsaki game da takarar shugabancin Nigeria a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.
Bayan karb’a ta karamci kamar yadda al’ummomin jihohin Kebbi da Sokoto suka yi masa jiya yayin da ya ziyarce su, jagoran ya ziyarci ofishin jam’iyyar PDP na jiha domin bayyana wannan kuduri ga shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da k’ananan hukumomin jihar daga bisani shugaban jam’iyyar ya mara mawa Jagoran baya domin bud’e ofishin yakin neman zabensa na Jihar Zamfara.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Sanata Hassan Nasiha yayin gabatar da jawabinsa ya fara da godiya ga jagoran talakawan bisa tsayawarsa tsayin daka wajen kare mutuncin jam’iyyar PDP a yanayin da ta shiga na fad’uwa zabe da rikicin shugabanci, ya gode masa bisa shawarwari na musamman da zasu amfanar dasu a jihohinsu da yake bayarwa a kowanne lokaci aka hisad’u, yace wajibi ne a yiwa Sule Lamido jinjina ko dan gwarzantaka da juriya da ya nuna Na kasancewarsa a PDP tsawon shekaru 20,
Ya k’ara da cewar al’ummar jihar Zamfara a yanzu suna cikin mummunan yanayi na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali na kashe – kashen rayuka, ya zama kana gidan za’a iya zuwa a kashe ka ko a sakawa garinku wuta, muna neman a taya mu da addu’a kuma ayi mana fatan Allah ya kawo mana shugabancin da zai zama mafita a gare mu a samu zaman lafiya mai dorewa amma wannan shugabancin na APC babu abinda zai iya yi mana
A nasa jawabin Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido yace na fara zuwa Zamfara a shekarar 1970 a matsayin d’an kasuwa, kuma Ina da abokai a wannan jihar sosai, maganar zuwa Zamfara a wajena baya matsayin siyasa sai dai matsayin zumunci domin ni naku ne ku nawa ne kuma mu daku amana ce, ba shakka an nuna mana karamci da mutuntawa da karb’a ta musamman kuma kun gode kwarai da gaske
Babu shakka rayuwar mutumin Zamfara tana cikin yanayin damuwa da rashin kwanciyar hankali da farko tukunna Ina addu’ar Allah ya kawo muku zaman lafiya da Nigeria gaba d’aya, a samu kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyar kowa, domin babu wani abu a rayuwar d’an Adam da zai yiwu dole sai da zaman lafiya.
A maganar siyasa a yanzu a matsayin shugabancin APC In akwai dad’i kun sani kuma kuna ji a jikinku in babu dadi ma kun sani, in akwai zaman lafiya kun sani, in akwai fatara, yunwa, talauci, garkuwa da mutane da kisan rayuka ko barazanar rikicin addini kun sani in babu kun sani.
Zab’en 2019 ba zab’e ne tsakanin kirista da musulmi ba, zabe ne tsakanin Musulmi da Musulmi, babu maganar kazo zabe ayi maka kabbara har ana cewa kayi ridda dan aka zab’i PDP, an kira ni kirista, an k’one ofishina, an kone Na Babayo a Azare, an zane Ku da bulala, an kira ni fasto, an kira mu a kowanne irin lafazi haka kawai saboda muna PDP, waliyyai sun hau yanzu ma’asumi yana mulki babu komai sai gilli da mugunta a matsayin hisabi, mutane sun shiga gonar ubangiji wai dole sai sun yi hisabi, a’a mulki a matsayin ramuwa
PDP zata dawo mulki a 2019 da karfin ikon Allah kuma za’a cigaba da inganta rayuwar yan Nigeria fiye da yadda aka yi a baya. Takara ta bata kwalliya bace ko ado ko Neman suna, ko ramuwar gayya, takara ce ta biyan bashin karramawa da adashen da Nigeria ta jefa min a ral
Categories
Labarai Siyasa

Ya zama dole ‘yan Najeriya su kawo karshen Gwamnatin Buhari a 2019 – Atiku

Hassan Y.A. Malik

Kungiyar yakin neman zabe na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta yi gargadi ga ‘yan Nijeriya da su tabbata ba su bari Buhari ya dawo mulkin Nijeriya a shekaarar 2019 ba.

Kungiyar ta Atiku Abubakar Campaign Organization ta bayyana alhininta bisa kisan gillar da ya afku a jihar Filato a baya-bayan nan, inda kungiyar ta bayyana lamarin da rashin kulawar gwamnati akan al’amuran da suka shafi al’ummar da ta ke mulki.

AACO ta ci gaba da cewa, gwamnati ta gaza wajen samar da canjin da ta yi ta wakar samarwa mutane a lokacin yakin neman zabe a sheakarar 2015.

Hasali ma dai sai talauci da ya karu, kashe-kashe ya yawaita, tattalin arzikinmu ya raunana da dai wasu abubuwa da dama da ke nuna gawawar gwamnatin nan, wadanda su ke nuna cewa Buhari bai dace da ci gaba mulkar Nijeriya ba a 2019.
Kodinatan kungiyar ta kasa, Dakta Fresh Onuoha ya shaidawa manaema labarai a jiya Litinin cewa, “Atiku Abubakar ne amsar matsalolin Nijeriya a shekarar 2019, domin gwamnatin Buhari ta gaza a kowane bangare na tafikar da harkar gwamnati.”

“Rayukan mutane a wannan gwamnati sam basu da wani muhimmanci sakamakon kisan mutane da ake yi babu dare babu rana da sunan wai fulani makiyaya, inda ita kuma gwamnati ta zauna turus, ta kasa tabuka komai.”

“Sam ba a sauraren jam’iyyun adawa da duk wani wanda zai fadi wata magana da ta saba da abinda gwamnatin ke ganin shi ne daidai duk kuwa da irin koke-koken da kungiyoyin jama’a ke yi babu dare babu rana. A yanzu ‘yan Nijeriya babu abinda suke yi sai kashe kawunansu saboda talauci.”

“Yunwa da talauci ya mamaye kasar baya ga cewa babu wani bangare na gwamnati da al’amura ke tafiya daidai. Lallai in har bamu tashi mun kai wannan gwamnati kasa ba, to kuwa za mu dawwama cikin yunwa da talauci.”

Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su yi Buhari da tawagarsa korar kare su zabi Atiku a shekarar 2019 don samun rayuwa mai inganci.” inji Dakta Onuoha.

Categories
Siyasa

Allah zai taimakemu mu kawar da Gwamnatin Buhari a 2019 – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo ya sha alwashin kai Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kasa, tare da binne ta a makabartar tarihi a zaben 2019 dake tafe.

Obasanjo ya bayyana cewar yana da yakinin cewar Allah zai taimake shi wajen ganin anyi duk yadda za ai domin ganin Buhari bai koma mulki karo na biyu ba.

Cif Obasanjon ya bayyana hakan ne a wajen wani taron tattaunawa da jama’a a birnin Badun na jihar Oyo tare da kungiyarsa ta CNM, a yayin da mambobin kungiyar suka shirya wani gangami a jihar ta Oyo.

Ya ce, kamar yadda Allah ya taimaka aka tumbuke rikakken dan kamakaryar nan Janar Sani Abacha, muna da tabbacin cewar, wannan Allah din yana nan kuma shi ne zai taimake mu mu kawar da wannan muguwar Gwamnatin ta Buhari.

Yayi kira ga matasa da dukkan ‘yan Najeriya da cewar kada su yi kasa a guiwa, domin akwai aiki ja a gabansu na ganin cewar sun taimaka a canja wannan Gwamnati.

 

Categories
Labarai Siyasa

Jigon APC a Kaduna Isa Ashiru Kudan ya fice daga jam’iyyar

Wani jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya ajiye takardun zamansa dan jam’iyyar APC a jihar,inda ya sa kafa ya tsallake.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar, Isa Ashiru wanda tohon dan jam’iyyar PDP ne, wanda kuma ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Kaduna au biyu, kuma dan majalisar wakilai ta kasa sau biyu.

Alhaji Isa Ashiru ya aike da wasikar ficewarsa daga jam’iyyar ne zuwa ga shugaban mazabarsa ta Kudan a yankin karamar hukumar Kudan, inda ya bayar da dalilin rashin demokaradiyya a cikin gida jam’iyyar.

Ya kara da cewar shi da magoya bayansa an ware u daga cikin jam’iyyar ba’a yin komai da su, bayan kuwa da goyon bayansu ne jam’iyyar ta kai gaci a jihar ta Kaduna. Shi dai Isa Ashiru shi ne mutumin da Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya kayar a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a shekarar 2014.

 

Categories
Siyasa

Matasa zaku hau Marsandi maimakon Adaidaita Sahu idan kuka sake zabata – Gwamnan Taraba

Gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishaku yayi alkawarin mayarda ‘yan Taraba musamman matasa miloniyoyi idan har suka sake zabensa a matsayin Gwamnan jihar a zaben 2019 dake tafe a cewarsa.

“Zaku dinga tuka manyan marsandi a maimakon Babur din Adaidaita Sahu, domin zaku dinga fitar  da madara da nama kuna samun kudade masu yawa idan kuka sake zabe na a matsayin Gwamnan jihar Taraba” Inji Gwamna Darius.

ko meye ra’ayinku akan wannanalkawari da Gwamnan Taraba ya yiwa al’ummarsa?

Categories
Siyasa

2019: Gamayyar matasan PDP sun bukaci Bafarawa ya fito takarar Shugaban kasa

Gamayyar kungiyar matasan jam’iyyar PDP reshen yankin Arewa maso yamma, bayan wani zaman gaggawa da suka gudanar a ranar Alhamis, sun bukaci tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa da ya daure ya tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Jagoran matasan yankin, ya shaidawa majiyar THISDAY, inda yace wasu daga cikin jiga jigan mutane daga Arewacin Najeriya,karkashin wata kungiya mai suna ‘Northern Coalation Force’ sun hadu a Birnin-Kebbi a jihar Kebbi domin tattauna makomar kasarnan.

A cewarsa, matasan sun tattauna akan makomarNajeriya, da kuma samun wani ingantaccen dan takarar Shugaban kasa wanda zai iya kalubalantar Shugaba Buhari a zaben 2019 da za ayi nan gaba, inda aka gabatar da sunayen Ahmad Muhammad Makarfi da kuma Attahiru Bafarawa domin tantancewa.

Inda daga bisani gamayyar suka amince akan Attahiru Bafarawa ya kasance wanda zai yiwa jam’iyyar PDP takarar Shugaban kasa, duba da irin ayyukan da yayi a baya da kuma yadda ya nuna gaskiya da rikon amana da tsoron Allah a yayin da ya rike Gwamnan jihar Sakkwato.

“Babu ko tantama, ana gudanar da wannan zama tsakanin kungiyar matasan Arewa da kuma wasu dattawa daga Arewacin Najeriya a Birnin-Kebbi, inda aka tattauna yadda jam’iyyar PDP zata fitar da dan takarar Shugaban kasa mai karfin da zai iya karawa da Shugaba Buhari, inda daga bisani aka cimma yarjejeniyar amincewa da tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa saboda kwarewa da kuma gogewa da yake da ita a sha’anin Siyasa da kuma Mulki.”

“Bafarawa na daya daga cikin kalilan din ‘yan siyasa masu gaskiya a kasarnan, kuma kwararren dan siyasa, wanda ya faro siyasa tun kuruciyarsa, yasan dama da hauni a siyasa, ya kuma san abinda ya dace da wanda bai dace, shi ne dan siyasa daya tilo wanda ya fara tun daga matakin kansila”

“Bugu da kari Bafarawa shi ne dan siyasa daya tilo da ya damu da hadin kai da kuma zaman lafiyar kasarnan, domin a sau da dama akan ga yadda yake nuna halin tausayi da kuma jin kai a duk lokacin da bala’i ya aukawa wasu al’umma musamman kashe kashen da ake yi na kabilanci, Bafarawa ne mutum guda tilo da kan fara kai gudunmawarsa ga mutanan da suke neman agaji”

Bayan haka kuma, Attahiru Bafarawa na daya daga cikin mutanan da aka gina jam’iyyun UNCP da ANPP da ACN da kuma APC da su, bisa jagorancinsa aka samar da jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya.

A lokacin da jaridar THISDAY ta tuntubi mai taimakawa Tsohon Gwamnan kan kafafen yada labarai Alhaji Yusuf Dingyadi game da wannan batu na gamayyar matasan jam’iyyar PDP da suka amince da Attahiru Bafarawa a matsayin wanda suke son ya yiwa jam’iyyar ta PDP takarar SHugaban kasa a zaben 2019, Dingyadi ya bayyana wannan batu da cewar wani abin farin ciki ne kwarai da gaske, sai dai yaki bayyana cewar ko Bafarawan zai yi takarar SHugaban kasa ko a’a.

Attahiru Bafarawa zai baiwa matasan jam’iyyar PDP amsa a lokacin da ya dace game da batun tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a zaben 2019. Yace a yanzu haka Bafarawa ya dukufa wajen yin adduah akan Allah ya kawo mafita ga halin da kasarnan take ciki, domin samun hadin kai da kuma cigaban wannan kasar.

Categories
Siyasa

APC: Saraki da Dogara sun goyi bayan takarar Adams Oshiomhole

Tsohon Gwamnan jihar Edo, Kwamared Aliyu Adams Oshiomhole ya bayyana cewar zai kaddamar da takararsa ta neman kujerar Shugabancin jam’iyyar APC ta kasa a ranar Alhamis dinnan.

Oshiomhole ya shaidawa ‘yan jarida a birnin Benin na jihar Edo cewar, Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar dokoki ta kasa Yakubu Dogara suna mara baya ga takararsa ta zama Shugaban jam’iyyar APC na gaba.

Haka kuma, ya bayyana cewar, Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha shi ne zai jagoranci Gwamnonin jam’iyyar wajen bikin kaddamar da takarar Oshiomhole da za’a yi a otal din Hilton dake Abuja.

Daman dai, tuni Adams Oshiomhole ya samu sahalewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen neman Shugabanci jam’iyyar na kasa.

Oshiomhole ya bayyana cewar ya shiga neman kujerar Shugabancin jam’iyyar na kasa ne domin shima ya bada tasa gudunmawar wajen ganin an gina jam’iyyar tare da shi.

Categories
Siyasa

Ina so Kwankwaso ya dawo PDP – Shekarau

Tsohon Gwmanan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP Malam Ibrahim Shekarau ya ce zai yi farin ciki idan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma PDP daga jam’iyyar APC.

Ana rade-radin cewa jagoran na Kwankwasiyya zai iya barin jam’iyyar APC bayan da uwar jam’iyyar ta goyi bayan Gwamna Abdullahi Ganduje a rikicin shugabancin da suke yi.

Hakazalika kuma ana ganin yana sha’awar yin takarar shugabancin kasar a zaben 2019, sai dai bai fito ya bayyana hakan ba kawo yanzu.

Sai dai Malam Shekarau, wanda shi ma ke son yin takarar shugabancin kasar a PDP, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu babu wata magana tsakaninsa da Kwankwaso kan shirin komawarsa PDP.

An dade ana rashin jituwa a siyasance tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadanda duka manyan ‘yan siyasa ne a Najeriya.

Ya ce ko a baya ma, ba shi da wata matsala tsakaninsa da Kwankwaso, kuma ba shigar Kwankwaso APC ce ta sa ya fita ba.

Duka mutanen biyu sun mulki jihar Kano tsawon shekara takwas-takwas, kuma suna da dimbin magoya baya.

Kuma wasu na ganin hadewarsu wuri guda za ta bai wa jam’iyyar APC gagarumar matsala ba wai a Kano ba nhar ma da wasu sassan kasar.

BBCHAUSA.COM

Categories
Siyasa

‘Yan daba sun hargitsa taron goyon bayan tazarcen Buhari a Jigawa

Wasu ‘yan jagaliyar siyasa sun tarwatsa taron gangamin nuna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Badaru su ci gaba da mulki a 2019.

An dai shirya taron ne a shiyyar Sanatan Arewa-maso-yamma, wato, Gumel, a filin wasa na garin jiya Lahadi, sai dai ya kare da hargitsin da tilas shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ado Sani ya hakura bai yi jawabi a wurin ba.

’Yan dabar sun rika rera wakokin adawa dake da munanan kalamai, wadanda aka ce sun yi haka ne ga sanatan da ke wakiltar Gumel, Abdullahi Gumel, wanda dama sun hana shi hawan dakalin da masu jawabi ke hawa su na kamfe.

Tun da farko dama sai da aka yi wa sanatan shigar-burtu, sannan Sanata Danladi Sankara ya shiga da shi cikin filin taron, saboda gudun kada a ‘yan dabar su kai masa hari.

Sai dai kuma wasu na cewa wadanda suka hargitsa taron, magoya baya ne ga wanda ke son kwace kujerar daga hannun Abdillahi Gumel a zaben 2019.

An tsara cewa dukkan ‘yan majalisar tarayya da ke wakiltar jihar Jigawa da wakilan majalisar jiha, za su halarci taron, amma guda biyu kadai suka halarta.

Shi ma gabban bako Gwamna Badaru bai je ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa duk wani mai rigar mutunci, musamman manyan ‘yan siyasa, sun rika sulalewa su na guduwa don kada ‘yan daba su ‘kaddamar’ musu.

Hausa.premiumtimesng.com