Categories
Siyasa

Zaben 2019: Har yanzu APC bata ayyana dan takararta ba – Bisi Akande

Tsohon shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, kuma tsohon Gwamnan jihar Legas Cif Bisi Akande, ya bayyanawa manema labarai a ranar alhams cewar, har zuwa wannan lokacin babu wani mutum da APC ta ayyana a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa. Yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai bayyana musu aniyarsa ta yin takara ba.

A dan haka, Cif Akande, yace kowanne dan jam’iyya yana da iko da kuma ‘yancin tsayawa takara a zaben 2019 da yake tafe. Ya kara da cewar, ko da Buhari zai sake neman tsayawa zabe, to dole ne zai yi takara tare da wasu a cikin jam’iyyar, ma’ana ba shi kadai za’a sahalewa tsayawa takara ba.

Bisi Akande ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga yankin kudu maso yamma, ya kara da cewar, har wannan lokacin Shugaba Buhari bai bayyanawa shugabannin yankin kudu maso yamman ko zai tsaya zabe ko ba zai tsaya ba.

Da aka tambaye shi ko jam’iyyar zata iya sahalewa Shugaba Buhari kara tsayawa zabe ko a’a, ya bayar da amsa da cewar, wannan ba abu bane na gaggawa, yace jam’iyya zata bayyana hakan a lokacin da ya dace, amma dai har yanzu Buhari bai nuna sha’awarsa ta tsayawa takara ba, a cewar Cif Bisi Akande.

A dan haka, tun da Shugaba Buhari bai bayyana mana kko zai tsaya zabe ba, to kowanne dan jam’iyya na da ikon nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Categories
Siyasa

Makiya bazasu tunzurani nayi rigima da Tambuwal ba – Wamakko

Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko, ya gargadi masu yunkuri kawo baraka tsakaninsa da mutumin da ya gaje shi a matsayin gwamnan sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, da cewar su sani hakarsu ba zata cimma ruwa ba.

Sanata Aliyu Wamakko wanda ke wakilatar Arewacin jihar Sakkwato a majalisar dattawa ta kasa, ya kara da cewar, da shi da Gwamna Tambuwal abu guda ne, dan haka babu wani abu da zai gitta tsakaninsu da zai sanya zullumi.

“Muna da manufa iri guda ni da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, dukkanmu burinmu shi ne cigaban jihar Sakkwato, dan haka mu duka abu guda daya ne, babu wani wanda zai ji kanmu, a matsayin tsohon gwamna da kuma mai ci”

Sanata Wamakko ya bayar da wannan sanarwa ne ta hannun mai magana da yawunsa Bashir Rabe Mani, wadda ya rabawa manema labarai, a gidan sanatan dake yankin Gawon nama a jihar Sakkwato.

Ina girmama Gwamna Tambuwal a matsayinsa na kanina, kamar yadda yake girmamani a ko da yaushe, shi (Tambuwal) mutumin kirki ne, babu wani sabani tsakaninmu, kuma ba za’a samu ba.

Categories
Siyasa

’Yan majalisu biyu na PDP sun canja sheƙa zuwa APC

Yan Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar adawa ta PDP sun canja sheka zuwa jam’iyyar dake mulki ta APC.

Ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja da Buari, Mista Zaphaniah Gisalo da wani mamba daga Jihar Kogi mai suna Yusuf Tijani ne suka yi canjin jam’iyyar.

Duk da cewa sauran ‘yan majalisun PDP sun soki lamirin wannan canja sheka, amma Jisalo da Tijani sun yi kunnen uwar shegu.

Categories
Siyasa

Zan cigaba da kasancewa sanata har karshen rayuwa ta, inji Bukar Abba

Tsohon Gwamnan jihar Yobe karo uku, kuma sanata mai wakilatar gabashin jihar a majalisar dattawa ta kasa, ya bayyana cewar, zai cigaba da zama a majalisar kasa a matsayin sanata har karshen rayuwarsa.

Tsohon Gwamnan wanda aka zabe shi a matsin sanata tun 2007, inda aka kuma sake zabarsa a shekarun 2011 da kuma 2015.

Alhaji Bukar Abba Ibrahim shi ne shugaban kwamatin kula da zaizayar kasa da sauyin yanayi na majalisar dattawa ta kasa.

Bugu da kari matarsa, Khadija Bukar an zabeta a matsayim ‘yar majalisar wakilai ta kasa har karo uku kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe ta a matsayin karamar ministar harkokin kasashen waje a 2015.

Bai dai bayyana ko zuwa ga wa yayi wannan bayanin ba. Amma dai Gwamnan jihar Yobe me ci Ibrahim Geidam zai kammala wa’adinsa a shekarar 2019 yayin da ake ganin zai nemi kujerar dan majalisar dattawa, wadda suka fito mazaba daya da tsohon gwamna Bukar Abba Ibrahim.

Sanata Bukar Abba a bayyana hakan ne a yayim da yake zantawa da manema labarai a yayin da ake shirin bikin cikar Nigeria shekaru 57 d samun mulkin kai.

Me kuke ganin zai faru tsakanin tsohon gwamna Bukar Ibrahim da Gwamna Ibrahim Geidam a 2019?

Categories
Siyasa

Buba Galadima ya caccaki gwamnatin Buhari

A tattaunawar da yayi da sashen Hausa na BBC, Injiniya Buba Galadima yace gwamnatin tasu ta APC da suka yi uwa suka yi makarbiya domin ganin kafuwarta, bata tsinanawa al’ummar Nigeria komai ba ya zuwa yanzu.

Galidima yace, sam bai gamsu da salon yadda ake tafiyar da gwamnatin Muhammadu Buhari ba. Sannan ya soki batun tsaro da yaki da rashawa. Ya kalubalanci jami’an tsaro cewar “ba zasu iya tuka daga Damaturu zuwa Damasak su kadai ba” yace sam batun da ake na tsaro rufar kura ne da fatar akuya.

Sannan Galadima, yace an yi watsi da wanda duk suka yi tallar Buhari tun farkon fitowarsa takara. Ya kara da cewa, “babu ko mutum daya da aka baiwa mukami a cikin mutanen da suka tallata Buhari tun farkon shigarsa al’amuran siyasa.

Da aka tambaye shi dangane da zaben 2019, Buba Galadima yace, ba zai ayyana wani mutum a matsayin wanda zai marawa baya a yanzu ba, a cewarsa akwai lokaci nan gaba da zai yi hakan. Da aka tambaye shi ko zai marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, yace indai ba a neme shi ba ba zai kai kansa ba. Ya kara da cewar, yafi karfin yaje a samu wani dan siyasa yace zai taimaka masa ko waye.

Me zaku ce kan wadannan bayanai na Buba Galadima da yayi a BBC?

Categories
Siyasa

Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta tsige mataimakin kakakin majalisa da wasu mutum uku

Majalisar dokokin jihar Adamawa a ranar litinin ta tsige mataimakin kakakin majalisar dokokim jihar Mista Sunday Peter da shugaban masu rinjaye Musa Muhammad.

Sauran wadan da aka tsige din sun hada da mataimakin shugaban masu rinjaye Mutawali Mohammed da kuma shugaban marasa rinjaye, Justina Nkom ‘yar jam’iyyar SDP dake wakiltar mazabar Lamude.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewar, Kabiru Mijinyawa ya jagoranci zaman majalisar na farko bayan da suka dawo daga hutun makwanni shida.

An zabi sabon mataimakin kakakin majalisar Mista Emmanuel Tsamdu mai wakiltar Madagali daga jam’iyyar APC, sannan kuma an zabi Hassan Burguma dan majalisa mai wakiltar Hong daga jam’iyyar APC a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.

Dan majisa Abubakar Hayatu daga APC ne ya gabatar da kudurin wannan tsigewa yayin da dan majalisa mai wakiltar Mubi ta kudu ya goyi bayan kudurin.

Sannan majalisar kuma, ta zabi Abubakar Isa dan majalisa mai wakiltar Shelleng daga APC a matsayin sabon mataimakin masu rinjaye, yayin da Lamsumbani Dili daga PDP ya zama sabon shugaban marasa rinjaye.