Categories
Tarihi

Sarkin Kano Ado Bayero: Wani gari yafi gaban kunu

Daga Fatuhu Mustapha

Ance wata rana sarkin Kano Ado ya dawo daga tafiya, ya biyo ta Katsina Road, sai yake cewa Sarki Waziri (Danrimi), akwai wani gida na anan, da na mallaka tun kafin in zama sarki, amma ban kara waiwayarsa ba, ban sani ba ko zan gane shi?! Sarki Waziri yace ” Allah ya taimaki sarki, sai sai inzo in duba” sarki yace “gidan kane? Gida nane, zan zo in duba kayana da kai na.

Bayan yan kwanaki, rannan da dare sai sarki ya sa aka kira masa Danrimi, yace masa yazo ya raka shi unguwa. Suka tafi, Danrimi na jan mota, sai Katsina Rd, su shiga nan, su shiga nan, har suka zo daidai wani gida. Sarkin Kano ya umarci Danrimi ya tsaya, yace masa “ai kuwa wannan ne gidan, tabbas”

Suka fito, suka saka akayi musu sallama da maigidan cikin dare. Maigidan ya fito, suka gaisa. Sarkin Kano ya kalle shi yace ” wannan gidan ka ne?” Yace “eh” yace masa saya kayi ko kuma baka akayi? Yace gaskiya asali gidan mahaifinmu ne muka gada. Sarki yace masa ” kai dan wane ne( ya fadi sunan maigidan), yace eh. Kafin ya mutu bai bar muku wasiyya ba? Sarki ya tambayi maigidan. Yace “eh ya bar mana wasiyya, yace gidan nan na wani mutum ne Malam Ado”.

Sarki yace masa ” to nine malam Ado, kuma ba zuwa nayi don in tashe ku ba, na sayi wannan gida sama da shekara 40 da suka wuce, kuma ni na saka mahaifinku a ciki, Amma abinda nake so da kai, gobe kazo fada, muje gaban sarki da kai, saboda a tabbatar da wannan magana, komai ayi shi da hukuma yafi amfani. Amma kar ka ji komai, ba tashinku zanyi ba”. Maigidan ya amsa yace “to Allah ya kaimu”. Sarki yace masa, In kazo ka nemi Sarki Waziri, zai kaimu gaban sarki da kai, sai a tabbatar da maganar.

Da safe maigida ya tafi fada, yaje ya nemi Sarki Waziri, aka kai shi office din sarki waziri. Ya gabatar da kansa, sarki Waziri yace ” kaine?” Yace “eh nine” yace “to jira”

Da sarki ya zauna a fada aka kira bawan allahnan, shi dai yana ta zura ido baiga malam Ado ba. Har aka kai shi gaban sarki.

Sarki yace masa ” kaine muka je gidan ka jiya?” Mutum ya gyara zama, ya kasa magana, saboda bai taba zaton Malam Ado sarkin Kano bane. Sarki yace masa ” to nine malam Ado. Gida nane. Ni na saka mahaifinku a ciki. Kuma mun ji dadi da ka rike wasiyyar mahaifinka. (Shi dai mutum yayi kasake, ya kasa cewa komai). Sarki yace ” Allah ya shi ma albarka”. Nan da nan fada ta dauka ” Allah ya shima albarka inji sarki”!!!!

Sarki yace ku nawa ne mahaifinku ya bari, yace ” mu bakwai ne: uku maza hudu mata” sarki yace “to yanzu in aka bar maka wannan gida an hada ka rigima da yanuwanka, saboda haka; kaje ka nemo gida a saya maka, su kuma kannenka maza a bar musu wannan gidan su raba. Yanuwanka mata kuma , ku kula dasu, kar ku bar su; su shiga wani hali.

Ance mutumin nan, saboda murna a kasa ya koma gida.

Allah ya jikan sarkin Kano Ado, Allah ya karfafi bayansa. Shi ko na yanzu , Allah yayi mai rabo mai yawa.

Categories
Tarihi

Yadda aka gano gawar Tafawa Balewa bayan juyin mulkin 1966

Daga Yasir Ramadan Gwale

Wannan bayanin yadda aka kashe Firaminista Sa Abubakar Tafawa Balewa, yana cikin wata tattaunawa da aka yi da marigayi Ibrahim Babankowa da jaridar Vanguard.

Babankowa: Na kasance Sango-Ota har wajen 15 ga Janairun 1966. Lokacin da aka yi juyin mulkin farko a Najeriya. A daren ranar da akai wannan juyin mulki, ina wajen binciken ababen hawa a Sango Ota a jihar Ogun, muna bakin aiki sai muka ga Kwambar motocin soji sun zo sun wuce ta gabanmu, akwai mota kirar Landroba da Fijo guda biyu da kuma wata Kanta. Sun fito daga Legas suka nufi Abekuta. A lokacin bamu zargi wani mugun abu ka iya faruwa ba kasancewar munga sojoji ne a cikin kaki, sai muke zaton ko zasu je aiki da ya shafi tabbatar da doka ne.

Abin da ban sani ba shi ne, ashe wadannan motoci dauke suke da Firaministan Najeriya zasu halaka shi. Mune mutane na karshe da muka ga gilmawar wadannan sojoji da kuma Firaminista a tare da su bamu sani ba. Daga baya muka fahimci, wadannan motoci sun tsaya kamar kilomita uku daga inda suka barmu. Suka shiga wani daji dake kusa da hanya, anan ne wadannan sojoji suka kashe Firaminista Tafawa Balewa da Okotie Eboh da sauran mutanen da ke tare da su. Wannan ya faru ne a daren Juma’ar 15 ga Janairun 1966 ranar da akai wannan juyin mulkin.Kamar awa daya da ta shige sai muka ga wadannan sojoji sun sake dawo sun nufi Legas. Bayan da gari ya waye ne muka fahimci cewar anyi juyin mulki. Saidai rudani ya biyo bayan rahotannin da suke nuna cewar an dauke Firaminsta daga gidan sa zuwa wani waje da ba’a sani ba.

Vanguard: Ya akai ka gano inda aka yasar da gawar Firaminista?

Babankowa: eh, na gano ta ne bayan kwana hudu da wannan da yin wannan juyin mulki. Naje wajen wani Sha-Katafi dake Sango Ota, dan na karbi magani, a lokacin wannan sha-katafi shi ne kadai asibiti a wannan yanki. Anan ne na saurari wasu marasa lafiya, cikin harshen Yarabanci, suna cewar akwai wani mugun doyi da suke ji a inda ke makwabtaka da su, amma basu san meye ke wannan doyin ba. Daga baya sai na gane cewar wadannan marasa lafiya dake wannan magana sun fito ne daga wani kauye dake kan hanyar Abekuta kusa da inda muka duba ababen hawa kwana hudu da suka shude.

Vanguard: Ya kayi da ka ji wannan batu?

Babankowa: Ina jin haka sai na sauya yanayin aikin namu. Na kasa ma’aikatanmu gida biyu, na tura runduna daya ta shiga yankin da muke zargi dan mu bincika, ta haka ne muka kawo zuwa ga wannan daji da aka kashe aka kuma yasar da gwarwakin su Firaminista. Abinda babu kyan gani ainun.

Vanguard: Me kuma kuka gano bayan nan?

Babankowa: Naga gawar Firaminista yashe a kasa ta fara rubewa, sannan naga gawar Minista Okotie da Kur Muhammad da kanar Abogo Largema da wasu mutum biyu. Na kadu matuka da ganin wadannan gawarwaki yashe a karkashin bishiya! A sabida haka na yi gaggawa na sanarwa da Insfekta na ‘yan sanda ta hanyar wani caji ofis dake Ikeja, dan sanda dake gurin Alhaji Kafaru Tinubu shi ya sadani da IG mukai magana. Na shaida masa cewar nagani kuma na shaida gawar Firaminista da wasu mutane a cikin daji. Daga nan ne na jira naji umarnin da za’a bani. Muna cikin wannan yanayi, ashe Insfekta yana hutu, wanda yake madadinsa shi ne Alhaji Kam-Salem. Daga nan aka bani umarnin kai tsaye na wuce babbar shalkwatar tsaro ta kasa dake Legas. Sabida bukatar gaggawa da ake na zuwa na, aka ce nayi amfani da jiniya idan na shigo Legas dan nayi sauri.

A lokacin da na isa Legas, tuni an bada sanarwa cewar Janar Aguiyi Ironsi ya karbe ragar ikon Gwamnati a matsayin Shugaban kasar Soja na farko. Har Aguyi Ironsi ya kaddamar da kansa a Shalkwatar tsaro dake Moloney. Isata wajen ke da wuya, natarar da wasu sojoji da suke jiran isowata, suka karbe dukkan kayan da suke tare da ni da suka hada da karamar bindiga da babba, suka kwabe mun takalmi da bel din da ke daure a kwankwaso na da hulata. Aka sanya ni gaba babu takalmi babu hula ba bel. A haka na isa ofis din Insfekta, isata ke da wuya sai natarar da Aguyi Ironsi zaune kusa da Alhaji Kam-salem. Ba wanda yayi mun magana can sai Gen. Aguyi Ironsi ya tambayeni cikin harshen Hausa, “ka ce kaga gawar Firaminista Balewa da ta wasu mutane”? Na amsa masa da cewar, eh haka ne. Ya sake tambaya ta, ta yaya akai kasan Firaminista? Na ce masa, nayi aiki da Sardauna a matsayin dogarinsa, kuma Sardauna da Balewa abokaine na kud-da-kud, dan haka na san Firaminista sosai.

Vanguard: Me kuma ya faru daga nan?

Babankowa: Daga nan aka sake fita da ni, inda Aguyi Ironsi ya bayar da umarnin a tsare ni a Naval Base dake Apapa, amma sai Insfekta yace, idan ba zaka damu ba ranka ya dade zamu tsare shi anan shalkwata, zamu gabatar da shi a duk lokacin da ka bukaci hakan. Gen. Ironsi ya karbi shawarar Kam-Salem suka cigaba da tsare ni a wajen. Can da tsakar dare, sai ga dogarin Firaminista Mista Kaftan wanda surikin Tafawa Balewa ne yazo da motar daukar gawa, da kuma wata kanta dauke da akwatunan daukar gawarwaki. Suka nemi a sake ni domin na jagorance su zuwa inda aka kashe su Firaminista.

Vanguard: Me ya faru da kuka je dajin?

Babankowa: Muna zuwa muka ga kumburarriyar gawar Firaminusta yashe a karkashin bishiya da hularsa zanna tana gefensa na dama. Yana sanye da farar kufta me alkyabba wanda tuni ta canza kala zuwa launin jini. A lokacin nan gawar Firaminista tuni ta fara zagwanyewa har ta fara tsutsotsi! Daga nan ne muka nannadeta da farin kyalle, haka nan na tallefe shi akan cinya ta saboda mu nade gawar duka. Mune mutanan farko da muka fara zuwa kan gawar Firaminista. Da aka gama nadewa aka sanya gawarsa a akwatu, sai nayi mata alama da Larabci dan kar a kasa gane ta. Daga nan muka nufi sashin saukar manyan baki na filin jirgin saman Legas, inda muka taras da wasu kananan jirage guda biyu suna jiranmu. Daga nan muka saka gawar Furaminista a jirgi tare da wasu danginsa dan zuwa Bauchi ayi mata sutura.

Isarmu Bauchi ke da wuya muka gabatar da gawarsa ga iyalansa. Babu wanda zai iya yiwa wannan gawa wanka a lokacin, kamar yadda addini ya shar’anta, sabida duk ta rube gaba daya kuma ta fara zagwanyewa! Haka nan mukai masa Sallah, aka bunne gawarsa. Hasbunallahu Wani’imal Wakeel! Wannan bakin tarihi ne da ba zamu taba mancewa da shi ba, an cutar da mu a zaman tare a kasarnan, Allah ka biwa wadannan bayin naka hakkin jinin su.

Marigayi Ahmad Ibrahim Babankowa shi ya baiwa jaridar Vanguard wannan labari mai matukar tayar da hankali. Ba shakka Inyamurai sun cucemu, Allah ya isa bamu yafe ba. Allah ya jikan Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello. Allah ya kai haske kabarinsu. Shima marigayi Ibrahim Babankowa muna yi masa adduar fatan alheri, Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa aljannah ce makomarsa. Muna mika ta’aziyarmu ga iyalansa musamman Sani Babankowa Allah ya yafe masa.

Yasir Ramadan Gwale
08-09-2015

Categories
Tarihi

Tarihi: Labarin Malam Mudi Spikin da wani Ɓarawo

Daga Fatuhu Mustapha
Wata rana malam Mudi Spikin ya dawo gida kawai sai ya hangi kofar gidansa cike da mutane ana ta hayaniya.  Nan da nan ya karasa da sauri domin yaga me ke faruwa, isar sa ke da wuya , ya tambayi wani mutum dake wurin, “me ke faruwa ne!” Mutimin yace masa ai barawo aka  kama ya saci buhun hatsi a gidan nan. Malam Mudi yace “subhanalLahi!” A gidan nawa?! Jin cewa shine maigidan yasa aka bashi wuri. Mutane kowa rike da makami, wasu na a miko shi mu gama masa aiki, wasu na a bari a kirawo yandoka.
Malam Mudi na shiga soro, yace ina barawo, aka ce masa gashi. Sai ya kalli barawo, yace masa ( cikin fada), “kai yanzu haka mu kayi da kai? Na gaya maka nima buhu guda ne, ya rage min a gidan nan, kuma ina da iyali, kuma ma ai cewa nayi in kazo kayi sallama, kace a auna maka rabin buhu, sai kawai kazo ka sunkuci buhu guda!!” Nan kuwa malam Mudi bai taba ganin barawo ba.
Nan kuma jikin kowa yayi sanyi, wani makwabcinsa yace ma, malam Mudi, “dama kai ka aiko shi?” Wani kuma ya kalli barawo, yace masa “kai ai sai kayi bayani, amma da kayi shiru, ai da tuni min gama maka aiki”
Nan da nan malam Mudi ya saka aka kawo kwanon awo, ya farke buhun nan da ya rage masa, ya aunawa barawo kwana 2o. Ya kulle ya daurawa barawo aka, har zai wuce, sai ya sanya hannu a aljihu ya dauko anini biyu ya mika masa, yace masa ga wannan in kaje kayi cefane, kasan uwargida sai da dan abin masarufi.  (Sai kace ya taba saninsa).
Tun daga ranar barawon nan ya tuba da sata.
Kaico! Ko yau a Arewa zamu samu dattawa irinsu malam Mudi Spikin? Allah ya jikansa da gafara!!
Categories
Tarihi

Haduwar Maitama Sule da Janar Murtala Mohammed

Daga Fatuhu Mustapha
Bayan anyi juyin mulki na 1967, duk lokacin da Janar Murtala Mohammed ya hadu da Dan Masanin Kano Dr. Yusuf Maitama Sule sai ya ringa yi masa irin wasan nan na malami da dalibin sa.
Ya kan ce masa, “mun dai kori ‘yan siyasa sai aje kuma a nemi sana’a”. Shi kuwa Dan Masani sai ya maida masa da cewa, “ai ka san Akuya ko bata haihuwa tafi kare”. A haka suke raha duk lokacin da suka hadu.
Rannan sai Janar Murtala ya zama shugaban kasa, ya kuwa tashi haikan akan yaki da zalunci da rashawa da ya addabi Najeriya, kusan komai gaskiyar ka kana shakkar ace Janar Murtala na neman ka. Kwatsam rannan sai ya aiko a gayawa Dan Masani cewa yana neman sa a Dodan Barracks (fadar gwamnati da ke Lagos kafin a dawo Abuja).
Dan Masanin Kano ya kwana yana jan Lahaula, saboda bai san neman da Murtala yake yi masa ba. Da safe ya hau jirgi, ya nufi Lagos, ya sauka a Airport, sai ya nufi Dodan Barracks, yana zuwa aka sanar da shugaban kasa, sai shi kuma yace a shigo da shi ofishin sa.
Da aka kai shi gaban Janar Murtala, suka gaisa sai Janar yayi masa barkwancin da ya saba yi in sun hadu cewar:
“Mun dai kore ku ‘yan siyasa, sai a je a nemi sana’a”. Sai Dan Masani yayi shiru, Janar Murtala yace, “Allah Ya gafarta ya kayi shiru?”
Sai Dan Masani yace:
“Ai kai a Karnukan ma Karen As’habul Khafi ne, wanda aka ce za’a shiga Aljanna da shi”.
Nan fa take Janar Murtala ya fashe da dariya yace masa, “To dama ina son in baka shugaban Hukumar Koken Ma’aikata ne (Public Complaints Commission).
Allah Ya jikan Janar Murtala, Ya jikan Dan Masani, Ya sanya Aljanna ta zama makomarsu gaba daya. Amin
Categories
Tarihi

Tarihin Marigayi Khalifa Sheikh Isyaku Rabiu

Daga Abdullahi Musa Badayi

An haifi Sheik Isyaka Rabiu cikin shekarar 1928, a wani kauye mai suna Tinki, wanda yake cikin karamar hukumar Bichi – Duk da yake tarihin kakaninnsa sun yo gudun hijira ne daga Borno, cikin shekarar 1892, domin su guje wa kisan gillar da Rabeh yake wa mutane.

Mahaifinsa mai suna Malam Rabi’u Dan Tinki, kauyen Tinki aka haife shi. Kuma zuri’arsu sun yi fice ne wurin harkar ilimin addini.

Malam Rabi’u Dan Tinki, ya yi karatun addini ne a wurin mahaifinsa, Malam Yunusa. Amma daga baya ya tafi wani gari mai suna Inshanwa, wanda yake can Damagaram Jamhoriyar Nijar. Inda ya yi karatu a karkashin wani fataccen Malami mai suna Gwani Kalla, inda ya kwashe shekaru sha uku.

Bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyar yin aure. Bayan ya yi auren kuma ya dauki matar ya nufi wani gari mai suna Inkiluwa, wanda yake kusa da Gashua, daga baya ya nufi Katagum, sannan ya dawo Kano.

Daga Kano ya sake tattara komatsansa, ya nufi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na’iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.

Kafin Malam Rabi’u Dan Tinki ya rasu a shekarar 1959, ya rubuta littattafai kusan 50. Shi ma Malam Rabi’u Dan Tinki a lokacin rayuwarsa, ya tura Isyaku Rabi’u garin Nguru neman ilmin addinin Musulunci. Bayan kammala karatun sa ne ya dawo gida Kano, cikin shekarar 1947. Sannan shi ma yayi auren fari, sannan ya fada harkar kasuwanci da izinin mahaifinsa, kuma yana hadawa da karatu.

Abubuwa sun fara bunkasa a cikin shekarar 1958, domin ya gina gida nashi na kansa a unguwar Jakara. Abubuwa suka ci gaba da bunkasa inda ya fara zama hamshakin dan kasuwa ya rika harkar litttattafai na addini, kayan masaku, da kekunan dinki. Malam Isyaka Rabi’u Shahararren dan Tijjaniya ne, yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyas Kaulaha, yana da jerin masa’antu, cikinsu akwai masakar Bagauda. Yana da wasu jerin gidaje na kawa, masu daukar hankalin baki, ko matafiya a kan titin Malam Aminu Kano.

Marigayi Malam Isyaka Rabi’u kafin rasuwar sa a Yammacin wannan rana ta Talata 8/05/2018 a baya, Ya dan taba harkokin siyasa a Jamhuriya ta daya. Ya yi jam’iyar NEPU, amma daga baya ya koma NPC. A Jamhuriya ta biyu ya samu kansa a jam’iyar NPN.

Haka kuma marigayin ya samun shaidar karramawa daga wurare da fannoni daban daban duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban addinin Islama a ciki da wajen Nigeria.

Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya ‘ya 42.

Allah ya jikansa ya rahamshe shi.

*Littafin da ya taimaka mana wurin bincike, Kano 100 Political And Business, na Ransom Enmenari da Ibrahim Barde.

Categories
Tarihi

Yau shekaru 35 da rasuwar Malam Aminu Kano: Tarihinsa a takaice

Daga Hassan Y.A. Malik

An haifi Malam Aminu Kano a shekarar 1920 a cikin birnin Kano.

Marigayi malam Aminu kano ya yi karatun Al-Qur’ani mai tsarki a wajen shehun malami, Malam Halilu. Malam Halilu shi ne limamin sarkin Kano ABDULLAHI BAYERO a shekarar 1929 zuwa 1953.

An sa malam Aminu kano a makarantar primary ta SHAHUCI da ke Kano a shekarar 1930 lokacin yana dan shekara goma da haihuwa.

Ya zama dalibin kwalejin kaduna wadda aka samar da ita a 1922 da sunan kwalejin Katsina a Katsina daga 1937 zuwa 1942.

Bayan ya gama kwalejin Kaduna ne, Malam Aminu Kano ya samu aikin koyarwa a makarantar Middle School da ke Bauchi, inda a lokacin Sir Abubakar Tafawa Balewa ya ke a matsayin Headmaster.

Daga Bauchi Middle School sai aka canzawa Malam Aminu Kano wajen aiki zuwa kwalejin horar da malamai ta Maru da ke gundumar Sokoto a matsayin headmaster a shekarar 1949 inda ya yi shekara daya a nan kafin daga nan ya ajiye harkar aiki ya kama harkokin siyasa gadan-gadan.

Malam Aminu Kano ya fara sansanar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin da ya taimakawa malam Sa’adu Zungur suka kafa wata kungiyar siyasa mai suna kungiyar cigaban Bauchi a jihar Bauchi a shekarar 1946.

Malam Aminu Kano da Malam Sa’adu Zungur sune suka karfafa kafuwar jam’iyar NEPA wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE ASSOCIATION kafin daga baya takoma NEPU wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION, an kafa jam’iyar ne a shekarar 8 ga watan 8 a shekarar 1950 kuma da mutane 8 aka kafa jam’iyar.

A shekarar 1947 ne Malam Aminu Kano ya jagoranci bude wata kungiya ta malaman arewacin Nigeria, kuma da shi aka bude jam’iyar mutanen arewa wadda daga baya ta rikede ta koma LPC a shekarar 1949 a matsayin jam’iyar da ke taimakawa mutanen arewa.

Malam Aminu Kano ya rungumi harkokin siyasa sosai wanda har hakan tasa ya ajiye aikinsa a ranar 4 ga watan Nuwamba a shekara 1950.

Malam Aminu Kano ya zama shugaban jam’iyar NEPU ta kasa a shekarar 1953 har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki na farko a Nigeria.

Ya taba cin zabe inda ya zama dan majalisar tarayya a shekarar 1959 zuwa 1966 inda ya wakilci Kano ta gabas a karkashin jam’iyar NEPU, shine me tsawatarwa a majalisar hadin gwiwar, kuma ya rike kwamishan lafiya na tarayya kuma dan majalisar zartarwa na koli a gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Yakubu Gowon.

Malam Aminu Kano da shi aka yi ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula a zamanin Yakubu Gowon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda a dalilin hakan ya haddasa hanbarar da gwamnatin Gowon din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammed ya gajeshi.

Da shi aka yi gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979.

Malam Aminu Kano shine shugaban jam’iyar PRP kuma dan takararta na shugabancin kasa a shekarar 1979.

Allah ya dauki ran Malam Aminu Kano a ranar Asabar 17 ga watan Afrilu, a shekarar 1983, a tsawon shekarunsa na 63 ya shafe shekaru 40 yana gwagwarmayar siyasa dan talakan arewa.

Ya yi kaurin suna wajen kin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwadayi kuma baya siyasar kudi face akida zalla kawai.

Indai ka jiyo shi to akan arewane, duk kungiyoyin da ya yi ko ya jagoranta to gaba dayansu za kuji na AREWA ne.

Bayan mutuwar marigayi Malam Aminu Kano an sawa muhimman wurare sunansa kamar irinsu filin jirgin sama na Kano wato Malam Aminu Kano Airport da kuma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano wato Aminu kano Teaching Hospital.

Allah ya jikan Malam Aminu Kano! Ya Allah kasa matasan arewa su yi koyi da irin halayyar wadannan bayin Allah nagari, wanda komai nasu akan arewa ne, basu da wayo sai sunji za’a illata AREWA!

Categories
Tarihi

Tsakanin Malam Aminu Kano da Sarakuna da Turawan mulkin mallaka

Daga Mansur Ahmed
Al’ummar yankin Arewa a kasar mu Nijeriya lokacin mulkin mallaka da bayan bada mulkin kai sun kasance a wani yanayi da Sarakunan Gargajiya da masu fada aji suka danne talaka da azabtar dashi tamkar bawa a wasu lokutan ma gara bawa kan irin Kama karyar da ake yiwa talaka. Zamanin ya kasance cikin yanayi na danniya da Kama karya da handama da babakere da nauyuka iri-iri na zalunci da aka dankara wa talakawa. Talakawa a lokacin na biyan kudin haraji da jangali da nomau a gonakin masu mulki a kyauta. Wasu lokutan ma in masu mulkin lokacin suka kai rangadi a yankunan dake karkashin su akan tilasta wa magidanci ya bar gidansa da dukkan abunda ya mallaka harma da iyalansa domin saukar dasu da tawagar su!
Malam Aminu Kano ya bayyana ne a tsakiyar lokacin da ake irin wannan zalunci da danne hakkin talaka. Yayi kira ga al’umma dasu bijire tare da kin amincewa da zalunci da kama karyan da akeyi masu tare da mutumta su kamar yan adam masu yanci da martaba. Kafuwar NEPU ke da wuya talakawa suka shiga jam’iyyar babu kama hannun yaro wanda ya jawo tsoro da fargaba ga turawan mulkin mallaka da Sarakunan gargajiya domin akidun NEPU na kira ne ga kawo karshen yadda suke tafiyar da mulkin su na son rai .
Talakawa a lokacin sun amsa kiran NEPU na samun yanci wanda hukumomi su kuma a lokacin suka dauki tsauraran matakai a kansu inda yayi sanadiyar daure tare da azabtar da magoya bayan NEPU. Wasu yan NEPU suka tafi gudun hijira wasu kuma akama sheka dasu barzahu. NEPU karkashin jagorancin Mallam itace jam’iyyar farko a tarihin kafuwar Nijeriya a kasa daya na yunkurin yanto talaka daga mulkin zaluncin fir’aunanci. Mallam Aminu Kano shi ya jagoranci dubban yan gwagwarmayan kwato yanci da wadanda muka sami labarin su da wadanda ma ba’a taba jin su ba muka sami yancin da muke morewa a yanzu. Wasu yan NEPU ma tsire su akayi har suka mutu kamar sannanen labarin Malam Audu Angale. Shi dai an tsire shine a bainar jama’a bisa zargin da akeyi masa na batanci ga Iyayen masu mulki ba tare da gurfanar dashi a gaban Shara’a ba. Haka ma an daura daruruwan yan NEPU ba tare da yi musu Shari’a ba in ma an kaisu gaban Shari’a ba’a basu damar kare kansu kan tuhumar da akeyi masu. Irin wannan zalunci da fin karfi shi yasa wasu yan NEPU in aka kai su gaban alkali sai suce su yan mishan ne domin kotunan basu da hurumin yiwa wanda ba Musulmi ba Shari’a sai a Kai su kotun Nasara inda za’a sake su domin babu shaidun da zasu tabbatar da zargin da akeyi musu.
NASARORIN DA YA SAMU A RAYUWA
Wanne nasarori ya samu a gwagwarmayar sa? Allah ya kaddara masa haddar al-qur’ani Mai girma wadda duk inda zai gabatar da Jawabi da wahala bai kawo aya ya fassara da take da alaka da taron ba, haka Lallai Mallam ya sami gagarumar nasara a gwagwarmayar sa na kawo karshen zalunci. Gwagwarmayar Malam ta tilasta wa Sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen nomau kyauta a gonakin masu mulki a kyauta. Ya kuma kawo karshen haraji da jangali. Sannan tsayuwar dakan da Mallam yayi ya baiwa ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowanne mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki, Yau a Najeriya tun daga kan shugaban kasa har kan wadda yafi kowa kankantar mukami Yayan talakawa ne
A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Suna kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin fadin ra’ayi ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya suka hana al’ummar su a wancan zamanin .
WASU DAGA CIKIN MANYAN ABOKAN GWAGWARMAYAR SA.
1. Malam Sa’adu Zungur
2. Bello Ijumu
3. Musa Kaula
4. Baballiya Manaja
5. Alhaji Adamu Danjaji
6. Magaji Dambatta
7. Mudi Sipikin
8. Malam Abba Mai kwaru
9. Malam Illah Ringim
10. Muhammad Danjani Hadejia
11. Malam Audu Angale
12. Alhaji Dauda Dangalan
13. Hajiya Asabe Reza
14. Hajiya Gambo Sawaba
15. Malam Lawal Dambazau
16. Mrs. Bola Ogunbon
Da sauran su da dama
An saka sunan Malam Aminu Kano a, Filin jirgin saman ƙasa da ƙasa dake kano, Asibitin koyarwa na kano, Aminu Kano Legal, Filin taro na Aminu Kano Triangle A Jigawa, Titin Aminu Kano Way a Kano, Jigawa, Lagos, Bauchi, Kaduna Da Abuja
Ya rasu ya bar mata daya, Aishatu. Wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar /22/5/2017 da ’yar sa daya Maryam. Sannan ya bar gida daya da gona. Allah ya jikan Mallam
Categories
Tarihi

Wasikar Malam Aminu Kano zuwa ga Firimiyan Arewa, Ahamadu Bello a 1958

39 Sudawa,
Akwatin gidan waya 744,
Kano.
8 ga Afrilu 1958.
Zuwa ga Alhaji Ahmadu Sardaunan Sakkwato.
Ina mai farin ciki shaida maka cewa na sadu da wasik’ar ka a ranar 1 ga wannan wata. Hakika, shirye – shiryen ka da suke cikin wannan takardar, babu shakka za su taimaki musulman kasar nan. Allah ya saka maka da mafificin alheri.
Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana maka farin ciki na game da irin karbar da kake yi min, da kuma yadda ka nemi da in tuntube ka a kan duk wani batu da na ji zan iya yi a kan haka. Na tabbata wannan zai amfani abokanta kar mu, wadda muka kulla tun lokacin da ba daya daga cikin mu da ya san zai rike wani mukami a gwamnati. Na yi alkawarin ziyartar ka a duk lokacin da Na zo Kaduna komai kuwa irin yanayin aiyyukana.
A cikin wasikarka na ga ka kawo wani batu da ya dade a raina, Wadda shine ‘yancin kai ga arewacin Najeriya da ma kasa baki daya, ka tuna da abin da na fada maka a cikin jirgin ruwa kan hanyar mu ta zuwa Landan na ce koda yaushe zan goyi bayan ka a kan maganar yancin kai, ka kira ni a duk lokacin da ka bukace ni zan taimaka a duk wata hanya da zan iya. Amma Ina fatan za ka yi nazari a kan shawararin da zan bayar sannan ka kula da wa su tsiraru da za su yi kokarin biyan bukatun kansu da sunan yancin Kai.
Ina fatan zaka sanar da ni a cikin lokaci duk lokacin da bukatar hakan za ta taso saboda yanayin tafiye – tafiye na.
Ina yi maka fatan kammala azumin watan Ramadan lafiya musamman a cikin wannan yanayi Na zafi. Allah ya shirya mana wannan kasa kuma ya daukaka ta.
Naka.
AMINU KANO.
Categories
Tarihi

Tunawa da marigayi Abubakar Rimi

Daga Mansur Ahmed

A dare ranar Lahadi 4 April 2010 ne, Allah (S.W.A.) yayi wa Alhaji (Dr.) Muhammad Abubakar Rimi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano (Kano da Jigawa) rasuwa.

Akan hanyar sa daga jihar Bauchi zuwa Jihar Kano, bayan ya dawo daga bikin nadin sarautar Sarkin Dass ya hadu da yan fashi a tsakanin garin Garko da Wudil. Duk da yan fashin basu taba shi ba amma za’a iya cewa sune sanadiyar mutuwar sa.

Bayan yan fashin sun karbe musu kudin su da wayoyin su, sannan suka taho kafin suzo Wudil Muhammad Abubakar Rimi ya gamu da bugun zuciya, nan take aka kai shi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Wajen karfe 11:40 na dare Allah ya karbi rayuwarsa.

Washe garin ranar da ya rasu aka yi jana’izar sa, a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Jana’izar Muhammad Abubakar Rimi ta samu halartar mutane sama da mutum miliyan daya daga sassa daban-daban na kasar Nigeria baki daya.

 

TAKAITACCEN TARIHIN ALHAJI MUHAMMAD ABUBAKAR RIMI

An haifi Muhammad Abubakar Rimi a kauyen Rimi na karamar hukumar Sumaila, jihar Kano, Nigeria. A shekarar 1940.

Alhaji Abubakar Rimi na daya daga cikin manya-manyan fitattu kuma jiga-jigan yan siyasar nahiyar Afrika. Yayi karatun sa na Kos a Zaria, kuma ya samu takardar shedar zuwa jami’ar London, kasar England a 1972. Ya hada diflomar sa a kasar kuma ya samu shedar babban digri.

Rimi yana daga cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar PRP a shekarar 1978 kuma an zabe shi a matsayin mataimakin jam’iyyar na kasa a taron ta na farko a jihar Lagos.

Abubakar Rimi an zabe shi a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Kano a October 1979 har zuwa May 1983 kuma shine gwamnan farar hula na farko a jihar. A farko 1983 Rimi ya fita daga jam’iyyar PRP ya koma Nigerian People’s Party (NPP).

A lokacin mulki Rimi yayi wa jama’ar jihar Kano da Jigawa aikin da wani gwamna bai taba yi ba.

Muhammad Abubakar Rimi shi ya gina gidan jaridar jihar Kano Triumph, ya gina gidan television na CTV Kano, ya gina Kasco da kuma Knarda.

Rimi a lokacin mulkin sa ne ya kirkiro sabbin masarautu na sarakunan yanka. Kamarsu: Kano, Gaya, Rano, Karaye, Auyo da Ringim.

A 1993 Rimi ya zama ministan yada labarai sannan ya zama shugaban NACB da NSPMC. yana cikin mutanen da suka samar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Rimi ya fita daga Jam’iyyar PDP a 2006 ya koma jam’iyyar Action Congress (AC) amma a 2007 Rimi ya sake komawa PDP.

A janairun 2006 wasu yan ta’adda suka shiga gidansa suka kashe masa matar sa Sa’adatu Abubakar Rimi.

Ranar 4 April 2010 ya rasu a asibitin Mallam Aminu Kano. An bunne shi ranar 5 April 2010 kamar yadda Addinin Musulunci ya ta nada.

A karshe Allah ya jikansa, Allah ya kai rahama kabarin sa, ya masa sakayya da gidan Aljanna firdausi. Ya baiwa iyalansa hakurin jurewa.

 

Categories
Tarihi

Jakolo ya bayyana yadda Sambo Dasuki ya nada Buhari Shugaban kasa a 1984

Tsohon dogarin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Almustapha Haruna Jakolo, ya bayyana yadda tsohon mai baiwa tsohon  Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, a zamanin mulkin soja a shekarar 1983 bayan juyin mulkin da aka yi, Sambo ya nada Buhari a matsayin Shugaban kasar Soja a wancan lokacin.

Mista Jokolo wanda shi ne tsohon Sarkin Gwandu da aka sauke, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Sun, yana mai mayar da martani kan wani littafi da Janar Muhammadu Iliyasu Bashar Sarkin Gwandu wanda ya gaji Jakolo ya wallafa.

A cewar  tsohon Sarkin Gwandu, Kanar Sambo Dasuki ya taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da kudi a juyin mulkin da ya kawo Buhari kan karagar mulki a shekarar 1983, bayan da aka kifar da Gwamnati Shehu Shagari.

Jakolo yake cewa “Zance na gaskiya, zuciyata tana bugawa, hankali na yana tashi matuka idan na kalli yadda ake yiwa Sambo Dasuki, na kan yi mamaki ainun”

“Abin mamaki ne kwarai da gaske. Idan har ban bayyana irin rawarda Sambo Dasuki ya taka ba a juyin mulkin shekarar1983, idan ba dan Sambo Dasuki ba, Buhari ba zai taba zama Shugaban kasa ba a wancan lokacin”

“Sambo shi ne mutumin da ya gamsar da mutane kan nadin Buhari a matsayin Shugaban kasa a wancan lokacin. Na rantse da Allah, na kuma rantsewa cewa, shi ne (Sambo Dasuki) ya kwantar da hankalin mutane kan nadin Buhari a matsayin Shugaban kasa. Lokacin da muke shirya juyin mulkin da ta sanadinsa Buhari ya zama Shugaban kasa,Sambo Dasuki ne ya samar da dukkan kudaden da aka yi amfani da su wajen juyin mulkin”

“A wancan lokacin Sambo Dasuki ya samo kudaden da aka yi juyin mulkin daga wajen Janar Aliyu Gusau da kuma Shugaban hafsan soja na wancan lokacin domin shirya juyinmulkin, babu sisin kwabo da aka karba a wajen Buhari akan juyin mulkin da ya bashi damar zama Shugaban kasa”

“Bama wannan kadai ba, Sambo Dasuki yayi amfani da kudin mahaifinsa, ya dauki nauyin wasu Malamai domin su tafi kasar Saudiyya su yi adduah,akan Allah yasa a yi wannan juyin mulki cikin nasara” A cewar Mista Jakolo.

Da yake bayani a cikin littafin da ya wallafa, ya ce “haduwa ta da gogaggen dan leken asiri” Wanda Yusha’u Shuaib ya wallafa, yace Sambo Dasuki ya yi bayani dalla-dalla akan yadda shi (Sambo) tare da wasu sojoji guda biyu, suka samu Buhari kan batun juyin mulkin 1983.

Mista Dasuki, ya bayyana cewar “shi ne tare da gudunmawar wasu sojoji guda biyu (Manjo Mustapha Jakolo da manjo Lawal Gwadabe) muka tafi Jos domin mu shaidawa janar Buhari a lokacin yana rike da mukamin GOC mai lyra da bataliya ta uku, muka shaida masa kudurin yin juyin mulkin 1983, wanda sanadinsa ne ya zama Shugaban kasa, Buhari shi ne mutumin da yafi kowa cin moriyar juyin mulkin da aka yiwa Shagari”.

Haka kuma, Mista Dasuki, ya cigaba da cewar, Buhari ya nuna tirjewarsa da kuma nuna rashin jindadin kan abinda ake yunkurin yi, amma muka gamsarda shi cewar babu wani abun damuwa, “Karka ji komai tunda a hannun ‘yan Siyasa zamu karbi mulki babu wani abu da zai faru”

A lokacin da Shuaibu, mawallafin wancan littafi, ya tambayi Sambo Dasuki, me ya sanya shi sanya hannu a juyin mulkin da aka yiwa Mista Buhari, shekara biyu bayan sun jagorancin juyin mulkin da ya kawi Buhari a matsayin Shugaban kasa, Mista Dasuki ya bashi amsa da cewar, “Buhari shi yafi kowa sanin wanda zai zarga kan wannan batu.”

Sambo Dasuki ya cigaba da cewar “A koda yaushe ina girmama wadan da suke sama da ni a tsarin aikin soja, ko muna soja ko mun yi ritaya, ina girmama su. Duk da cewar ni karamin soja ne, amma ina daga cikin wadan da suka tsare Buhari, amma ba ni na kama shi ba.

“Na samu Buhari ne lokacin da ake tsare da shi a sansanin soja dake Bonny tare da Lawal Rafindadi. Babu ta yadda za’a yi ace na musguna masa a wancan lokacin,kamar yadda wasu ke fadi. Amma na godewa Allah, kusan duk wanda aka yi wannan al’amari da su suna nan a raye”

Dan haka ba gaskiya bane, zargin da ake yi cewar, Sambo Dasuki shi ne jagoran sojojin da suka kama tare da tsare Buhari a juyin mulkin da aka yi masa shekarar 1985, Kanar Abdulmumini Aminu, wani dan asalin jihar Katsina, ya bayyana sunayen mutane sukun da suka tsare Buhari a wancan lokacin, a wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Sunday Trust a watan Agustan 2015 zaku iya karanta tattaunawar ta wannan rariya likau da zaku iya samu a (Links: https://goo.gl/KEz5nkhttps://goo.gl/wirj2Thttps://goo.gl/9vZM5A).

Kanar Aminu yace,mutum uku ne suka jagoranci tsare Shugaban kasar wancan lokacin (Janar Buhari) wanda suka hada da Lawal gwadabe da John Madaki.

Ya karada cewar “Ba zan ji shakkar bayyanawa duniya cewar ni ne na jagoranci tsare Shugaban kasar wancan lokacin Janar Buhari. Na tafi Dodan Barak a wancan lokacin tare da rakiyar sojoji guda biyu Manjo John Madaki da Lawan Gwadabe, mu uku ne muka isa inda Shugaban kasa yake, nine wanda na hau kan bene na sauko da Buhari.

“Tareda dukkan girmamawa, Ina yawan karantawa a shafukan jaridu,mutane suna cewar wai mun cusguna masa, mun kuma ci zarafinsa. Wannan sam ba gaskiya bane. Ni da janar Buhari, mu biyu ne kadai muka san abinda yafaru da shi, dan haka babu wani abu mai kama da cin zarafi da na yi masa”

“Mun bashi dukkan girmamawa a matsayinsa na Shugaban kasa, tun kafin wannan lokacin ma, muna matukar girmamashi, saboda yanayinsa. Muna girmamashi har ya zuwa wannan lokaci, babu kuma wani sabani tsakaninmu da shi, shi kansa ya san cewar ba yadda muka iya a wancan lokacin aikin soja ne ya biyo ta kansa”

“Shi da kansa ya taba shaida min a wani lokaci cewar, batu ne kawai na waye zai zama Shugaban kasa lokacin da ake tsananin adawa da mulkin Shagari. Ina daya daga cikin wadan da suka taka muhimmiyar rawa wajen kawo shi kan mulki.”